Kasar Sin da gaske take yi game da kudurinta na fifita rayuwar jama’arta a gaba da komai, kamar yadda take ci gaba da auna ci gabanta ta fuskoki da dama a kan mizanin kare hakki da mutuncin kowane dan kasa.
Yanzu haka, kasar ta dauki wani kwakkwaran mataki na sake fasali tare da shigar da tsarin kare muradun jama’a a cikin dokokin shari’ar kasar a hukumance, da nufin karfafa kare muradun kasa da na zamantakewa. A karkashin haka, an gabatar da wani daftarin doka a ranar Jumma’ar da ta gabata ga babban kwamitin Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Sin (NPC) domin amincewa da shi.
- DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta
- Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II
Dokar da ake son kafawa ta kunshi karfafa sa ido kan shari’a da kuma zamanintar da yadda ake gudanar da shugabancin al’amuran jama’a. Shugaban kwamitin kula da harkokin shari’a na NPC Yang Xiaochao ya ce, dokar tana da muhimmanci wajen kare muradun jama’a da kuma karfafa ci gaban da aka samu tun bayan kaddamar da amfani da wani tsarin kare muradun jama’a a shekarar 2015.
Asalin tsarin shari’ar da ake amfani da shi game da kare muradun al’umma ya bai wa masu gabatar da kara damar yin aiki na neman hukunta masu laifi a madadin sauran al’umma a shari’o’in da suka shafi laifukan gurbata muhalli, da rashin kiyaye tsaftar abinci, da kuma rashin da’a ga gwamnati wadanda dukkansu idan aka bar su kara-zube, za su tauye hakkokin galibin jama’a. Amma a halin yanzu, sabon daftarin dokar da ake son kafawa ya fayyace nau’ikan dokoki 16, ciki har da karin wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka shafi al’adun gargajiya da kuma tsaron kasa, wanda ke nuna kara fadada tsarin dokar.
Domin ganin ba a tauye hakkin kowane bangare tsakanin mahukunta da mabiya ba, a karkashin daftarin dokar, dole ne masu gabatar da kara su fara gabatar da bukatar hukumomin gwamnati da su sauke nauyin da ke wuyansu kafin shigar da kara a kansu. A bangaren kare hakkin jama’a kuma, an haramta daukar matakan tilastawa kamar hana mutum amfani da asusunsa na banki da kadarori ko takaita ‘yancin walwala a yayin gudanar da bincike. Kazalika, an karfafa gwiwar ‘yan kasa da kungiyoyin kyautata zamantakewa su bayar da rahoton keta hakkokin jama’a da kuma sa ido kan shari’o’in da ake gudanarwa kan hakan.
Daga shekarar 2015 zuwa 2025, hukumomin da ke kula da share hawayen jama’a a bangaren shari’a sun yi aiki a kan korafe-korafe fiye da miliyan 1.22 wadanda galibi aka gabatar a kan ma’aikatun gwamnati.
Su dai tsare-tsaren da ake amfani da su na kare muradun jama’a a kasar Sin ba a tattare suke a wuri guda ba, suna warwartse ne a karkashin dokokin gudanarwa na fararen hula daban-daban, amma wannan daftari ya hade su wuri guda.
Kokarin tabbatar da wannan daftarin doka na kare muradun al’umma a kasar Sin, babu shakka ya kara fito da burin kasar na gyare-gyare a dukkan fannoni tare da cike gibin da ake ganowa, yayin da kasar ta hau turbar cimma burin zamanintarwa a karkashin tsarin gurguzu nan da shekarar 2035. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














