Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Barkanku da Sallah da fatan kowa ya yi Sallah lafiya, kuma da fatan ba a ci nama da yawa ba, Allah ya maimaita mana, Amin. Shafin Taskira shafi ne da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, domin tattaunawa akai. Sai dai a yau shafin namu zai yi duba ne tare da maida hankali kan shagulgulan bikin sallah wanda yake gudana a yanzu. Inda shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin matasa game da yadda bikin Sallah ya gudana a nasu guraren, tare da jin irin kwalliyar da suka gudanar a ranar sallah da kuma wadda za su yi a nan gaba, ko matasa sun taya iyayensu da ‘yan uwansu aikin Sallah?, Wanne tanadi aka yi wa abar kaun ko abin kauna a ranar sallar da ta gabata ko a yanzu?, shin an kai ziyara gidan ‘yan uwa da abokan arziki ko tukunna dai?. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
TSOKACIN TASKIRA
Sunana Mansur Usman Sufi Marubucin littafin Karshen Zalunci daga Jihar Kano:
Gaskiya bikin sallah a unguwarmu ya gudana cikin lumana da annashiwa, nayi wanka na sanya sabbin kaya da turare, yayin da na isa masallaci na samu sallar idin babban sallah bayan na saurari huduba da liman yayi mai ratsa zuciya, liman yayi layya.
Inda na koma gida nayi tawa layyar. Sannan na tafi zuwa gidan ‘yan uwa domin sada zumunci. Na sanya shadda da hula da takalmi. Bayan na dawo na samu shayi da abincin gargajiya. Na taya mama yanka nama, mun yi dambun nama da dafaffe da sauran su. Tana din da na yi wa ‘yan uwana shi ne zan roka masu shiriya da lafiya da dukiya a wajen Allah, domin wannan lokaci ne na karbar addu’a. Ina shirin ziyara sosai dai-dai abin da ya sawwaka, bayan wadda nayi ta ranar sallah.
Sunana Habiba Mustapha Abdullah daga Jihar Kano:
Biki yayi biki, sallah rana ce ta farin ciki tare da nishadi mun yanka Rago da fatan kowa ya samu abin sawa a baki, mun yi shiga ta alfarma tare da farin ciki a fukokkimu mun dawo daga idi mun ci dabino da Kwakwa. Mun ta ya iyayyenmu aikin Sallah da kuma ‘yan uwa. Na yi wa saurayina tanadin abincin sallah shi ne kyauta ta farko da na fara bashi wadda ya ci a gaban idanuna. An yi yawon sallah gida-gida da ma wajen shakatawa dan ‘yan uwa tare da nuna farin ciki a zuciyar mu, na ci ado na sha kwaliya ina jiran zuwan shagaban kasan dake mulki a cikin zuciyata, mu tafi yawon sallah. Matar aure ku yi hakuri ku bar mana mazajenku saboda yawon sallah, in dai sallah ta wuce ya yi shekara bai fito ba. Daga taku mai saku dariya dare da rana.
Sunana Yakubu Producer Gwammaja mai kamfanin Gwammaja Entertainment daga Jihar Kano:
Mun yanka dan karamar Tinkiya sakamakon tattalin arziki da shugabanni suka saka mu, ada muna yanka SA har biyu, amma yanzu sai godiya. Na sa fararen kaya jallabiya doguwar riga na ci tuwan shinkafa shi ne best food dina, tabbas nayi tsire nasa an yi min nama tomass. Na bawa kannena sabbi kudi saboda kada su yi roko ko yawon kwadayi. Gaskiya bana yawo da sallah, sakamakon na girma, kuma bana san warin babbarkar nama, ko warin tumbin sallah, yana sa min ciwon kai.
Sunana Abba Pash daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment Kannywood):
Mun gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki, ga abubuwan kallo abin sha’awa musamman yadda aka yanka San gidan mu kowa na kallo yara da manya. Nayi shigar farar shadda da babbar riga, na je nayi Sallahr Idi na dawo gida na ci Waina da Alkubus Miyar Taushe. Daga nan muka fara aikin nama ‘yan matan gidanmu sun soya, wani kuma suka yi dambun nama da shi, can gefe kuma kanina ne yake gasa Tsire, shi ma. Bayan mun gama aikin nama daga nan na kara wanka na canza kaya na na fita domin ziyara gidan ‘yan uwa da abokai, washegarin Sallah ma na tashi na shirya na tafi kallon wasan Sallah a Fabs dake Nassarawa GRA ni da abokai na.
Sunana Siyama Abdul daga Jihar Kano:
Toh gaskiya bikin Sallah anan unguwarmu ya kasance abun burgewa da ban sha’awa, dan yadda kowa yake hada-hadar sa da kuma yanke-yanke na dabbobi iri daban-daban, kuma a taru a yi ta kallo. Mu dai mun yanka katoton Sa da Raguna biyar dan har sai da san ya zubar wa da mutane uku hakora, wani ya zubar masa da hakori daya, wani biyu, wani daya gashi nanne dai. Shagulgulan ranar gaskiya sun kayatar da mu. Ni dai na sa Hijab da Doguwar rigar shadda da sarka, dan kunne, awarwaro da takalmi da kuma Dadduma ban saka jaka ba. Bayan mun dawo daga masallacin idi kuma abin da na fara ci shi ne ‘Fried Rice’ da ‘Pepper Chicken’ da ‘Co-slow’ da Lemon Kwalba. Sosai ma kuwa dan dani aka fara aiki kuma aka gama aikin, mun yi suyar nama, Dambun nama, Tsire, da kuma Kilishi. Na yi wa kawayena da Cousins dina tanadin ranar da za su zo gidanmu a ci a sha ai nishadi da dai sauransu. Eh! toh, ana kan shirin zuwa guraren, tunda babbar sallah ce ba a fiya ziyara ran daya da biyu ga sallah ba, saboda wadansu ba gama aikin su kai ba, muna shirin zuwa gurin wasanni da gurin Tarihi, sai gidajen ‘yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa.
Sunana Real Hassan King daga Jihar Katsina Dutsanma LGA unguwar kudu (Gwammaja Entertainment):
Mun yi bikin sallah cikin farin ciki da soyayyar juna hadi da annushuwa tare da al’ummar yankinmu, mun yanka Kosasshen Rago mai launin ja da kuma fari. Na sanya fararen tufafi tare da bakar Dara, hadi da bakin takalmi da farar Azurfa da bakin Agogo dauke da jar Darduma. Na ci tuwon shinkafa miyar alayyahu tare da bushasshen kifi. Na taya Anti Zainab aikin suyar naman Sallah. Naman sallah an soya, wani an yi danderun, wani kums an dafa, wani an kai wa Hajiya Kaka, kai da kafa an kai fatar masallaci. Na tanadar wa Khadija da zazzafar Azurfa, tare da chocolate, hadi da barka da sallah. Na fara zuwa gidan kakar mu, sannan gidan uncle Yakubu, sannan gidan Yaya Ahmed da Anti Nabila, sai gidan su budurwata Khadija.
Sunana Abdulrrashid Haruna daga Jihar Kano:
Toh Alhamdulillah bikin Sallah ya gudana wajan mu daidai da yadda ran mu yake so cikin nishadi da walwala da godiya ga ubangiji. Eh! toh ban yanka ba amman an yanka mana Raguna Alhamdullilah. Alhamdulillah na sa Jallabiya launin fari. [Dariya] Bayan dawowata na samu Tuwon Shinkafa da miyar Taushe mun yi musabaha. Eh! na taya aiki sosai, an soya naman sannan an dafa da dai sauransu, Wow! abin ba misali farin cikin ba misali Allah dai ya maimaita mana, Amin. Tanadin da nayi kafin Sallah tanadi ne na musamman, amma na aiwatar. Mun je ziyara sosai, kamar guraren shakatawa haka da sauransu.
Sunana Abbale Ibrahim Ismail daga Jihar Kano Jogana:
Bikin sallah to da farko dai ya sa ni farin ciki mara misaltuwa duba da yadda aka kawo rago aka yanka, mata da maza manya da yara sun ci kwalliya sunf ito fresh abin su suna daukar photos suna zagaye gari. Ni ma dai ba a bar ni a baya ba, duba da yadda na yi shigata na fito na halacci masallacin idi hanyata ta zuwa masallaci nan abin ya sani nishadi, da kyar mutane suke wucewa sabida cunkuson mutane kowa yana son zuwa, godiya ga ubangiji ma sha Allah. Game da abinci kuwa bayan na dawo na sami tuwo da nama na ci, ma sha Allah Allah mun gode maka. Eh! gaskya da ni aka yi ayyuka wajan fito da ragon zuwa yankashi, tom gaskiya tanadin da akayi wa baby na hmm ba zai fadu ba itan da aka yi wa kadai za ta iya bayyanawa mutane shi. Na ziyaraci Brigade, Dorayi, Bayero Mall, nan gaba ina so zan je Shoprite da kuma Kaduna.
Sunana Sulaiman Rijiyar Zaki daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment Kannywood):
Na tsaya na taya aiki kafin na fita, Naje wajen hauwan sallah daga nan na je wajen abokina,Na tanadar wa budurwata barka da sallah, sannan za mu je mu gaida family ta.
Sunana Umar Aminu (Kash Out) daga Jihar Adamawa:
Alhamdulillah bikin Sallah yayi kyau sosai kamar hawan Arfa, abun layya mun yaka Rago. Gaskiya an sha kwalliya yadda aka saba amma ta bana ta fi ta kowani shekara. An taya aiki sosai, nayi fidar Ragona iri daba-daban ba za ma su misaltu ba, an yi aiki sosai. Na tanada wa masoyiyata rana guda wadda za ta zama ranar ta ta ce ta musamman. Mun je gurare da dama amma an je bakin ruwa an yi hoto.
Alhamdulillah bikin Sallah yana tafiya yadda ake so, saboda za ka ga manya da yara kowa ya fito da sabbabin kaya, eh! to a gaskiya ni ban yi layya ba, amma iyayenmu sun yanka naman Rakumi da Saniya guda daya wanda za a ci a sha, sannan kuma a raba wa ‘yan uwa da abokannan arziki. Eh! to ni gaskiya a mafi yawancin lokutan ni ina saka farin kaya da hula wanda ake kira da zanna. Kusan duk inda ka waiga za ka ga kowa ya sa sababbin kaya. Bayan mun dawo muka dauki hotuna, sannan aka kawo mana Tuwan Shinkafa da miyar Taushe daga baya kuma aka kawo mana shinkafa da miya. Mafi yawanci idan muka ci muka sha, mukan tube kayan Sallah mu dan yi aikin nama. Mun yi aikin nama sannan mun sarrafa gaba daya, mu bawa makota da ‘yan uwa da dangi, bayan mun gama sai muyi wanka mu tafi ziyara zuwa ga ‘yan uwa. Gaskiya mukan fita da amaryata duk bayan sallah da kwana daya ko biyu donin shakatawa da kuma kai ziyara zuwa ga ‘yan uwa da abokannan arziki, dan wani lokacin mukan kai bayan magriba ba mu dawo ba. Shi ziyar yana da mahimmaci musamman a irin wannan lokacin kusan za ka ga kowa yana zaune a gida, duk gidan da kaje za ka ga mutane, bayan nan kuma mukan je hawan Sallah.