• English
  • Business News
Monday, October 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Jinkirin Tabbatar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Ke Cutar Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi

by Sani Anwar
2 months ago
Jinkiri

Duk da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na tilasta bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, aiwatar da cikakken shirin a faɗin jihohin Nijeriya, ya sha banban a tsakanin jihohi kamar yadda binciken LEADERSHIP ya nuna.

Jihohi kamar Jigawa da Bayelsa, na iƙrarin cewa; sun cika wannan ƙa’ida, wasu kuma kamar Jihar Kogi, Nasarawa da Ogun, sun nuna shakku a kan haka. Galibi ana zargin ƙin yin hakan ne, sakamakon tasirin da gwamnoni suke da shi, wanda ke da alaƙa rashin jajircewa daga ɓangaren gwamnatin tarayya da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

  • Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata
  • Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Bauchi, Ahmad Makama, Ya Rasu

Sai dai, yayin da ake ci gaba da yunƙurin sauya kundin tsarin mulkin ƙasar, masu ruwa da tsaki sun amince da cewa; batun samun ‘yancin cin gashin kai, dole ne ya wuce batun shelar doka, wanda ya haɗa da samun ‘yancin cin gashin kai ta fuskar kuɗaɗe da aiwatar da gaskiya a ƙananan hukumomi.

Kamar yadda ake tsammani, Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda ake ci gaba da samun tsaikon aiwatar da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na bai wa ƙananan hukumomi cikakken ikon cin gashin kansu ta fuskar kuɗi, inda ta bayyana lamarin a matsayin wanda ke matuƙar cutar da ma’aikatan Nijeriya da kuma tattalin arziƙin ƙasar baki-ɗaya.

Sanarwar ta Ƙungiyar Ƙwadagon ta baya-bayan nan, ta ƙara matsin lamba ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su gaggauta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli tare da maido da martabar demokuraɗiyyar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

Ƙungiyar Ƙwadagon ta lura cewa, jinkirin aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, yana da matuƙar tasiri kai tsaye da kuma mummunan tasiri ga albashin ma’aikata, fansho da kuma yiwuwar ɗorewar ci gaba da aikin.

Da yake zantawa da LEADERSHIP, shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ƙungiyar Ƙwadago, Kwamared Benson Upah ya ce, jinkirin ba wai kawai yana kawo cikas ga jin daɗin ma’aikatan ƙananan hukumomin ba ne, har ma yana nuna rashin mutunta hukunce-hukuncen shari’a a faɗin wannan ƙasa.

“Tun daga rana ta farko, mun ɗauki dukkan matakan da suka dace, domin ganin an aiwatar da wannan hukunci; dalili kuwa shi ne, abu ne da muka sha fama da shi.

“Jinkirin aiwatarwar, yana matuƙar cutar da ma’aikata da kuma tattalin arziƙi. Haka nan kuma, zai shafi ci gaba tun daga tushe. Jinkirin ya kuma nuna rashin ƙima da mutuncin hukumar shari’a,” in ji shi.

LEADERSHIP ta rawaito cewa, shekara guda bayan hukuncin Kotun Ƙolin, aiwatarwa ta gagara, inda Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ke zargin gwamnonin jihohi da ɗana tarko a kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi tare da kawo cikas ga aiwatar da su.

Sai dai, Ƙungiyar Ƙwadagon ta ce; a shirye take wajen sake ƙara zage damtse wajen ganin an mutunta hukuncin da kuma aiwatar da shi.

Upah ya ƙara da cewa, “Ko kaɗan ba za mu huta a kan wannan gwagwarmayar da muke kan yi ba, wannan hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke, yana ci gaba da ba mu ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske”.

Martani daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan, na nuni da cewa; yayin da ake ganin ƙananan hukumomi da dama suna jin daɗin cin gashin kansu a ɓangaren harkokin kuɗi, amma sai ga shi har yanzu ana ci gaba da samun tsaiko wajen aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.

 

NASARAWA

A Jihar Nasarawa, har yanzu ƙananan hukumomi ba su buɗe asusun banki da babban bankin ƙasar ba, domin fara karɓar kason kuɗin tarayya kai tsaye.

Shugaban Ƙungiyar NULGE, Kwamared Adamu Sharhabilu ya ce; “Har yanzu ana amfani da asusun haɗin gwiwa, shi yasa ƙananan hukumomi ba za su iya biyan cikakken albashi ba, kazalika; ma’aikatan ba sa karɓar mafi ƙarancin albashi.”

Haka nan, ya soki zaɓukan da ake gudanarwa na ƙananan hukumomi, inda ya bayyana cewa; “Gwamnoni ne ke yanke shawarar waɗanda za su zama Shugabannin Ƙananan Hukumomi. Waɗanda ake zaɓar, galibi yaransu ne da ba za su iya ƙalubalantarsu ba. Ta yaya kuwa cin ‘yancin gashin kai zai yiwu a irin wannan yanayi?”

Ya kuma bayyana cewa, “Har yanzu, gwamnoni ke saya wa Sarakuna da sauran Hakimai motoci, maimakon ƙananan hukumomi, wanda haƙƙinsu ne da an bas u ‘yancin cin gashin kansu.”

Saboda kuɗaɗe daban-daban da ake kwashewa, waɗanda suka haɗa alawus-alawus na Sarakuna da sauran kuɗaɗen bayar da horo, ya sa ƙananan hukumomi ke ci gaba da tsitsi a ɓangaren kuɗi.

 

DELTA

Ƙananan hukumomi a Jihar Delta, sun jima suna cin gashin kansu, tsawon lokaci tun kafin yanke wannan hukunci na Ƙotun Ƙoli. Gwamnatin Gwamna Sheriff Oboreɓwori, tana bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu, tun kafin Kotun Ƙoli ta yanke wannan hukunci na ba su ‘yancin cin gashin kansu, kan harkokin kuɗi.

Bugu da ƙari, dukkanin ƙananan hukumomi 25 na Jihar Delta, suna miƙa rahotannin kuɗaɗensu ga ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF). Hakan kuma, ya fito ne a yayin taron kwamitin fasaha na kwamitin raba asusun kuɗaɗen tarayya, inda aka Majalisun Jihar Delta sun miƙa rahoton kuɗi ga Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF).

 

Kwara

Har Yanzu Muna Jiran Gwamnatin Tarayya– Ƙungiyar ALGON

A Jihar Kwara, shugabannin ƙananan hukumomin sun ce; suna sa ido ne ga gwamnatin tarayya, domin ganin an tabbatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomin.

Sakataren yaɗa labaran na Ƙungiyar ALGON a jihar, kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Ifelodun, Hon. Femi Yusuf ya bayyana cewa, shugabannin gudanarwa sun tanadi aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi da zarar gwamnatin tarayya ta ba su dama.

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, reshen Jihar Kwara, Kwamared Olayinka Murtala; ya zargi gwamnatin tarayya da na jihohi, kan tsaikon da aka samu wajen aiwatar da wannan ‘yanci na cin gashin kan ƙananan hukumomi.

 

ZAMFARA

A Jihar Zamfara, Shugabannin Ƙungiyoyin NLC da NULGE, sun bayyana cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya a matsayin wani babban shinge da ya tokare al’amuran jihar.

Shugaban Ƙungiyar NLC na jihar, Kwamared Sani Halliru ya bayyana cewa:

“Cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya, su ne ginshiƙin gazawar cin gashin kan, don haka; muna buƙatar gyara kafin abubuwan su daidaita.”

“Kowace jiha, dole ne ta samu Babban Akanta Janar na ƙananan hukumomi, wanda zai wakilce su a kwamitin rabon asusun tarayya (FAAC). Idan ba a samu wannan ba, cin gashi kai ba zai yi tasiri ba.”

 

NIGER

A Jihar Neja kuma, gwamnatin ta ce; ba ta yi watsi da duk wani shiri na tabbatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi ba, amma Ƙungiyar NULGE ta jihar ta ce; babu wani ƙoƙari da gwamnatin tarayya ke yi na tabbatar da ganin an fara amfani da dokar.

Shugaban Ƙungiyar NULGE a jihar, Idris Abdukarim Lafene ya ce; saboda tsananin rashin kishi da manufa, fadar shugaban ƙasa ta canza ranar da za a fara aiwatar da cikakken ‘yancin cin gashin kan.

 

JIGAWA

Ƙananan hukumomi a Jigawa, sun samu ‘yancin cin gashin kansu, tun bayan da Kotun Ƙoli ta zartar da wannan hukunci a faɗin wannan ƙasa.

Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi na Jihar Jigawa (NULGE), Kwamared Abubakar Garba Shitu ne ya tabbatar da cewa:

“Ba mu da matsala game da ‘yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi, duk da cewa; hukuncin kotu ya bai wa jihohi damar ci gaba da tsoma baki kan harkokin gudanarwar ƙananan hukumomi.”

Haka zalika, Farfesa Salim Abdulrahman Lawan, Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) a Jigawa, kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwaram, ya tabbatar da cewa:

“Ba su da wata matsala dangane da abin da ya shafi batun ‘yancin cin gashin kai a Jigawa; tuni an riga an aiwatar da shi.”

Ya kuma yaba wa Gwamna Malam Umar Namadi, bisa aƙidarsa ta ƙoƙarin bin doka da oda da kuma ƙoƙarinsa na samar da ci gaba a faɗin jihar.

 

KEBBI

A Jihar Kebbi, batun ‘yancin cin gashin kai ya zama sai dai a faɗa da baki. Koda-yake, ana fitar da kason duk wata ta hanyar amfani da asusun haɗin gwiwa da Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautu.

Shugaban Ƙungiyar ALGON na jihar, kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kebbi, Alhaji Dahiru Ambursa, ya tabbatar da ce:

“Muna karɓar kasonmu daga jihar ta hanyar asusun haɗin gwiwa.”

Shugaban Ƙungiyar NLC, Kwamared Murtala Usman; ya zargi gwamnoni da rashin bayar da haɗin kai:

“Bayan yanke hukuncin Kotun Ƙoli, mun yi ƙoƙarin sauya asusun haɗaka, sai kuma abin ya ta’azzara, inda aka samu rashin amincewa daga gwamnatin tarayya da kuma jihohi.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nijeriya
Labarai

Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista

October 13, 2025
nema
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

October 13, 2025
Sojojin somaliya
Manyan Labarai

Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako

October 13, 2025
Next Post
Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya

Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista

October 13, 2025
Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano

Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano

October 13, 2025
nema

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

October 13, 2025
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya

Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya

October 13, 2025
Sojojin somaliya

Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako

October 13, 2025
Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

October 12, 2025
Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

October 12, 2025
An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje

An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje

October 12, 2025
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

October 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.