• English
  • Business News
Friday, August 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma

by Sulaiman
3 hours ago
in Ra'ayi Riga
0
Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta rataya ne kan ka’idojin kare hakkin dan Adam, mutuncinsa, sannan samar masa da ci gaba. Ba kamar tsarin da kasashen yammacin Turai ke yi ba, wanda ke ikirarin jaddada hakkin jama’a ta bangaren siyasa. Kasar Sin na amfani da wani sabon salon abin koyi da ke ba da fifiko ga samar da ci gaba a matsayin ginshikin ’yancin dan Adam. Wannan hangen nesa ya tsara manufofinta da hadin gwiwarta da kasashen Afirka, wanda hakan ya sa kasar Sin ta zama babban jigo a duniya wajen kare hakkin dan Adam ta hanyar samar masa da ci gaba.

 

Domin fahimtar yadda kasar Sin ke hadin gwiwa da kasashen Afirka wajen inganta hakkin dan Adam, bari mu yi la’akari da wasu muhimman abubuwa da suka shafi hakkin dan Adam, sai mu tambayi kanmu, mun taba ganin irin haka a lokacin babakeren kasashen yammacin Turai a Afirka?

 

Samar da Ci Gaba a Matsayin Jigon Hakkin Dan Adam

Labarai Masu Nasaba

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Kawo Wa Afirka Fatan Warware Matsalar Karancin Wutar Lantarki

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma. Ta hanyar inganta yanayin rayuwa da samar da damarmakin tattalin arziki, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tana kara karfafa martabar jama’ar Afirka ta hanyar samar musu da ci gaba.

 

’Yancin Cin Gashin kai da Kiyaye Mutuncin Kasa

Wani muhimmin jigo na diflomasiyyar kare hakkin dan Adam ta kasar Sin, ita ce samar da ka’idar ikon mallakar kasa da rashin tsoma baki kan harkokin gudanar da mulkin kasashen abokan huldarsu. Ba kamar yadda kasashen yammacin Turai ke yi ba, kasar Sin ba ta jingina sharuddan siyasa kan lamuni ko tallafin da take bayarwa, kamar sauye-sauyen shugabanci ko tsoma baki kan harkokin siyasar kasashen. Wannan tsari na Sin ya yi matukar janyo ra’ayoyin gwamnatocin kasashen Afirka, wadanda galibi ke kallon taimakon da sai an gindaya musu sharudda a matsayin tauye musu hakkin ‘yancin cin gashin kansu. Don haka kasar Sin ta gabatar da kanta a matsayin abokiyar huldar da ke daukar kasashen Afirka a matsayin kasashe masu ‘yanci ba Bayi ba.

 

Kare Rayuwa da Lafiya

Kasar Sin ta tallafawa kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya da taimakon jin kai. Tun daga shekarar 1963 kasar Sin ta fara turo tawagar likitocinta zuwa Afirka don aikin agaji. A lokacin da cutar annobar Ebola da annobar COVID-19 ta barke a kasashen Afirka, kasar Sin ta jaddada ‘yancin rayuwa da lafiya a matsayin babban hakkin dan Adam. Irin yadda ta samar da alluran rigakafi, asibitoci, da kayan aikin likitanci, hakan ya nuna yadda kasar ke kare mutuncin dan Adam ta hanyar kare bukatunsa na halittarsa na yau da kullum.

 

Musanyar Al’adu da Mutuncin Dan Adam

Baya ga samar da tattalin arziki da kiwon lafiya, kasar Sin na ingiza yin mu’amala tsakanin jama’arta da na Afrika don karfafa mutunci da daidaito. Ba da tallafin karatu ga daliban Afirka a jami’o’in kasar Sin, shirye-shiryen al’adu, da hadin gwiwar kafofin watsa labarai, duk hakan na nufin sauya tunanin yadda kasashen yamma suka dauki Afirka. Ta hanyar karfafa mutunta al’adu da hadin gwiwa, kasar Sin ta gabatar da kanta a matsayin mai daukaka darajar mutum da kasa baki daya.

 

Kalubale da Suka

Hausawa na cewa, “sara da sassaka, ba ya hana Gamji toho”, duk wanda ya kudiri aniyar tsamo wani daga cikin kangin talauci da koma baya da wani ya jefa shi, dole sai ya fuskanci “kalubale da suka” daga wannan mai zaluncin. An ce lamunin kasar Sin ga Afirka kuma babu “tsangwama”, na nufin mallake yankin ne. Wasu kuma sun ce, matsalolin muhallin Afirka na da nasaba da ayyukan da kamfanonin kasar Sin ke yi a yankin. Duk da wannan suka, shugabannin Afirka sun jaddada kuma kullum a shirye suke kan ci gaba da kare muradun Sin domin ta tsamo su daga babakeren kasashen yammacin Turai da suka mayar da su Bayi, suna masu jaddada cewa, ci gaban da kasar Sin ke samar wa yankin, shi ne asalin kare hakkin dan Adam.

 

Da wadannan muhimman abubuwan da kasar Sin ke yi a Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, za mu tabbatar da cewa, huldar Sin da Afirka wacce ta rataya a kan samar da ci gaba, kare ‘yancin cin gashin kai, kare mutunci, su ne hakikanin kare mutuncin dan Adam sabanin yadda kasashen yammacin Turai suka kakabawa Afirka, wai ‘yancin dan Adam, ‘yancin siyasa.

Ta hanyar ba da fifiko ga bunkasuwar tattalin arziki, da mutunta ‘yancin kai, kasar Sin ta sake fayyace ka’idojin hadin gwiwar ‘yancin dan Adam da kasashen Afirka. Ba tare da wani kalubale ba, wannan hangen nesa na kasar Sin ya yi tasiri ga yawancin ƙasashen Afirka da ke neman mutunci, daidaito, da cin gashin kai a dangantakarsu ta ƙasa da ƙasa.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Bayyana Dalilin Obasanjo Na Tsanar Buhari

Next Post

Hakurin ‘Yan Arewa Ya Fara Karewa Kan Matsalar Tsaro – ACF

Related

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Kawo Wa Afirka Fatan Warware Matsalar Karancin Wutar Lantarki
Ra'ayi Riga

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Kawo Wa Afirka Fatan Warware Matsalar Karancin Wutar Lantarki

1 day ago
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Ra'ayi Riga

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

3 days ago
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

5 days ago
Tunawa Da Tarihi Tana Da Ma’anar Musamman
Ra'ayi Riga

Tunawa Da Tarihi Tana Da Ma’anar Musamman

2 weeks ago
Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Ra'ayi Riga

Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

2 weeks ago
Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
Ra'ayi Riga

Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu

3 weeks ago
Next Post
Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

Hakurin 'Yan Arewa Ya Fara Karewa Kan Matsalar Tsaro – ACF

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar Masana’antu Ta Yi Fatali Da Sake Gabatar Da Haraji Na Kaso 4 Na Kwastom

Kungiyar Masana’antu Ta Yi Fatali Da Sake Gabatar Da Haraji Na Kaso 4 Na Kwastom

August 29, 2025
Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya

Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya

August 29, 2025
Nijeriya Da Brazil Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Bunkasa Tattalin Arziki

Nijeriya Da Brazil Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Bunkasa Tattalin Arziki

August 29, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas

Sojoji Sun Ceto Mutum 117, Sun Kama Masu Laifi 150 Cikin Mako Guda

August 29, 2025
Masanan Kimiyya Na Kasar Sin Sun Samu Nasara A Bangaren Fasahar Sadarwar 6G Mai Amfani Da Haske Da Lantarki

Masanan Kimiyya Na Kasar Sin Sun Samu Nasara A Bangaren Fasahar Sadarwar 6G Mai Amfani Da Haske Da Lantarki

August 29, 2025
Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

Hakurin ‘Yan Arewa Ya Fara Karewa Kan Matsalar Tsaro – ACF

August 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma

Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma

August 29, 2025
Obasanjo

An Bayyana Dalilin Obasanjo Na Tsanar Buhari

August 29, 2025
Tsaro

Mutane Da Dama Sun Tsere Sakamakon Harin ‘Yan Bindiga A Neja Da Kwara

August 29, 2025
Marafa Ya Fice Daga APC, Ya Zargi Tinubu Da Watsi Da Zamfara

Marafa Ya Fice Daga APC, Ya Zargi Tinubu Da Watsi Da Zamfara

August 29, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.