Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara a ranar Juma’a ta bayyana yadda aka kama, Dr Ayodele Joseph, wanda ake zargi da yi wa mara lafiya da ta zo neman magani a asibitinsa fyade.
Tun da farko dai ‘Yansanda sun yi nasarar kama Ayodele kuma an gurfanar da shi a gaban kotu ranar Laraba kan zargin laifin rashin da’a da fyade.
- Kotu Ta Tura Shugaban Asibiti Kurkuku Kan Zargin Yi Wa Majinyaciya Fyade
- Alkalin Babbar Kotun Kwara, Oyinloye Ya Rasu Yana Da Shekara 58
Da yake gabatar da shi yayin holin bayyana masu aikata muggan laifi a cikin Jama’a, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Paul Odama, ya ce da farko sun gurfanar da shi ne saboda saba dokar tsare mutane da ya yi.
Odama, ya ci gaba da bayyana cewa a baya an gurfanar da wanda ake zargin (Dr. Ayodele Joseph) a gaban kuliya bisa zargin rashin da’a da ya yi sanadiyar mutuwar wani Nneka Akanike a asibitinsa.
A cewarsa, “tunda farko dai majinyaciyar ta kunna wayarta ta danna wuri yin rikodin don nadar bayanan aikin tiyatar da likitan zai yi mata amma shi bai sani ba.
“Daga baya ta farka daga barci bayan an yi mata tiyatar, inda ta tsinci kanta tsirara, kuma a lokacin da ta kalli faifan bidiyon, ta gano cewa Dokta Ayodele Joseph ya yi lalata da ita ba bisa ka’ida ba a lokacin da ake jinya.
“Bincike ya haifar da dawo da faifan bidiyon da aka yi na jima’i a don tabbatar da binciken lafiyar matar,” in ji shi.