Mai shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye na babbar kotun jihar Kwara ya rasu.
Mai shari’ar ya rasu ne a daren ranar Lahadi bayan ya sha fama da rashin lafiya.
- Kamar Buhari Da Ganduje: Darius Ishaku Ya Nemi Gafarar ‘Yan Taraba
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 63, Sun Ceto Mutum 150 Da Aka Sace
An taba kai shi kasar Indiya neman magani amma ya rasu yana da shekara 58, kamar yadda majiya ta shaida wa manema labarai.
Ya yi aiki da Babalakin & Co. kafin a nada shi alkalin babbar kotun Jihar Kwara.
Har ya zuwa rasuwarsa, Marigayi Oyinloye ya kasance alkali na babbar kotu.
Ya gurfanar da wasu ‘yan damfarar yanar gizo da EFCC ta gurfanar da su a gaban kuliya tare da bayar da umarnin a kwace kudaden da suka samu na laifukan da suka hada da wasu manyan motoci da kuma dubban daloli tare da mayar da su ga gwamnatin tarayya.
A watan Yuni, 2017, Marigayi Oyinloye ya yi fatali da hukuncin biliyan hudu da aka yanke wa Sahara Reporters da mawallafinta, Mista Omoyele Sowore, kan wasu labaran da aka buga a shekarar 2015 kan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki. Daga baya aka daukaka kara a kan hukuncin.
Ya kuma yankewa wani malami dan shekara 38 da haihuwa a Kwalejin Fasahar Lafiya ta Jihar Kwara, a Offa, Adebisi Ademola, daurin watanni shida a gidan yari.
Gawarsa ta taso da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Alkalai da ke Ilorin zuwa Ijara-Isin domin yin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A jawabin ta’aziyyar gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana lamarin a matsayin mar dadi, inda ya kara da cewa shi masanin shari’a ne mai gaskiya.