A yayin da matsalar sauyin yanayin duniya ke kara kamari, ya zama dole kasa da kasa su sa kaimin amfani da makamashi masu tsabta da ake iya sabuntawa, a wani kokari na tinkarar matsalar sauyin yanayi, da ma tabbatar da dauwamammen ci gaba. Don haka, a kwanan baya, a gun taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28(COP28) da ke gudana a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, sama da kasashen duniya 100 ne suka amince da manufar ninka adadin wutar lantarki da ake samarwa, da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa nan zuwa shekarar 2030.
Wasu daga cikin kafofin watsa labarai da suka yi tsokaci kan hakan, sun ce kasar Sin ce daya tilo, cikin manyan kasashen duniya, da ke da ainihin ikon cimma wannan buri.
- COP28: Sin Da Afirka Za Su Bunkasa Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kananan Ayyukan Samar Da Makamashi Mai Tsafta
- Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni
Hasali ma dai, furucin ba wai an yi shi ne ba tare da tushe ba. Kasancewar kasar Sin ta dade tana dora matukar muhimmanci a kan bunkasa makamashi masu tsabta, wadda a shekaru bakwai a jere ta zo na farko a duniya wajen yawan zuba jari ta bangaren samar da makamashi masu tsabta, sa’an nan, ta kuma zo ta farko a duniya wajen samar da wutar lantarki da makamashi masu tsabta, adadin da ya zarce KW biliyan 1.4. Baya ga haka, sama da rabin motoci masu aiki da sabbin makamashi masu tsabta na duniya a kasar Sin suke. Lallai, ma iya cewa, batun rage fitar da iskar Carbon ya zame wa al’ummar Sinawa jini da tsoka.
A sa’i daya kuma, kasar Sin tana kokarin taimakawa kasa da kasa wajen bunkasa makamashi masu tsabta. A gun hadaddiyar daular Larabawa da ke karbar bakuncin taron COP28, akwai wata tashar samar da wuta da makamashin rana da ta kasance irinta mafi girma a duniya, wadda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin ginawa, tashar da ake kira Al Dhafra. An ce, tashar na iya biyan bukatun magidanta kimanin dubu 200, wadda kuma za ta rage iskar Carbon da ake fitarwa da kimanin ton miliyan 2.4, kwatankwacin yawan iskar Carbon da motoci dubu 500 ke fitarwa.
Sai kuma a Nijeriya, tashar samar da wuta da karfin ruwa ta Zungeru, wadda ba da jimawa ba kamfanin kasar Sin da ya gina ta ya mikawa kasar ta Nijeriya, wadda ta kasance daya daga cikin tashoshin irinta mafiya girma a kasar, wadda wutar lantarki da ta samar har ta ishi birane biyu masu girman Abuja, inda ta taka muhimmmiyar rawa wurin daidaita matsalar karancin wuta da ake fuskanta a kasar.
Da tashar Al Dhafra da ta Zungeru, da ma tashar Karot ta kasar Pakistan, kusan muna iya samun irin aikin samar da makamashin da ake iya sabuntawa da kamfanonin kasar Sin ke aiwatarwa ko ina a duniya. Kawo yanzu, rabin na’urorin samar da wutar lantarki da karfin iska, da ma kaso 80 na na’urorin samar da wuta da makamashin rana a kasar Sin ce ake samar da su.
Daidai kamar yadda Abdulaziz Alobaidli, babban jami’in kamfanin Masdar na samar da makamashi masu tsabta na hadaddiyar daular Larabawa ya fada, Sin babbar kasa ce da ke sauke nauyin da ke bisa wuyanta, wadda ta yi namijin kokarin bunkasa aikin samar da makamashi masu tsabta, wadda kuma ta ba da gudummawarta wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi a duniya.