Fannin sarrafa magunguna muhimmin bangare ne na bukatun al’ummar kowace kasa, duba da yadda fannin ke taka muhimmiyar rawa wajen biyan bukatun kiwon lafiyar al’umma.
A kasar Mali, wannan fanni ya jima yana fuskantar koma baya, amma a yanzu muna iya cewa hakan ya fara sauyawa, domin kuwa bayan shafe tsawon shekaru ’yan kasar ta Mali na sayen magunguna masu tsada da aka sarrafa a ketare. A yanzu haka ’yan kasar sun fara amfani da magungunan da ake sarrafa a cikin kasar.
A shekarar 2013 ne dai kamfanin sarrafa magunguna na Humanwell mai helkwata a kasar Sin, da hadin gwiwar asusun samar da ci gaba na Sin da Afirka, suka zuba kudi har yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50, don gina masana’antar sarrafa magunguna irinta ta farko a birnin Bamako, fadar mulkin kasar ta Mali, masana’antar da aka sanyawa suna “Humanwell Africa Pharmaceutical”.
Masana’antar da aka samar karkashin wannan shiri, ta fara aiki bayan shekaru 2, inda take samar da nau’o’in magunguna daban daban da ake amfani da su a cikin kasar, tare da sayar da wasu a kasashe renon Faransa dake yankin yammacin Afirka.
Wannan muhimmin aiki da ya tabbata, albarkacin shigar kasar Mali shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, ya haifarwa kasar tarin alherai, ciki har da samun kudaden shiga daga masana’antar, yayin da kamfanin na Humanwell Africa Pharmaceutical, ya samar da guraben ayyukan yi har kusan 200 ga alummun yankin da aka kafa shi, inda suke aiki, tare da samun horo a fannonin lura da masana’anta, da jagorancin ci gabanta.
Ko shakka babu wannan yunkuri na dada tabbatar da burin kasar Sin, na yin tafiya tare da kasashe masu tasowa, ciki har da na nahiyar Afirka, ta yadda za a kai ga gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama a fannin kiwon lafiya da wanzar da ci gaba. (Saminu Hassan)