• English
  • Business News
Saturday, May 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kauyen Xiaoheifa Ke Kokarin Rungumar Kyakkyawar Makomarsa A Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Yadda Kauyen Xiaoheifa Ke Kokarin Rungumar Kyakkyawar Makomarsa A Kasar Sin

Yadda ake kiwon kaza a karkashin bishiyoyi a kauyen Xiaoheifa

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Noma tushen arziki, kuma kullum kasar Sin na dora muhimmanci a kan raya aikin gona da kauyuka da kuma rayuwar manoma, kasancewarta babbar kasa wajen ayyukan noma.

Tun bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar a shekerar 2012, jam’iyyar ta dora matukar muhimmanci a kan ayyukan da suka shafi noma da raya kauyuka da kuma manoma, matakin da ya taimaka wajen fitar da manoma kusan miliyan 100 daga kangin talauci, daga bisani kuma ta fara aiki da shirin farfado da kauyuka, kuma sakamakon haka, rayuwar manoma ta ingantu sosai, baya ga yadda aka yiwa kauyuka gyaran fuska sosai. Kauyen Xiaoheifa dake yankin Daxing na birnin Beijing ya zama misali a wannan fanni.

  • Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan-Adam Da Ake Iya Sarrafa Shi Daga Nesa

Malam Xu Shuzhi, mazauni kauyen Xiaoheifa ne,wanda ya bayyana cewa, “Sauye-sauyen da suka faru a kauyenmu, na gan su duka da idona, daga yadda yake fama da koma baya zuwa irin ci gaba da ya samu yanzu. Duk da cewa, har yanzu ba mu kai kauyuka da suka ci gaba ba, amma dai mun samu manyan sauye-sauye.”

Xu Shuzhi yana da gonakin da fadinsu ya kai kimanin eka 0.67, a baya, shi da iyalansu duka na dogara ne a kan noman masara da alkama. Uwargidansa tana da nakasa a kafa, ga kuma ciwon sankara, kuma yaransu biyu a wancan lokaci na karatu a makaranta, amma kimanin kudin Sin Yuan 6,000 (kwatankwacin Naira 600,000) ne kawai yake samu a duk shekara a aikin noma, abin da ya sa su cikin kuncin rayuwa.

Xiaoheifa
Yadda manoman kauyen Xiaoheifa ke shuke-shuke a karkashin bishiyoyi

Ganin cewa kauyen Xiaoheifa na yankin karkara ne, kana ga tsofaffi da masu fama da nakasar sassan jiki, shi ya sa a baya, kauyen Xiaoheifa ya yi matukar fama da koma baya, inda matsakaicin kudin shigar da kowane mazauni kauyen ya samu a duk shekara bai kai kudin Sin Yuan 6,000 ba. Sakamakon haka, Xiaoheifa ya zama daya daga cikin kauyuka mafi fama da talauci a yankin birnin Beijing.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Irin wannan yanayi ya fara sauyawa a shekarar 2012, bayan da hukumar birnin Beijing ta fara aiki da shirin dasa bishiyoyi masu fadi a sassan birnin a kokarin kyautata muhallin zama, kuma a kauyen Xiaoheifa, gwamnati ta yi hayar gonakin da fadinsu ya kai kimanin eka 160 a kan kudin Sin Yuan miliyan 3.6 (kwatankwacin Naira miliyan 360) a kowace shekara don dasa bishiyoyi, baya ga biyan kudin kula da bishiyoyi na kudin Sin Yuan 4 a kan kowane muraba’in mita daya, tare da samar da guraben aikin kula da bishiyoyin ga mazauna kauyen.

Xiaoheifa
Malam Xu Shuzhi ke nan da ke tattaunawa da wakiliyarmu

Malam Xu Shuzhi ya ce, “Mun amfana, mun samu aikin yi, kuma da farko an biya mu Yuan 80, sai kuma ya zuwa bara waccan, an kara kudin zuwa yuan 100, a lokacin Yuan 30 ne kawai muke iya samu a kowace rana in mun fita cin rani, ga shi kuma wannan aiki ba shi da wahala, gyara bishiyoyi da yi musu ban ruwa ne kawai, duka na iya.”
Ana biyan Yuan 100 ne a aikin kulawa da bishiyoyi a kowace rana, adadin da ya kai kimanin Yuan 2000 zuwa 3000 ke nan a wata, don haka, rayuwar mazauna kauyen ta fara ingantuwa sannu a hankali.

Xiaoheifa
Yadda ake kiwon kaza a karkashin bishiyoyi a kauyen Xiaoheifa

Sai dai a yayin da bishiyoyi ke girma, kulawar da suke bukata na raguwa, don haka ma, kudin da gwamnati ke biya ta fannin kulawa da bishiyoyin ma na raguwa shekara da shekaru, lamarin da ya damu jagororin Xiaoheifa. Malam Liu Jiwei, jami’in kwamitin kula da kauyen ya ce, “Ya zama dole mu yi amfani da albarkatun da muke da su, a maimakon mu dogara ga kasafin kudin da gwamnati ta samar kawai. Sabo da in dai bishiyoyi sun girma, ba zai yiwu ba a ci gaba da samar mana kudin kulawa da su, to, me za mu yi? Don haka, dole ne mu yi amfani da dukkan albarkatun da muke da su, don al’umma su samu moriya, a yayin da kuma gwamnati ma ta amfana, wato mu ci moriyar juna, mafitarmu ke nan.”

A shekarar 2014, a yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron majalisar wakilan jama’ar kasar, ya bayyana cewa, ya kamata a yi kokarin bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma, a yayin da kuma ake inganta muhallin zama.

Lallai furucin ya wayar da kan jagororin kauyen, wadanda suka zura idonsu ga sararin kasa dake karkashin bishiyoyin.

Da bishiyoyin suke kanana, daidai lokaci ne da ya dace a yi shuke-shuke a karkashinsu. Liu Jiwei ya ce,

“Na farko, hakan ya taimaka wajen yin tsimin albarkatun gonaki, na biyu kuma ya yi tsimin kwadago, sabo da a yayin da muke kulawa da bishiyoyi, ba wani abu mai wahala in mu shuka wani abu a kasa, hakan kuma ya zama jifan tsuntsu biyu da dutse daya.

Xiaoheifa
Malam-Liu-Jiwei-ke-nan-da-ke-nuna-mana-manhajar-da-aka-kirkiro-na-gudanar-da-harkokin-kauyen-a-zamanance.jpg

Amma ta hakan, manoma sun ci riba, sakamakon yadda mu kan raba musu amfanin gona da muka shuka in an girbe su don su ci, sa’an amfanin da suka rage mu kan sayar kuma mu tara mu raba su ga manoman a karshen shekara.”
Sai dai babu wanda a kauyen ya taba yin shuke-shuke a karkashin bishiyoyin, manoman kauyen ma sun nuna shakku da yin hakan. Bisa binciken da suka yi, daga karshe a shekarar 2015, kwamitin kula da kauyen ya yanke shawarar hadin gwiwa da wani kamfani wajen noman nau’in furen da ake kira Marigold a Turance, wanda ake amfani da shi wurin harhada magunguna, kuma kamfanin ya samar da tsiron furen da ma fasahohin noma, a yayin da mazauna kauyen suka samar da kwadagon aikin da kamfanin ke biya.

Sama da mazauna kauyen 50 ne suke aikin, wadanda daga karshe suka samu matsakaicin kudin shigar da ya kai kudin Sin Yuan kimanin 6000, hakan ya faranta musu rai, tare da karfafa niyyar jagororin kauyen wajen bunkasa tattalin arziki na karkashin bishiyoyin.

A shekarar 2016, gwamnatin birnin Beijing ta fara aiki da shirin tallafawa kauyuka masu fama da talauci, matakin da ya taimaka ga kulla hulda a tsakanin cibiyoyin nazarin kimiyyar noma na birnin da ma kauyen Xiaoheifa, kuma masanan aikin gona da yawa sun je kauyen. Bayan dogon nazari, sun bayar da shawarwari game da shuke-shuke da ya dace a yi a karkashin bishiyoyin dake kauyen, shawarwarin dake zama manuniya a bangaren kimiyya wajen aiwatar da aikin. Daga baya, daga laimar kwado zuwa albasa da karas da tattasai, shuke-shuke da aka yi sun yi ta karuwa.

Xiaoheifa
Yadda manoman kauyen Xiaoheifa ke girbin karas da suka shuka a karkashin bishiyoyi

Daga bisani, mazauna kauyen sun kuma fara kiwon kaji a karkashin bishiyoyin, hanyoyin tattalin arzikinsu sai kara fadada yake yi, wanda hakan ba kawai ya kara samar da abinci ga mazauna kauyen ba, hatta ma ya taimaka ga kara kudin shigarsu. Malam Xu Shuzhi ya ce, “Daga noman furen Marigold a farkon fari har zuwa noman tattasai, babu wanda ban yi ba. Daga lokacin da na kama aikin a shekarar 2013 zuwa yanzu, kudin da na samu daga aikin ya kai Yuan kimanin dubu 170.”

Xiaoheifa
Wurin shan iska mai dausayi da aka kafa a kauyen Xiaoheifa

Kawo yanzu, an kafa cikakken tsarin noma da kiwon kaji a karkashin bishiyoyi a kauyen Xiaoheifa, kuma matsakaicin kudin shigar mazauna kauyen ma ya karu daga kasa da yuan 6,000 zuwa kimanin dubu 30 a duk shekara. Duk da haka kauyen bai tsaya ba, a maimakon haka, sai ya fara nazarin tsarin gudanar da harkokin kauyen a zamanance, inda ya hada gwiwa da jami’ar koyon harkokin noma ta kasar Sin wajen fito da wani tsari na zamani da ya kunshi manhajar gudanar da harkokin kauyen ta wayar salula da mazauna kauyen ke iya amfani da ita, matakin da ya kara inganta aikin gudanar da harkokin kauyen.

Baya ga haka, domin mazauna kauyen su kara jin dadin rayuwarsu, an kuma gyara wani bangaren kauyen da a baya ake zubar da gurbataccen ruwa da shara a ciki, inda aka dasa nau’o’in furanni da tsirrai, aka kafa wurin shan iska mai dausayi mai fadi eka 22, don mazauna kauye su rika shakatawa, wanda ya samu karbuwa sosai.

Xiaoheifa
Tattasan da aka shuka a karkashin bishiyoyi a kauyen Xiaoheifa

Yanzu haka, kauyen Xiaoheifa na kokarin gano wata mafita a nan gaba. Malam Liu Jiwei ya ce, kauyen na shirin gudanar da aikin yawon shakatawa, don mazauna kauyen su ci karin moriya.

“Inda muka dosa ke nan, wato muna shirin hada wannan wurin shan iska da kuma bishiyoyin da muke da su da kuma al’adun kauyenmu, don mu gudanar da harkokin yawon shakatawa, ta yadda idan baki sun zo, mai yiyuwa ne za su kwana daya ko biyu a wajenmu, su dandana abincinmu, su girbi amfanin gona da muka shuka a karkashin bishiyoyi, don su ji dadi su shakata, a sa’i daya kuma mazauna kauyenmu su samu riba. Abin da muke so mu yi ke nan a nan gaba.” (Lubabatu Lei)

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ko Kun San Yawan Makamai Masu Linzamin Da Koriya Ta Arewa Ta Mallaka?

Next Post

“Mun Kammala Ayyuka Sama Da 2000” – Fantami

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

11 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

12 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
“Mun Kammala Ayyuka Sama Da 2000” – Fantami

"Mun Kammala Ayyuka Sama Da 2000" - Fantami

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bukaci Kada Amurka Ta Siyasantar Da Hadin Gwiwar Bangaren Ilimi

Sin Ta Bukaci Kada Amurka Ta Siyasantar Da Hadin Gwiwar Bangaren Ilimi

May 23, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi

Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi

May 23, 2025
Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata

Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata

May 23, 2025
Sin Da ASEAN Sun Kammala Tattaunawa Game Da Kafa Yankin Ciniki Cikin ‘Yanci

Sin Da ASEAN Sun Kammala Tattaunawa Game Da Kafa Yankin Ciniki Cikin ‘Yanci

May 23, 2025
An Gudanar Da Taron Kolin Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Na Duniya Na Shekara Ta 2025 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kolin Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Na Duniya Na Shekara Ta 2025 A Beijing

May 23, 2025
Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3

May 23, 2025
Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

May 23, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz

May 23, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu

May 23, 2025
Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai

Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai

May 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.