Yayin da kasashen duniya da dama ke kara bayyana bukatar fadada cudanya, da hada-hadar kasuwanci ta amfani da kudaden cikin gida, maimakon nacewa amfani da dalar Amurka, yanzu haka a kasar Kenya dake gabashin Afirka wannan buri ya fara ciki, inda kudin kasar Sin RMB ke kara samun karbuwa tsakanin al’ummun kasar musamman ’yan kasuwa dake gudanar da cinikayya da takwarorinsu na kasar Sin.
Ko shakka babu, hakan wata manuniya ce dake tabbatar da cewa, sannu a hankali, kudin Sin RMB na maye gurbin dalar Amurka, a hada hadar kasuwanci dake kara bunkasa tsakanin kasashen biyu.
Wasu alkaluman hukumar kididdiga ta kasar sun nuna cewa, kasar Sin ce babbar abokiyar huldar cinikayyar kasar Kenya, kasancewarta mafi zuba jarin waje, da gudanar da ayyukan raya kasa a Kenya, idan an kwatanta da sauran kasashe dake gudanar da irin wadannan huldodi tare da kasar.
A shekarar 2022 da ta gabata kadai, alkaluman hukuma sun nuna cewa, adadin hajojin da Kenya ta fitar zuwa Sin sun kai darajar kudin kasar Shillings biliyan 27.5, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 193, yayin da adadin hajojin Sin da kasar ta shigar gida suka kai darajar dalar Amurka biliyan 3.17.
Sakamakon irin wannan cudanyar kasuwanci mai armashi dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu, a halin da ake ciki, bankunan kasuwanci da dama a Kenya, suna samar da damar hada-hada da kudin Sin RMB, wanda a baya babu irin wannan dama. Hakan ya nuna irin ci gaban da aka samu, karkashin manufar amfani da kudaden gida mafiya sauki domin habaka cinikayya.
Masharhanta na cewa, amfani da kudade daban daban na kasashen dake cudanyar kasuwanci da juna, muhimmin mataki ne na bunkasa alakar cinikayya, saboda hakan yana iya rage tsadar hada-hada, ta hanyar kawar da bukatar canjin kudi zuwa dalar Amurka, ko sauran kudaden manyan kasashen yammacin duniya.
Idan har wannan manufa ta dore, ko shakka babu karin kasashe masu tasowa, musamman na nahiyar Afirka, za su ci babbar gajiya daga hada-hada da kudin kasar Sin RMB, yayin da Sin da kasashen na Afirka ke kara fadada hada-hadar kasuwanci da cinikayya a dukkanin fannoni. (Saminu Hassan)