Babban jami’in gudanarwa na Tesla, Elon Musk, ya sanar da cewa ‘Neuralink’, kamfaninsa na farko na kula da kwakwalwa ‘brain-chip’ ta samu sahalewa daga hukumar kula da ingancin kayan abinci da magunguna ta kasar Amurka domin gudanar da aikin dashe ga wadanda suka fito duniya ba tare da idanuwarsu guda biyu na amfani ba ko da kuwa dashen jijiyoyi ne ta yadda za su dawo ganinsu radau.
“Na’urar gyara na maido da mutum ganinsa daga makanta daga kamfanin Neuralink zai bayar da mafita ga wadanda suka rasa ganinsu gabaki daya da wadanda ba su taba gani ba a duniya. Zai dawo musu da ganinsu radau, kuma zai janyo wa mutanen da tun haihuwar ba su gani zuwa gani karin farko,” kamar yadda hamshakin attajiri a bangaren fasahar zamani ya wallafa a shafin Tiwita a ranar Laraba.
- Tsohuwa Ta Yi Barazanar Kai Ƙarar Wanda Ya Shirya Gasar Cin Taliya Da Jikanta Ya Lashe
- Tinubu Ga ‘Yan Kasa: Ina Sane Da Tsadar Rayuwar Da Kuke Ciki
Musk ya wallafa bayanin nasa tare da hoton Geordi La Forge, dan wasan kwaikwayo a talabijin na ‘sci-fi TB series Star Trek’, wanda ya kasance makaho tun daga haihuwa kuma aka yi amfani da wasu fasahohin wajen ba shi damar gani.
Ya ce, a matakin farko daidai gabar cimma burin da ake hako, za a hada na’urar ne kamar a zanen Atari, amma daga bisani za kai matakin cimma burin dawo wa mutane ganinsu radau kamar irinsu Geordi La Forge.
Shi dai Elon Musk ya kafa kamfanin nasa Neuralink a 2016 wanda ya kware sosai a bangaren kirkire-kirkiren kwakwalwar kwamfuta.
Fasahar Neuralink ta hada da dasa kwakwalwa wanda ke karantar siginar din jijiyoyi kuma yana watsa su zuwa na’urorin waje ba tare da waya ba, gami da kwamfutoci da na’urorin hannu.
Shafin kimiyya da fasaha ya nakalto cewa Neuralink kuma yana habaka dasawa wanda ke bai wa guragu damar sarrafa na’urorin fasaha da tunaninsu.
An kuma bayar da rahoton cewa Neuralink yana gudanar da gwaje-gwajen cutuka ba tare da mutum ya je ya zauna a gaban likita domin neman masa bayanin jinya ba, zai iya samun kulawar likita daga nesa ta hanyar fasahar.
A cikin Agusta 2024, an ba da rahoton ko’ina cewa Neuralink ya samu nasarar dasa kirar kwakwalwar kwamfuta a cikin majiyyaci na biyu, wanda a yanzu yana iya sarrafa wasannin bidiyo da kirkirar 3D ta amfani da tunaninsu kawai.