Tsohuwar Shugabar Hukumar Tashohin Jiragen Ruwa Nijeriya NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ta tattauna da wakilin jaridar Punch, ALEXANDER OKERE a kan hamayyar da ta fuskanta a yayin da take shugabantar NPA a matsayinta ta ‘ya mace, da zargin da aka yi mata na bacewar Naira Biliyan 156, da kuma yadda aka sauke ta da irin dangantakarta da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a halin yanzu. Ga dai yadda hirar ta kasance kamar yadda Mataimakin Editanmu Bello Hamza ya fassara:
Fitar da littafin tarihin ki mai suna, ‘Stepping On Toes’, an yi masa tarba iri-iri, shin za ki iya ware maganganun da aka yi kai da suka fi baki sha’awa?
Ba zan ce na mayar da hankali kan mayar da martani ba. A gare ni, abin da yake da muhimmanci shi ne fitar da shi ta fuska daban-daban. Akwai al’amura daban-daban amma ba zan yi martani a kan su ba. domin akwai jami’an gwamnati da suka ba da labarin gogewarsu a cikin ma’aikatun gwamnati yayin da wasu ke ganin bai kamata wasu daga cikin wadannan bayanan a yanzu su kasance kamar hakan ba.
Me ya ja hankalinki kika sanya wa littafin wannan take?
Taken littafin ya yi daidai musamman ganin a yayin gudanar da sauye sauyen da gabatar a NPA na taka sawun wasu da dama, wanda wasu da dama ke ganin na takura musu, a kan haka na zabi sunan littafin, ‘Stepping on toes’.
A cikin littafin, kin bayyana cewa Ministan Sufuri na lokacin, Rotimi Amaechi, ya ba ki mukamin Manajan Darakta na NIMASA amma kika ki karba, a maimakon haka, sai kika ba da shawarar a bai wa Dakuku Peterside. Me ya sa kika ki karbar wannan tayi?
Na ga cewa a wancan lokacin ya zama wajibi a ba da shawara wanda ya zai rike wannan wuri ya zama ya fito ne daga Jihar Ribas saboda sun sha kaye a zaben gwamna kuma ga alamu tawagarsa ba su da wata kwarin gwiwa. Don haka, yana da mahimmanci a ce wanda rike wurin ya zama daga bangarensu ne.
Wasu kuma suna ganin kamar ko wurin ya yi miki kankanta ne, me ya sa kika aikata hakan?
A wancan lokacin NPA ma ba ta kan doron hanya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sake nada Manajan Darakta, kuma da kyar Manajan Daraktan ya kai wata shida. A bayyane yake, kuma babu wata alama da ta nuna za a cire shi don a nada wani.
Ki bayyana a cikin littafin cewa Shugaban kasa a shirye yake da ya rike ki a matsayinki, wanda hakan ya sa aka sabunta wa’adinki na aiki a NPA. Shin kina ganin an yaudari Shugaban kasa ne har ta kai ga ya amince da tsige ki daga mukaminki, bayan tun da farko an nemi lallai a yi miki adalci?
Ba zan san dalilinsa na yanke shawarar nada wani MD ba. Abin da rahoton kwamitin ya kunsa da kuma tuhumar da ake masa kamar yadda na yi dalla-dalla a cikin littafin ya fito karara. Don haka ban aikata abin da suke zargin ba, kuma hakan ya fito fili. Tabbas na ga an yi abin ban mamaki, amma a gare ni ba shi da alaka da sake nada shi a matsayin manajan darakta da kuma batun zargin da ake yi min, na kudaden da ba a san da su ba, kuma babu su, sannan kwamitin ya tabbatar. Wannan shi ne abu mafi mahimmanci da za a lura.
Shin wannan abin da ya faru ya tabbatar miki da jita-jita da ake ta yayatawa cewa ‘yar manuniya ce dake ishara da kasancewarsu a kan hanyarsu ta shiga fadar shugaban kasa?
Ba zan fadi haka ba, domin na ki shiga cikin masu ra’ayi ko hasashen al’amarin da ba ni da cikakkiyar shaidar a kansu. Don haka, ba ni da masaniya kan hakan kuma ba na zaton za kuma a sani.
Lokacin da aka sauke ku, me ya sa ba ku yi kokarin ganin Shugaban kasa ba don ku iya daidaita al’amura ko ya janye batun tsige ku?
Na gana da shugaban kasa sau da yawa, kuma na ci gaba da ganawa da shugaban kasa hatta lokacin da ya nada wani. Saboda haka akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da shugaban kasa. Na shigar da shi a cikin lamarin dakatar da ni kuma ya duba takardun, amma kamar yadda nake ci gaba da maimaitawa, a bangarena ban yi domin na ci gaba da rike mukamina a NPA ba sai na kara tabbatar da cewa zargin da ake mini ba a tabbatar da shi gaban kwamitin ba.
Me shugaban kasa ya ce game da dakatar da ke da kuma cire ki?
Mun tattauna kan al’amuran da suka shafi batutuwa da dama; Na san shugaban kasa tun kafin ya ba ni mukami a NPA; abokin mahaifina ne, don haka yawancin hirarmu ta ta’allaka ne a kan al’amuran sirri ba game da dakatar da ni ba ko kuma batun NPA ba. ni makusanciyar Shugaban kasa ce kuma ina girmama shi.
Wasu mutane za su yi mamakin me ya sa ba ki yi amfani da wannan damar ta ganawarki da Shugaban kasa don tambaya game da hakan ba ko kuma ki nemi daidaita lamarin?
A wurina, daidaita al’amura domin a mayar da ni a kan mukamina ba shi ne ba shi ne mafi a’ala ba, in tabbatar da ana zargina da karkatar da Naira biliyan 165 kuma kwamitin da aka kafa bai tuhume ni ba, wannan shi ya fi muhimmanci a gare ni. Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya kara yi shi ne ya umurci ministar da ta bayyana min zarge-zargen da ake min, wanda hakan ya ba ni dama na fayyace matsayina da kuma kasancewa a cikin jama’a.
Da yawa, da mutane sun yi imanin cewa ba a biya Naira biliyan 165 ba, kuma ba kowa ba ne zai damu ya san sakamakon ba, me ya sa ba ki yi tunanin zuwa kotu ba, watakila ko ki kalubalanci batancin da aka yi muki?
Kun ambaci cewa mutane da yawa sun yi imanin cewa kudaden sun bace. An kafa wani kwamiti kuma ya yi aiki na tsawon watanni takwas don tantance ko ba a biya wadannan kudade ba, kuma kwamitin ya fito ya ce an fitar da wasu kudaden da ma. Don haka, idan mutane za su yi tunanin ci gaba da yada labaran karya duk da cewa kwamitin da Ministan Sufuri ya kafa ya fito da rahoton cewa babu wani abu, na gano cewa karya ne. To ka ga ba zan iya mu’amalantar mutanen da suka dage kan karya ba bayan kuma gaskiya ta yi halinta ba. Abu mafi mahimmanci shi ne, da yadda muka gudanar da aiki a NPA, ba zai yiwu a ce kudin gwamnati ya bace ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka dage kan biyan duk kudaden shiga da aka tara a cikin Asusun Baitulmali.
Wadannan asusu suna a Babban Bankin Nijeriya. Don haka abin zai iya zama batun sulhu ne kawai ba wai a ce wani ya yi sata ba. Kamar yadda na yi bayani a cikin littafin, ana yin sulhu da rarar aiki a karshen kowane aikin tantancewa, kuma yana da mahimmanci yin hakan domin samun daidaito. Kudaden na cikin asusun TSA a babban bankin kasa CBN. Batun zuwa kotu bai dace da sakamakon kwamitin ba.
Mu garzaya kotu a kan me; bata sunan?. Kwamitin ya ce babu wani kudin da ya bata, to me nake kalubalanta, kuma wa nake kalubalantar shari’ar kotu?
Takamaimai waye yake adawa da ke?
Tsohon Ministan Sufuri. Kamar yadda na bayyana a littafina, ya ce min yana so in bar mukamin, kuma a dakatar da ni shi ne matakin farko, a kan hakan kuma yana ganin dakatarwar za ta dore har sai mun kai ga lokacin gudanar da manyan zabuka, ka ga a sannan Shugaban kasa da kowa zai manta cewa an dakatar da ni, shi kuma ya samu abin da yake so ya cire ni ya fitar da ni daga NPA.
Me kike tsammanin shi ne laifinki?
To, kamar yadda ni ma na fada a cikin littafin, watakila ya ji akwai batun rashin biyayya a lokacin da ya ji ina hulda da Shugaban kasa kai tsaye. Akwai wuraren da ya ke da sabanin ra’ayi a kan wasu abubuwa na tsari da na yi sun saba wa ka’idar jagorantar ayyukan saye da sayarwar jama’a. Don haka, wannan yana iya zama dalilinsa, amma a gaskiya baya ga wannan ban san wani dalilin da ya sa zai so a cire ni ba.
Ko dai kina ganinsa kamar yana da girman kai ne?
Ba ni da tabbas kasancewarsa mai girman kai; na tsammaninsa a mutum ne mai tsari. Kamar yadda na yi tsokaci a lokacin taron (zama), duk lokacin da na mayar da amsa ga wasikar da fadar shugaban kasa ta rubuto min, fadar shugaban kasa na karba. Don haka, ko kadan ba a taba ce min kar in gana da shugaban kasa ba ko kuma a ce na mayar da martani ga fadar shugaban kasa a waje cikin kafar sadarwa. Don haka, kamar yadda na ambata a cikin littafina, da yawa daga cikin wasiku da bayanai tare da shugaban kasa, a zahiri fadar shugaban kasa ce ta fara neman Hukumar NPA ta ba da bayanai da kuma karin haske, don haka ban ga wani laifi ba game da amsa bukatun neman bayanai ta hanyar ofishin shugaban kasa ba.
Tsohon ministan ya yi murabus ne domin ya tsaya takarar shugaban kasa, wanda kuma bai samu nasara ba. Shin kina ganin ya kamata shugaban kasar ya sake nada shi ganin cewa suna da kusanci?
A gaskiya ba ni da wani tunani a kan haka; yana da nasaba ne da abin da Shugaban kasa ya yi imani da shi, cewa shi ne mafi alheri ga fannin.
Kin yi farin cikn rashin nasarar da ya yi
Na goyi bayan wanda ya yi nasara.
Shin kin goyi bayan Bola Tinubu?
Kwarai kuwa
Kina ganin Amaechi zai zama shugaban kasa nagari idan da ya lashe zaben fid da gwani da na shugaban kasa?
Ina tsammanin rashin tabbatar da tikitin ya magance hakan. Ni dai babu ruwana da shi. Wakila kuma sun zabi Tinubu.
A yanzu mecece dangantaka tsakaninki da Amaechi?
Kamar yadda na ambata a cikin littafina, na gode masa da ya ba ni wannan aiki kuma ina da kyakkyawar dangantaka da shi.
Yanzu kuna yin magana da shi?
Eh, na ganshi a wani biki, muka yimagana. Amma dai tun da aka fitar da littafin ban gan shi ba amma a bayan barina ofis, na hadu da shi a wasu lokuta kuma mun yi magana da shi.
Shin kun yi magana game da sabaninku?
A’a, ba mu tattauna a kan wani bambance-bambance ba. Babu wani bukata; Ina tsammanin hukuma ce kawai ta hada mu. Ba na la’akari da abin da ya faru a matsayin bambance-bambance. Ina la’akari da shi a matsayin wani abu mafi hukuma dangane da matsayinsa na abin da ya kamata a yi, kuma ina da hangen nesa na. Abin da na tattauna a cikin littafin abubuwa ne da ke cikin jama’a. Ba na tsammanin akwai da yawa daga cikin abin da ke cikin wannan littafin da babu shi a kafofin yada labarai na jama’a ba a cikin shekara guda da ta wuce. Gaskiya ce da aka tattara cikin littafi guda. Ina tsammanin hakan ne musabbabin da ya haifar da bambancin. Amma ba na tsammanin, alal misali, minista ko wani zai yi mamakin gaske idan sun kasance suna bibiyar gyaran NPA tun daga lokacin da na zo.
Shin akwai wadanda suke ganin ba ki taka wata muhimmiyar rawar da ta dace ba a siyasa a matsayinki Majanar Daraktar NPA?
Abin da ban fahimta ba shi ne taka rawa a siyasa ta wace hanya, misali, taka rawa a siyasar cewa, INTELS su shiga cikin tsarin hakar kwangila ko kuma suna cewa ba ku tsawaita kwangilar shekara guda bayan ya kare, Ban ga abin wata siyasa da ya wuce samun kamfanoni su yi abin da ya dace don amfanin gwamnati da bin dokokin da ka’idoji ba.
Shin kin fuskanci matsin lamba daga mutane kan lallai ku yi sulhu domin maslahar aikinki?
Lallai kam! Amma ba na yin sulhu.
Kina zaton kin taka yatsun Amaechi kenan ko?
Ba na tsammanin na yi. Idan mutane sun yi imani da hakan, to hakan ne ya kasance. Abin da ke da mahimmanci shi ne a duba wadannan ayyuka da na tsaya tsayin daka tare da su daidai da yadda yakamata a tafiyar dasu. Tashoshin Ruwan Nijeriya, musamman ma na Legas, na cike da matsaloli da dama, tun daga kan cunkoson jiragen ruwa zuwa lokacin da jiragen ruwa ke daukar kaya da kuma zargin karbar kudade da hukumomi daban-daban na can ke yi. Ta yaya al’amura suka koma irin wannan abin kunya?
Yayin da kake magana game da cunkoso a tashar jiragen ruwa, wanda zai haifar da cunkoso game da shiga tashar jiragen ruwa da fita, a cikin littafin na bayyana kalubalen da muke da shi da kuma mafita da aka samar. Na sanya tsarin kira na e-call lokacin da nake wurin don magance matsalar cunkoson shiga tashar jiragen ruwa. Mun kuma yi aiki a kan kaddamar da fitar da kaya ta amfani da hanyoyin ruwa, ta hanyar amfani da jigilar kayayyaki masu yawa – an shigar da tsarin dogo. Don haka duk wasu ayyuka ne na neman magance matsalar cunkoso da aka tura da farko a yankunan Tin Can da Apapa. Wadancan mafita suna nan kuma an samu nasara; an ga raguwar yanayin cunkoso a yankin Apapa.
Kina nufin tashoshin jiragen ruwa suna da inganci a yanzu?
Ingancin ya inganta, ba tare da wata shakka ba, tare da kaddamar da na’urorin daukar hoto. A lokacin da nake can, babu na’urar daukar hoto a tashoshin jiragen ruwa, don haka kowace kwantena sai da hukumar da ke da alhakin yin hakan ta duba. Don haka Hukumar Kwastam da kowace hukuma za ta bude duk kwantenar da ta zo. Amma da shigar da na’urorin daukar hoto, duk wata kwantena da za ta wuce na’urar daukar hoto na kallonta, kuma hukumomin gwamnati na iya zama a ofishinsu su duba su yi lissafin da ya dace.
A zahiri, ya kamata mutane su yi farin ciki game da hakan, kina ganin wadanda abin ya shafa suna farin ciki?
Kowa yana so ya ga ci gaba a kayan aikin tashar jiragen ruwa. Abubuwan da ake amfana a aikin gwamnati suna ko’ina cikin hukumomin gwamnati. Na’urar daukar hoto tana nufin karancin sa hannun dan’Adam. Inda aka sami karancin sa hannun dan adam, sai ku samu hanyar da za a dasa na’urar. Don haka a zahiri, kaddamar da hanyoyin intanet yana rage wahala a cikin tsarin.
Tsawon lokaci har zuwa shekarar 2020, an samu rahotannin da aka tabbatar da cewa an kwashe kwanaki 21 zuwa 25 ba a yin amfani da jiragen ruwa a dalilin karbar kudaden da hukumomin gwamnati ke yi. Me ya sa rashin da’a ya yi yawa a cikin tashar tashar jiragen ruwa?
Batun tuhume-tuhumen na da nasaba ne da tsawon lokacin da abin da ke can ke fitowa. Lokacin da ake ajiye kaya kafin a sauke su aiki ne da dole sai an samu sarari a cikin kowace tasha, wanda shi ne ake gudanar da aikin sharewa cikin sauri. Don haka bin wasu shirye-shiryen da muka tura, mun sami dai sauki a lokacin da muke jiran jiragen ruwa.
Har zuwa lokacin da kika tafi, burin samun tashar jiragen ruwa na Gabas mai aiki ya kasance a mafarki, alhali yana iya taimakawa wajen rage cunkoson tashoshin jiragen ruwa na Legas. Kina tsammanin akwai dakarun da ke cin gajiyar wannan rashin aiki?
A’a, bana tunanin haka. Ina ganin cewa, hadin kai tsakanin tashar jiragen ruwa ta Gabas da kuma inda za a kai kaya na karshe ne ke da kalubale yadda mutane ke amfani da wadannan wuraren, dangane da yadda kaya ke tafiya daga Onne (a cikin Jihar Ribas) cikin sauki zuwa na karshe, da kuma ta yaya tasirin wuraren da ke can. Alal misali, wasu manyan jiragen da muke da su a tashar jiragen ruwa na Gabas ba sa barin manyan jiragen ruwa, wanda ke hana manyan jiragen ruwa zuwa wurin. Haka nan, hadin kai zuwa wasu wurare, kamar yadda na ambata, kalubale ne. Ba na ganin wani karfi a can; batu ne na abin da ke aiki kuma yana cikin maslaha ga wanda aka aika.
Ya kamata NPA ta zama hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa. Kina ganin zai fi kyau idan NPA tana da wasu hukumomi masu karfin ikon tilastawa?
A’a, aikin NPA, kamar yadda yake, ya isa. Bangaren tsaro yana tare da hukumar da ke da fasaha da ilimin yin hakan; don haka NPA tana da wuraren tsaro na wadanda ke magance bukatun tsaro cikin gaggawa a cikin yanayin tashar jiragen ruwa. Bayan haka, NPA ba ta bukatar samun wani abu a waje da abin da ake iya samu.
Lokacin da abubuwa suka tabarbare tsakanin ku da Amaechi, me ya sa Malam Nasir El-Rufai bai sa baki ba tun da ya hada ku duka biyu?
Ina da kyakkyawar alaka da shi (El-Rufai). Ya sa baki. Ya yi magana da Amaechi, ya yi magana da ni, kuma ya yi kokari ya sami matsaya. Mallam El-Rufai tabbas ya karanta littafin kuma yana nan lafiya. Wannan shugabana ne.
Yawan mata masu mulki a Nijeriya ya yi karanci, kuma a majalisa ta 10 da ke tafe, sannan yawan mata ya kara raguwa. Shin wannan matsalar ta Nijeriya ce, ko kuwa laifin mata ne da ba sa taimakon ‘yan uwansu?
Ina ganin da a zahiri ya kamata a sami karin mata da za su fito cikin wannan da’irar siyasa. Adadin ba shi ne abin da muke fata ba. Muna sa ran ganin yadda za mu inganta ta hanyar samun karin wadanda aka nada a mukamai masu mahimmanci don cike gibin da aka samu daga mukamai masu zabe. Na’am, akwai takura a kan al’amuran addini da na al’adu wadanda ke kawo kalubale ga mata su fito siyasa.
Daya daga cikin batutuwan da kika tabo shi ne cewa marigayi Isa Funtua ya yi shakkun iya tafiyar da hukumar NPA. Kina ganin hakan na da alaka da mayar da mata saniyar ware a harkokin mulki a Nijeriya ko akwai wasu dalilai?
Yana da dalilin fadin hakan kuma ba batun al’adu ba.
Shin kuna da yakinin cewa gwamnatin Bola Tinubu wadda kema kika yi yakin neman zabe za ta yi abubuwa daban-daban da za su shafi nada mata da yawa a gwamnatinsa?
Ina jin zai yi. Mutum ne mai son ganin ci gaban mata, don haka ina da yakinin cewa zai sanya mata da yawa a majalisarsa. Ina fatan yin aiki da shi, idan aka ba ni dama, da yi wa gwamnatin APC hidima.
Game da zaben gwamnan Adamawa, ‘yar takarar jam’iyyarku, Uwargida Aishatu Binani, ta karanta jawabin karba a lokacin da aka ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara ba a bisa ka’ida ba, wasu mutane na ganin hakan ya rage darajar mata, kuma hakan ya zama kamar yankan kauna. Me kike tunani?
Ina ganin abin da ya faru shi ne an yi zabe wani bangaren da ba a kammala ba. Wani bangaren kuma aka kammala yi aka bayyana sakamako dan takarar (wanda ya yi nasara). Don haka, a gare ni, wannan abu ne da ya shafi duba dokokin zabe da kuma yadda za a gudanar da sahihin sakamakon zabe daga APC har na daya jam’iyyar wacce ba jam’iyyata ba wacce bayyana ta yi nasara. Za mu duba tsarin don ganin ko akwai sahihanci a cikin aikin.
Shin, kamar sauran mutane, kina jin bai kamata Binani ta karanta jawabin amincewa da lashe zabe ba lokacin da Kwamishinan Zaben ya bayyana ta a matsayin wacce ta yi nasara bayan ba shi da ikon yin hakan?
To, ina ganin zabinta ne da masu ba ta shawara da abin da suke ganin ya dace a doka.
Kenan sun ba ta gurguwar shawara kenan?
Ban sani ba, ta yadda za su iya samun madogara ta shari’a da suke kallo amma za ka ga ai INEC ta soke sakamakon. A karshen wannan rana, alkalan zabe ne ke tantance abin da ya dace ko a’a.
Wadanne kalubale kika bayyana a hukumar NPA da kike ganin gwamnati za ta yi gaggawar magancewa domin inganta tsarin tashar jiragen ruwa?
Ina tsammanin batutuwan sun kasance iri daya, batutuwan cunkoso, hanyoyin tashar jiragen ruwa da tabbatar da inganci wajen jigilar kayayyaki. Wadancan batutuwa ne da ke dawwama da bukatar samun hadin kai zuwa kasa, shigowa, da fita, ta amfani da tsarin sufuri na tsaka-tsaki, da kuma duba bututun mai don rarraba kayayyakin mai. Wani muhimmin bangare na cunkoso a Apapa shi ne aikin gonakin tanki a can, ba a hada shi da ayyukan tashar jiragen ruwa ba. Abin da wasu ba su gane ke nan ba. Idan kun yi amfani da bututun da aka tura zuwa can don jigilar kayan mai, ba za mu sami wadannan matsalolin ba. Don haka, inganci a tashoshin jiragen ruwa yana nan; kawai don habaka mahimman alamun aiki na samun abubuwa.
Yaya kika ji an nada daya daga cikin daraktocinki don ya maye gurbinki?
Ban damu da komai ba, shi darakta ne da na yi aiki da shi tsawon shekaru biyar. Idan har wani zai iya ci gaba da gyare-gyare, zai iya.
An yi maganar ana watsi da kwantenoni a tashar jiragen ruwa, menene kike ganin zai magance wannan?
Yin watsi da kwantena yana da alaka da share kaya. Wasu daga cikin kayan ana watsi da su ne saboda ba a share su ba, kuma aiki ne na hukumar kwastam. Don haka, akwai wuraren da ake dakon kaya a Ikorodu inda ake kai kayan dakon kaya, don haka hukumar kwastam ta yi gwanjonsu. Wadannan fagage ne da ke hannun Hukumar Kwastam da Hukumar NPA.
Duk da sauye-sauyen da ka samu, wasu sun zarge ki gami da yin amfani da karfin mulki ta hanyar da aka ce ka soke kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba. Yaya za ki mayar da martani kan hakan?
Wasu daga cikin kwangilolin da na ambata a cikin littafina da dukan tsarin an yi dalla-dalla a can. Wannan shi ne abin da ake gani cewa an daina kwangila, kuma ministan ya ji saboda labarin da aka yi a kafofin yada labarai cewa an daina kwangilar, ya sanya alkalami a takarda ya ce an daina kwangila lokacin da kwangilar ta kare. Wannan wani bangare ne na rashin fahimta da ya sa wani minista ya rubuta cewa an daina kwangilar ne lokacin da ba haka ba.
Galibin ‘yan Nijeriya sun yi amanna cewa akwai cin hanci da rashawa da dama a harkar tashoshin jiragen ruwa. Ta yaya za a rage shi, ko kina ganin an wuce gona da iri?
Aiwatar da hanyoyin intanet don rage sa hannun dan’Adam yana da mahimmanci. Na’urar daukar hotan takardu, tsarin kira na kafafen sadarwa, dandali na biyan kudi da duk wannan na iya magance cin hanci da rashawa a fannin. Najeriya za ta iya tare da shugabanci na gari.
Shin kuna ganin harin da aka kai a cibiyar NPA a lokacin zanga-zangar #EndSARS ko za ki iya fadar dalilin yin hakan?
Zan iya cewa an yi niyyar hakan ne da nufin rusa wani tsarin aiki. Amma musamman kamar yadda na ambata a cikin littafin, an lalata hotona ciki har da na shugaban kasa. Na ji a raina cewa akwai damuwa game da kundin tsarin mulkin hukumar inda ya zamto babu wani mutum daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma (na zartarwa da wanda ba na zartarwa ba) kuma duk wannan na iya haifar da wata kiyayya ganin cewa babu nasu a ciki.
Kina ganin za ki iya yin aiki da Mista Amaechi nan gaba ko kuma har yanzu ba ki yafe masa ba?
Ba ni da wata matsala tare da shi kuma ba na tsammanin akwai wani abu na bukatar neman gafara a cikin wannan. Batun tsarin aikin gwamnati ne ba batun yafiya ba. Ba na sirri bane, aiki ne kawai.
Shin kina ganin wasu kalubalen da kuka fuskanta lokacin da aka nada ki sun shafi jinsinki ne, musamman kasancewarki mace ta farko da ta shugabanci NPA?
Ba ni da tabbacin an tauye hakkin mace. Batun ni mace ce a zahiri ai dama mata ne suke yi. Kasancewata ‘yar Arewa, ganina ina matashiya, da kasancewar wacce ban taso daga bangaren yankin ruwa ba wannan ma ya haifar da tashin hankali.
Tun bayan fitar da littafin, ki kun sami wani bayani daga wani a makusanta Amaechi ko kuma shi kansa tsohon ministan?
A’a ban samu ba
Shin kina damuwa cewa wasu mutane za su iya biyo bayanki bisa ga wasu abubuwan da kika ambata a cikin littafin?
Ba ni da wani jin tsoro a matsayina na mutum. Na ba da labarina kuma na karfafa kowa da kowa ya yi haka domin yana ba da damar yin lissafi da gaskiya. Ba ni da wata nadama, duk wanda bai yarda ba yana da damar rubuta nasa littafin. Labarina na abin da ya faru a zahiri zai bace idan ban rubuta tarihin ba.
Nada ki da gwamnatin Buhari ta yi ya jawo kakkausar suka daga wasu ‘yan Nijeriya da suka ji takaicin hakan, kamar yadda aka kungiyar ‘yan ‘Bring Back Our Girls Campaign’ ta yi suka kan shigarki gwamnatin da ta gaza ceto ‘yan matan da aka sace. Shin kin damu da wadannan suka?
A gaskiya ba wannan gwamnatin (Buhari) ba ce ya kamata ta ceto ‘yan matan Chibok. A zamanin (tsohon shugaban kasa Goodluck) Jonathan ne aka sace ‘yan matan. Don haka a zahiri gwamnatin Buhari ta kubutar da wasu ‘yan matan. Jama’a sun yi imanin cewa an ba ni tukuicin kamfen na Chibok a matsayin Manajan Darakta na NPA.
Kin ce gwamnatin Buhari ta ceto ‘yan matan, shin hakan na nuni da an kubutar da dukkan ‘yan matan?
A’a, amma dai ya ceci adadi mai yawa; sama da kashi 70 cikin 100 na ‘yan matan shugaba Buhari ne ya ceto su.
An ce gwamnati harka ce ta ci gaba, Shin kin damu cewa wasu suna jin kamar kina aiki da gwamnati?
A’a, bari ka ji gaskiyar lamari Gwamnatin da ta ke a lokacin da aka sace ‘yan matan agana gwamnatin da ta gaza wajen ganin an ceto ‘yan matan. Wannan gwamnatin ta ci gaba da agan har tsawon shekara guda kuma ba ta kubutar da agan. Wata sabuwar gwamnati ta shigo ofis kuma ta ci gaba da aikin ceto. Ya sami damar ceto sama da kashi 70 na ‘yan matan. A cikin ‘yan matan 276 da aka sace, wannan gwamnatin ta kubutar da sama da 100 daga cikinsu. Don haka, zai fi dacewa a ce an yi garkuwa da su a wata gwamnati da ta gabata daga baya aka samu wata sabuwar gwamnati ta ci gaba da ceto su, don haka gwamnati na ci gaba. Ba ni da wata matsala wajen yi wa gwamnatin da ta ci gaba da aikin ceto ‘yan matan Chibok.
Duk da alkawuran da gwamnatin Buhari ta yi, ta kasa ceto sauran ‘yan matan. Yayin da ‘yan makonni ya rage wa gwamnatin ta kare, shin an yi rashin adalci idan aka ce shugaban kasa ya kasa cika alkawarin da ya agan ceto su?
Ba zan ce ya gaza ba domin kamar yadda na ambata ya ceci sama da kashi 70 cikin 100 na ‘yan matan kuma an agan kulawa. Don haka ana kokari. Cewa kokarin bai sa an kwato ‘yan matan gaba daya b aba shi ne yake agana a yi komai ba, an yi duk abin da ya kamata a yi. Don haka Buhari ya karbi agan bayan an dade da yin garkuwa da ‘yan matan. Ba za a yi adalci agana aka ce shugaban kasa ya kasa cika alkawarin da ya agan ceto su.
Mece ce alakarki da sauran manyan mambobin kungiyar BBOG, kamar Aisha Yesufu, yanzu?
Ina da kyakkyawar dangantaka da su. Ina yin kuma mata agana da (Yesufu).
Ta kasance mai tsananin sukar gwamnatin Buhari, ta nuna farin cikinta da kuka yi wa gwamnatin aiki?
Babu wani zabi na wani ya yi murna ko kada ya yi, abin dana zabawa kania nane, a gasikiya wannan ba abu ne mai muhimmanci ba. Aisha Yesufu ta shoio kungiyar BBOG. Ba ita ta kaddamar da kungiyar ba, tana dai zuwa a yi zanga-zanga da ita ne, tabbas muna gaisawa da Aisha muna wasa da dariya a astakaninmu, na ciga da halartar taron zaman dirshan na BBOG da ake yi a ‘Falomo Roundabout’ a duk mako a lokacin.