Sanin kowa ne cewa Sin kasa ce wacce ta dauki yaki da fatara da muhimmanci, musanmman ma a yankunan karkara inda masu fama da kangin talauci suka fi yawa. Sin dai kasa ce mai tasowa da ta fi kowace girma a duniya kuma tana gaba-gaba a kan yaki da fatara ko kuma talauci a yayin da ta dauki matakai wadanda suka sa ta kawar da kangin talauci daga dukkan fannoni zuwa shekarar 2020.
Wannan cimma nasara dai yana da inganci mai yawa a rayuwar jama’a, da tattalin arziki, da yanayin tsarin gudanar da mulki.
Matakan dai da aka fi ba da muhimmanci a yaki da fatara da raya karkara su ne kamar: fifita harkar noma a kasafin kudi na kasa, da tallafi ga manoma da masu fama da fatara, da bayar da bashi maras yawan riba, da cire haraji a kan manoma da kayan amfanin gona, da bada tallafi a kan kayan aikin gona da kuma saukaka biyan kudi daga ’yan makaranta na karkara. Ana kuma shawartar manoma da su rika shiga kungiyoyin hadin gwiwa domin samun ci gaba da kuma bunkasa jarinsu.
A cikin hanyoyin da tsarin ya kunsa dai sun hada da zuba jari da bunkasa ababen more rayuwa da bunkasa fannin noma da bada tallafi, da bada basusssuka marasa kudin ruwa, haka kuma gwamnati na fadakar da manyan kamfanoni da su zuba jari su hada kai da kananan ’yan kasuwa musamman wadanda ke karkara. Lallai abin jinjinawa ne yadda wannan shiri ya yi nasara a kan saukaka fatara da kuma raya karkara a cikin shekaru goman da suka wuce.
A shekarun baya dai lokacin da na samu damar kai ziyara kasar Sin a yayin da na je wasu larduna wadanda suka hada da Beijing, da Shanghai, da Anhui, da Jiangsu, da Fujian, da Shaanxi.
Abubuwan da suka fi burge ni a shirin yaki da fatara na kasar Sin a nan shi ne kokarin da samari da suka kammala karatun jami’o’i suke yi a kan wani shiri wanda aka dauka su domin aiki da taimakawa a kauyuka don ganin iyalai masu fatara su samu kudaden shiga ta hanyoyi da dama musamman noma, da kiwon dabbobi, da sana’o’i domin fitar da su daga kuncin fatara.
Wani abun burgewar kuma da na lura da shi a cikin ziyarce-ziyarce na a cikin kasar shi ne wato, manoma ba su biyan kudi a manyan hanyoyi wato “toll gate” in dai har sun dauko kayan amfanin gona. Suna wucwe ne kyauta, kuma wannan duk yana cikin tsarin tallafi da rage fatara ne.
Bugu da kari, a sakamakon wannan nauyi da jam’iyyar Kwaminis ta kasar ta dauka, an samu cimma nasarar saukaka fatara da kuma bunkasa yankunan karkara a gomman shekarun da suka gabata a karkashin shirin, wanda aka ayyana a taro na kasa na 18 na jam’iyyar Kwaminis ta kasar a shekarar 2012.
A wannan lokaci ne aka kaddamar da shirin kuma aka tashi gaba daya domin cimma nasarar kakkabe fatara wanda a karshe aka yi nasarar fitar da mutanen da talaucin ya yi ma katutu fiye da miliyan 100. A nan dai ina iya cewa samar da abinci ta fannin fadada harkar noma da raya karkara ne babbar nasara domin a yau, kasar Sin tana ci da kanta duk da tana da yawan mutanen da ya kai biliyan 1.4, dan haka kuma ana samun karin ci gaba a kauyuka.
A sakamakon nasarar da kasar Sin ta samu na cimma burinta na kawar da talauci da raya karkara, kasashen Afirka ma za su iya koyi da matakan da kasar Sin ta dauka domin saukaka fatara a kasashensu.
A Najeriya, a misali, gwamnati ta dauki irin wannan darasi a yayin da ta bullo da shirin bunkasa noman shinkafa ta hanyar bayar da basussuka masu karamar riba da tallafi ga manoma ta hanyar samar da kayan aikin gona da takin zamani. Ta wannan darasi, manoma da dama sun samu ci gaba kuma kasar Najeriya ta samu bunkasar tattalin arziki da kuma rage kudin fita da ake amfani da su wajen shigowa da shinkafar a shekarun baya. (Mai sharhi: Lawal Sale)