Taron da aka gudanar a ‘Co. Roscommon’, ya mayar da hankali ne a kan yadda masu kiwon Akuyoyi za su inganta garken da suke kiwon tumakansu, musamman tumakan da suke kiwatawa; don samun kudin shiga.
Mahalarta taron da dama, sun taru ne a cibiyar gudanar da bincike kan kiwo na kasa ‘Teagasc’ (NFS).
- Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar KasarÂ
- Zaben Fitar Da Gwani Na APC A Edo Ya Bar Baya Da Kura
An gudanar da wannan taro ne a ranar 23 zuwa ranar 25 a otel din Athlone Springs.
A jawabinsa a gurin taron, Farfesa O’Mara ya ce, fannin kiwon tumaki na da muhimmanci matuka, ganin cewa namansu da aka fitar zuwa ketare a shekarar 2023, an samu kudin shiga da suka kai kimanin Fam miliyan 440.
Acewar O’Mara, babbar manufar da taron ke son cimma shi ne, yadda za a kara habaka kiwon tumakai da kuma kara bayar da damar yin gasa.
Shi kuwa Dakta Tim Keady ya gabatar da kasida a wajen taron, kan yadda za a lura da abincin da ya kamata a ciyar da tumaki da kuma illolin da zai shafe su wajen ciyar da su a lokacin da suke dauke da juna biyu.
Ya kara da cewa, a lokacin da tunkiya ke da juna; sannan ne ‘yarta ke fara girma.
A cewarsa, kashi 60 cikin 100 na ‘yar karamar tunkiyar da ke mutuwa, na afkuwa ne a tsakanin cikin awa 24 na haihuwarta.
Ya kara da cewa, kashi 70 cikin 100 na ‘yan tayin tunkiya na girma ne cikin mako shida na daukar juna biyu.
Keady ya bayyana cewa, bayanai sun nuna cewa, yawan nauyin haihuwa na kai wa daga kilo 6 ko 5.6 na tagwayen tinkiya ko daga kilo 4.7 na tunkiyar da ke haihuwa da yawa.