Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da ginin Radio House da aka gyara a Abuja, wanda ke nuna wani babban mataki na dawo da muhimman ababen more rayuwa da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.
Da yake zagaye don duba ginin mai hawa 14, ministan ya bayyana halin lalacewar da ginin ya shiga har tsawon kusan shekaru 20.
- Kotu Ta Sake Bayar Da Belin Tsohon Gwamnan Kogi Kan Naira Miliyan 500
- Tallafin Wutar Lantarki Ya Kai Naira Biliyan 199.64 A Nijeriya – NERC
Ya ce: “Lokacin da na zo nan, wurin nan ya lalace— na’urorin esi ba sa aiki, lif na hawa ba ya aiki, kuma ma’aikata na hawa har hawa tara ko goma don isa ofisoshin su. Hatta banɗakuna sun lalace; wannan bai dace ba.”
Ministan ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa gaggawar amincewar da ya yi na kuɗaɗen da suka ba da damar gyaran ginin, wanda ke ɗauke da ma’aikatar da kuma Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya.
“Bisa taimakon Shugaban Ƙasa, mun mayar da wannan ginin ya zama wurin aiki mai amfani kuma mai inganci, na’urorin esi suna aiki, dukkan lif suna aiki, kuma kayan aikin sun zama na zamani. A karo na farko cikin kusan shekaru ashirin, Radio House ya dawo aiki, kuma ma’aikata suna farin ciki.”
A cewar Dakta Suleiman Haruna, Daraktan Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare, wannan aikin ya dace da burin Shugaba Tinubu na zamanantar da ababen more rayuwa na aikin yaɗa labarai a duk faɗin ƙasar nan.
Ministan ya jaddada cewa ana ci gaba da ƙoƙarin yin irin wannan gyaran a tashoshin Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN) da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) da ke Kaduna, Legas, da Inugu.
Ya ce: “Muna dawo da darajar kadarorin yaɗa labarai na Nijeriya kamar yadda suke a da. Wannan ba kawai gyaran gine-gine ba ne; yana nufin mayar da masana’antar kafofin watsa labarai na Nijeriya ta dace da mafi kyawun masana’antu a duniya.”
Ministan ya kuma yi kira ga ma’aikatan da su yi amfani da wannan tagomashin da gwamnati ta bayar ta hanyar yin aiki da ƙwazo da ƙwarewa.
Ya ƙara da cewa, “Yanzu da ake ba mu abubuwa masu yawa, dole ne mu ma mu mayar da martani ta hanyar tallafa wa burin Shugaban Ƙasa na farfaɗo da martabar Nijeriya.”
Ya jaddada muhimmancin ƙwararrun ‘yan jarida wajen bunƙasar ƙasa, tare da alƙawarin kare yanayin aiki mai kyau, wanda ya haɗa da samar da tsarin albashi da ya dace da matsayin su.
Idris ya ce: “Shugaban Ƙasa yana ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa don kula da dukkan ɓangarori, amma saboda rawar da kafofin watsa labarai suke takawa da kuma haɗarin da ke tattare da aikin, muna fatan ganin ‘yan jarida suna samun tsarin albashi da ya dace da irin aikin da suke yi wa ƙasar mu.”
A nata ɓangaren, Shugabar Kwamitin Haɗin Gwiwa na Ma’aikata a ma’aikatar, Kwamared Chika Ukachukwu, ta yaba da aikin gyaran da aka yi, tana mai cewa kyakkyawan yanayin aiki da aka yi zai ƙarfafa wa ma’aikata gwiwa.
Ta kuma miƙa kyautar Gwarzon Jagoranci ga ministan a matsayin yabo bisa jajircewar sa da sadaukarwar sa wajen cimma burin ma’aikatar.
Taron ya samu halartar Muƙaddashin Babbar Sakataren Ma’aikatar, Comfort Ajiboye, da Darakta Janar na FRCN, Alhaji Muhammad Bulama.