ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Malamai Suka Dirar Wa Batun Yaki Da Nijar

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Malamai

Manyan malaman musulunci a Nijeriya sun yi kashedin afka wa Nijar da yaki sakamakon kin mayar da Shugaba Bazoum a bisa karagar mulki da sojojin juyin mulki suka yi. 

Idan dai za a iya tunawa dai, kungiyar ECOWAS ta yi ganawar gaggawa a cikin watan Agusta, inda ta bai wa sojojin juyin mulki da ke kasar Nijar kwanaki bakwai na su mika mulki ko su fuskanci takunkumai ciki har da barazanar daukar matakin karfin soja.

  • NSCDC Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 10, Ta Kafa ‘Yan Sintiri
  • Fasahar Aikin Gona Da Ire-Iren Hatsi Masu Inganci Na Sin A Bikin Baje Kolin Uganda

Da yake nashi gargadin, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ka da ya shiga yaki da kasar da ke makwabtaka da Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Shahararren malamin, ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar nan da ka da ta amince da bukatar da shugaban kasar ya gabatar mata kan yakar Nijar.

A cewar dattijon malamin, maimakon su shiga yaki da kasar, kamata ya yi Shugaba Tinubu da sauran shugabannin ECOWAS su tattauna da gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta hambarar da shugaba Bazoum.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

“’Yan Nijeriya da Nijar sun dade a tare. Don haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bi hanyoyin diflomasiyya da nufin karfafa kyakkyawar alaka da bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasashen yammacin Afirka,” in ji shi.

A nasa bargaren, Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya gargadin cewa, mutane a hankali da lallashi ake bin su wajen cimma wani lamari da kuma kula da lamarinsu, ba a son gaggawa da ganganci a cikin harkokin mulki.

Ya ce dokokin kungiyar ECOWAS sun tsara cewa duk abin da ya faru a cikin gidan wata kasa bai shafi wata kasa ba, saboda haka a bar mutane su zabi hanyar da suke so, don haka idan aka ce za a afka wa kasar Nijar da yaki domin wani abu da mutanen kasar suka yi, wannan babban kuskure ne.

Ya kara da cewa kar gwamnati ta sake da dauki wannan mummunan hanyar, sai dai a ja kunnansu kan wannan juyin mulki. Ya ce ‘yan siyasan afirka har yau ba su balaga ba, suna nan a matsayin kananan yara wanda suke kuntata wa mutanensu ta hanyar rashin kula da jin dadin al’umma.

Dakta Gumi ya ce idan da ‘yan siyasan suka balaga za su iya gudanar da harkokin mulki ta yadda babu wanda zai yi musu juyin mulki.

Har ila yau, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya yi gargadin cewa Faransa da Amurka ne suke son amfani da Nijeriya wajen kai wa Nijar hari, yana mai bayyana yadda kasashen biyu suka zama danjuma da danjummai.

“Ko da ‘yan kudancin Nijeriya ba sa Kallon Nijar da Nijeriya a matsayin daya, su ‘yan arewa haka yake a wurinsu… Gazargamu ita ce shalkwatar Daular Kanem Borno har yanzu akwai ragowar gine-gine na tarihi, ko da aka kacancana mu ba a rushe mana tarihi ba, wasu yankuna suna Nijar wasu suna Nijeriya… Haka idan aka duba iyakokin Daular Shehu Usman daga Borno zuwa Sakkwato, kowane gari an dare shi gida biyu. Idan aka duba iyakokin Hadejia, wasu an raba an ba Nijar. Akwai wani yanki na Gumel da yake Nijar. Idan ka tsallaka iyakar kasa ta Maigatari har yanzu dai kana cikin yankin Gumel ne amma an bai wa Nijar. Haka nan Daular Gobir an kacancana ta ce a tsakanin Nijar da Nijeriya… Mahaifar Shehu Usman Danfodiyo, Marata a Nijar take. Dangantakar da ke tsakanin Nijar da Nijeriya ta fi karfin tunani,” in ji sanarwar da ya fitar.

Wakazalika, Majalisar Malaman Nijeriya ta nemi a dakatar da batun daukar matakin soja domin warware matsalar ta Nijar.

Malaman sun ce matakin ba zai haifar da sakamako mai kyau ga kasashen biyu ba. Sun nemi kowane bangare da ya dauki matakin salama cikin yanayin diflomasiyya domin tallafa wa Jamhuriyar Nijar da mutanenta.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da kungiyar ta yi, inda shugabanta Aminu Inuwa Muhammad da sakatarenta, Injiniya Basheer Adamu Aliyu suka fitar da wata sanarwa a kan matsayar da suka cimma.

“Yana da kyau gwamnatin Nijeriya ta sake yin duba kan kokarin da ta ke yi, sannan kuma ga barazanar tsaro ta ko ina, wadanda su ke ta tatse ‘yar lalitar kasar, kada a afka mu cikin wani rikici da za mu iya kaucewa, kawai don mu farantawa wasu kasashen duniya a siyasance.”

Malaman da suka sanya hannu kan takardar a yayin zaman sun kai 25 daga sassa daban-daban na kasar nan, inda suka yi fatan cewa barazanar da ake gani a zahirance ba zai kai ga janyo barakar zaman lafiya a tsakanin Nijeriya da Nijar ba.

Majalisar ta jadadda goyon bayan matakan diflomasiyya da a ka fara dauka ta hanyar aikewa da wakilai domin zama da jagororin sojin juyin mulkin Nijar don tattaunawa cikin salama.

“Juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar da ma duk wadanda a ka yi a sauran kasashen yankin SAHEL abun takaici ne, kuma ya cancanci duk masu ra’ayin dimokuradiyya su yi tir da shi da ma duk masu neman zaman lafiya a duniya.

“Duk da cewa mutane da dama na fifita dimokradiyya da tsare-tsarenta, amma hanyar samar da shugabanci na gari, abu ne da ya kebanci mutanen kowace kasa su kadai. Don haka damar mutanen Jamhuriyyar Nijar ce su bi duk hanyoyin da su ka ga sun dace domin dawo da dimokradiyya a kasarsu, idan sun ga hakan ya dace; kuma duk wani kokarin da wani zai yi, a ko ina yake, matukar ba mutanen Nijar ba, abu ne da zai yi karan tsaye ga dimokradiyya da sunan samar da dimokradiyya.” In ji majalisar.

 A ranar Juma’ar makon da ya gabata, manyan hafsoshin sojin wasu kasashen yammacin Afirka sun amince da daukar matakin soja idan har aka kasa shawo kan lamarin ta hanyar diflomasiyya.

Hafsoshin sojojin sun hada da na kasashen Togo, Sierra Leone, Senegal, Nijeriya, Ghana, Liberiya, Guinea Bissau, Gambia, Cote D’iboire, Cabo Berde da kuma Jamhuriyar Benin, wanda suka bayyana haka jim kadan bayan ganawar da suka yi a Abuja.

Domin mayar da martani, gwamnatin mulkin sojar a Jamhuriyar Nijar ta rufe sararin samaniyar kasar sakamakon barazanar daukar matakin soji da kungiyar ECOWAS ta yi.

Wannan lamari na juyin mulki ya kara dawo da hannun agogo baya, a daidai lokacin da kasashen waje ke ci gaba da kwashe ‘yan kasarsu daga Nijar tare da yi musu gargadin kar su kuskura su ziyarci kasashen Burkina Faso da Mali, wanda kasashe ne da sojoji suka yi juyin mulki a yankin Afirka cikin ‘yan shekarun nan.

Jamus da Italiya dai sun yi kira ga ECOWAS ta kara tsawaita wa’adin da ta bai wa sojojin juyin mulkin na dawo da mulkin dimokuradiyya.

Tuni dai kasashen Mali da Burkina Faso suka ayyana goyon bayansu ga sojojin juyin mulkin na Nijeriya yayin da suka bayyana cewa afka wa Nijar da yaki tamkar afka musu ne kuma ba za su rungume hannu suna kallo ba, za su taya Nijar.

Malamai
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Kallon-kallon: Kungiyar ‘Yan Kwadago Da ‘Yan Nijeriya

Kallon-Kallo: Kungiyar Kwadago Da ‘Yan Nijeriya (2)

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.