Tabarbarewar tattalin arziki a Nijeriya ya haifar da karin karancin biyan kudin haya yayin da masu hayar ke ci gaba da biyan kudin haya a duk shekara.
Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 34.6 cikin 100 da kuma yawan rashin aikin yi, da yawa daga cikin masu haya suna kokawa don biyan bukatunsu, lamarin da ya tilasta wa masu gidaje fuskantar karuwar basussuka.
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
Masu haya a Nijeriya na kara kokawa kan yadda farashin hayan ya tashi a yayin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa.
Yayin da hauhawar farashin kaya ya kai kashi 34.6 cikin 100 a watan Nuwambar 2024, masu gidaje sun kara kudin hayar gida da kashi 100 bisa 100 a manyan garuruwa kamar Legas, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar kudi ga masu haya da da kuma raguwar kudaden shiga.
Rahotanni sun nuna cewa kusan kashi 80 cikin 100 na kadarorin da wasu masu gidajen ke kula da su ne ke da karancin masu haya, wanda hakan ya haifar da takaici da kuma tunani sayar da su.
Duk da kokarin da gwamnati ke yi na habaka biyan kudi na wata-wata, kudaden na haya na shekara-shekara karuwar kudaden haya na kara dagula lamarin.
Masu gidajen na kara bayyana takaicin rashin biyan kudin haya, wanda hakan ya sa wasu ke tunanin sayar da kadarorinsu. Mutane da yawa suna ba da rahoton matsaloli wajen karbar kudin hayar, musamman daga masu biyan kudin haya na dogon lokaci wadanda suka ambata a baya kan biyan kudi.
An dai bayyana dokar ba da hayar gidaje a Jihar Legas a matsayin wani shamaki wanda ke zama kalubale ga masu gidaje na su kwato kadarorinsu daga hannun wadanda suka gaza biyan kudin haya.
Sakamakon haka, masu zuba jari suna barin kasuwar saye-sayarwa, domin fargabar dawowar dogon lokaci a kan zuba jari saboda tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa. Wasu masu gidaje suna tunanin kara kudin hayar don rage asara.
Masana dai na nuni da cewa lamarin zai kara tabarbare ne in ba tare da sa hannun gwamnati ba, kamar yadda ake sarrafa haya, da barin masu gidajen haya a cikin wani yanayi na tsadar kayayyaki da kuma rage karfin saye da sayarwa.
Duk da wadannan kalubale, masu haya a jihar Legas sun nuna sha’awar biyan hayar shekara-shekara fiye da biyan hayar wata-wata kamar yadda binciken kasuwar gidaje na BuyLetLibe 2024 ya yi kiyasi.
Hakan dai na faruwa ne duk da hayar da ake yi ba bisa ka’ida ba da ke kawo cikas ga zuba hannun jari na cikin gida da na waje a fannin kadarori na kasar.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, tabarbarewar tattalin arziki a kasar, kamar hauhawar farashin kayayyaki, na kawo cikas ga harkokin zuba jari na cikin gida da na waje a fannin.
Wannan ma kamar yadda rahoton ya yi hasashen cewa irin wannan dabarar za ta haifar da gasa ga rukunin gidaje da ake da su a wuraren da ake bukata. Rahoton na BuyLetLibe mai taken ‘Rahoton Mazauna Gidaje’ ya bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na masu karba sun fi son biyan haya na shekara-shekara akan kudin wata.
Bayanan binciken ya ci karo da ra’ayoyin jama’a da kuma shirye-shiryen gwamnatin Jihar Legas na bullo da biyan kudin haya ta intanet a duk wata a bangaren gidaje na jihar.
A cewar rahoton, kusan kashi 62.6 cikin 100 na masu amsa tambayoyinmu na Legas har yanzu sun fi son biyan hayar shekara fiye da sauran hanyoyin biyan kudi.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda mai suna “EKO Rebenue Plus Summit,” mai taken “Bude Sabbin hanyoyin Haraji Ga Jihar Legas.” Shirin ya zayyana samar da Naira biliyan 2.5 a duk shekara daga masu biyan kusan 100,000 duk shekara.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Jihar Legas za ta mallaki wannan tsarin na zamani, tare da hukumomi kamar ma’aikatar gidaje ta Jihar Legas da sauran MDAs a matsayin abokan aikin fasaha.
Wani kashi 36.4 kuma ya nuna sha’awar motsawa cikin watanni shida zuwa 12 masu zuwa. Rahoton ya yi nuni da cewa, fifikon hayar ‘yan Legas na nuna tsananin bukatar gidaje masu araha a jihar.
Bugu da kari, binciken ya nuna cewa mafi yawan ‘yan Legas sun gwammace su biya tsakanin Naira miliyan 1 da miliyan 3 a matsayin biyan kudin hayar shekara-shekara, kamar yadda kashi 34.5 na wadanda suka amsa suka bayyana.
Haka kuma, kashi 11.8 bisa 100 na masu karba sun fi son farashin haya tsakanin Naira 100,000 zuwa Naira 500,000, yayin da kashi 26.4 bisa 100 sun fi son biyan kudin haya a duk shekara tsakanin Naira 500,000 zuwa Naira miliyan daya.
A daya bangaren kuma, kashi 7.3 cikin 100 na wadanda aka bayyana za su iya biyan kudin hayar Naira miliyan 5 zuwa miliyan 10 domin kashi 20 cikin 100 za su zabi biyan kudin hayar tsakanin Naira miliyan uku zuwa miliyan biyar.
Dangane da girman gidaje, yawancin ’yan Legas da aka ruwaito a cikin binciken sun nuna fifikon daki mai gadaje 2 ad daki mai gadaje 3 da kashi 38.2 cikin dari da kashi 35.5 bisa dari bi da bi.
Hakanan, kashi 16.4 cikin dari da kashi 9.2 cikin dari na masu amsawa sun zabi dakuna 4 da dakuna 1 bi da bi a matsayin nau’in gidan da suka fi so. Dangane da yanayin da ake ciki a fannin kadarori na Legas, rahoton ya yi hasashen cewa kasuwar gidaje a Legas za ta ci gaba da baje kolin gidajen zama duk da matsalar tabarbarewar tattalin arziki da aka samu a shekarar da ta gabata.
An yi nuni da cewa, saurin karuwar farashin zai ragu a rabin na biyu na shekara idan aka kwatanta da yadda aka samu karuwa a cikin shekara daya da ta gabata.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, tabarbarewar tattalin arziki a kasar nan (habakar hauhawar farashin kayayyaki) na kawo cikas ga zuba jari na cikin gida da na waje a fannin, inda masu zuba jari ke daukar hanyar “jira ku gani”.
Irin wannan dabarun ana hasashen za su haifar da gasa ga rukunin gidaje da ake da su a wuraren da ake bukata.
Ta kuma jaddada cewa, duk da matsalolin tattalin arziki, harkar gidaje za ta bunkasa nan da shekaru masu zuwa saboda karuwar yawan jama’a da kuma saurin karuwar birane.