Kungiyar Liverpool ta barar da damarta na darewa akan teburin gasar Firimiya bayan da ta buga canjaras da abokiyar karawarta Manchester United a wasan mako na 32 a filin wasa na Old Trafford da ke birnin Manchester.
Liverpool ce ta fara jefa kwallo a minti na 24 da fara wasan ta hannun Luis Diaz bayan da alkalin wasa Anthony Taylor ya soke kwallon da Garnacho ya jefawa Manchester United minti biyu kacal da farawa.
- Bayar Da Tallafin Wutar Lantarki Kaso 85 na Kara Nuna Tinubu Mai Kishin Jama’a Ne – Minista
- Man City Da Arsenal: Yadda Aka Yi Faɗuwar Guzuma A Wasan Da Aka Kece Raini A Etihad Etihad
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Bruno Fernandez ya farkewa Manchester kwallo daga tsakiyar fili yayin da mai tsaron ragar Liverpool Conor Kelleher ya baro da’irarsa.
A minti na 64 kuma matashin dan wasan Manchester Kobie Mainoo ya jefa kwallo a ragar Liverpool wanda yasa wasan ya kara zafi dab da karewar lokaci, Mohammad Salah ya farkewa Liverpool a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan Wan Bissaka yayi keta a daira ta 18.
Da wannan sakamakon 2:2 ne Liverpool ta ci gaba da zama a matsayi na biyu, inda take da maki iri daya da Arsenal wadda ke matsayi na daya akan teburin gasar Firimiya.