Dubban Kogon Buddha na Kezil suna cikin tsaunin Mingwutag dake gundumar Baicheng ta jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin. An fara tono jerin kogon Kezil ne daga karshen karni na 3 zuwa farkon karni na 4, wanda ya kai tsawon kilomita 3. Akwai jimillar kogo 251 da kuma zane-zanen bango masu murabba’in mita 10000 a ciki.
Rukunin kogon Kezil kamar maganadisu ne dake jawo hankalin Nuryan Maimaiti sosai, a matsayinta na darektar sashen karbar baki na cibiyar nazarin kogo na Kezil ta jihar Xinjiang, ta riga ta shafe shekaru 6 tana aikin binciken rukunin kogon, inda ta bar sawunta a duk wuraren da suke, don gano tarihin mu’amala da cudanya tsakanin kabilu daban-daban na jihar Xinjiang.
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
- Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya
Kuqa, wanda aka fi sani da Kucina, shi ne zango na farko a kan hanyar siliki lokacin da aka fara yada al’adun addinin Buddha zuwa kasar Sin. Lokacin da aka gabatar da addinin Buddha zuwa Kuqa, ya kuma kawo dimbin gine-ginen addini, da sassaka da zane-zane, wanda ya haifar da dimbin rukunonin koguna a yankin Kuqa. Daga cikin su, jerin kogon Kezil na iya wakiltar fasaha ta kogon Kucina, kuma su ne jerin kogon addinin Buddha da aka gada mafi dadewa, mafi girma, mafi yawan nau’o’i, kuma mafi tasiri a Yankunan Yamma, wato wurin da ake kira da gama gari ga jihar Xinjiang ta kasar Sin da tsakiyar Asiya.
A wannan lokaci, jihar Xinjiang tana da sanyi, kuma dusar kankara da yawa da kauri ta rufe tsaunin Mingwutag, jerin kogon Kezil suna a kan dutsen Mingwutag, kuma wata hanya mai lankwasa ce ta hada manya da kanana kogo tare.
A tunanin yawancin mutane, ba zai yiwu mutane su zabi bude ido a nan a lokacin sanyi mai tsanani kamar haka ba, amma a kasan tsaunin dusar kankara, akwai wasu mutane dake tafiya a kan hanyar zuwa jerin kogon, kuma wadda take tafiya a gaba don yin bayani ga sauran mutane, ita ce Nuryan.
Nuryan ta bayyana cewa, “Wannan ba abin mamaki ba ne, akwai masu yawon bude ido da yawa a lokacin rani, don haka ba zai yiwu a zauna a cikin kogo na dogon lokaci ba. Saboda haka, wasu masu sha’awar kogo da suke da kwarewa a fannin, suna zabar yin ziyarar a lokacin hunturu, wato lokacin da mutane kadan ne ke yawon shakatawa a nan, ta hakan za su iya yin cudanya sosai da jagororin.”
Nuryan ’yar Kuqa ce, a shekarar 2017, ta yi mu’amala da al’adun Kucina bisa radin kanta, kuma irin al’adun sun burge ta matuka. A daidai wannan lokacin, cibiyar nazarin jerin kogon Kezil ta jihar Xinjiang tana kokarin daukar ma’aikata domin yada al’adun Kucina. A matsayinta na ma’aikaciyar gwamnati a ofishin gwamnatin gundumar Kuqa, ta mika takardar neman aikin ba tare da bata lokaci ba.
Wata kawarta ba ta fahimci dalilinta na yin hakan ba, ta kuma tambaye ta, ko ya cancanci ta bar aikinta mai kyau, ta tafi cikin duwatsu don binciken kogo? Nuryan ta amsa cewa, idan mutane da yawa za su iya fahimtar tarihi da al’adun Xinjiang ta hanyar kokarin ta, a ganin ta, ya dace!
A shekarar 2018, Nuryan ta shiga cibiyar nazarin kogo ta Kezil, kuma ta fara koyon ilmin nazarin kayayyakin tarihi daga karce.
Nuryan ta ce, “Da farko, na san wadannan haruffa, amma haruffan ba su san ni ba.” Ta yi bayani kan wannan jimlar da ta fada cewa, wurin da kogon Kezil suke, shi ne mahaifar addinin Buddha na kasar Sin, tana iya furta wasu kalmomin Buddha, amma ba za ta iya fahimtar su ba.
Ban da wannan kuma, akwai zane-zanen bango iri-iri a cikin kogon. Haka kuma ana bukatar ta fahimci nau’ikan zane-zane, da abubuwan da suka shafa da ma tarihinsu. Ta nemo wasu litattafai irin na tarihi da addinin Buddha, kuma ta dukufa wajen karanta su.
Nuryan tana son koyon ilmi, kuma ta kware wajen neman dabarun karatu. A duk lokacin da ta yi nazari kan wani kogo, ta kan bi bayanan kwararru don gane shi a dukkan fannoni. Misali, lokacin da ake rubutu game da fadi da tsayin wani zanen bango, da abubuwan da ke cikin zanen, da kuma halin musamman na mutanen dake cikin zanen, ita da kanta ta tantance dukkan wadannan daga cikin bayyanai da abubuwan da ta gano a cikin wannan kogon.
Bisa tushen litattfai da bayyanai, da ma fahimtar da ta samu da kanta, tare kuma da takaitawa da aiki da ilimin da ta yi, ta samu sakamako mai kyau cikin sauri a fannin koyon ilimin kogo.
Kasar Sin tana da wadatar al’adun da suka shafi kogo, don zayyana bayanai daga sauran al’amura, Nuryan ba wai kawai ta koyi ilmi kan jerin Kezil ba, har ma da wasu shahararrun rukunonin kogo, ciki har da na Mogao dake Dunhuang, da Longmen, da dai sauran su.
A cewar Nuryan, “Wasu masu yawon bude ido da suka taba ziyartar sauran wasu kogo, su kan kwatanta su da kogon Kezil, idan ba mu da ilimi game da kogon dake sauran wasu wurare, ba za mu iya amsa tambayoyinsu yadda ya kamata ba.”
A duk lokacin da ta yi magana game da kogon Kezil, Nuryan ta kan yi magana ba tare da tsayawa ba: a lokacin da tsohuwar Kucina ta zama tashar kasuwanci da ta hada babban yankin Turai da Asiya da ma wata muhimmiyar tasha dake kan tsohuwar hanyar siliki ne aka kawo addinin Buddha zuwa kasar Sin.
Akwai ruwan ma’adinai mai launin shudi a jikin bangon kogon, wanda ya fito daga makwabciyar kasar Sin Afghanistan, wanda ke tabbatar da cewa, Kucina cibiyar cinikayyar waje ce ta tsohuwar kasar Sin. Zane-zanen bango da aka zana game da yadda wasu ’yan mata ke yin kade-kade a cikin kogo mai lamba 38, sun nuna dimbin kayan kida daga tsohuwar kasar Girka, da tsohuwar Indiya, da kuma filayen tsakiyar kasar Sin, lamarin da ke nuni da haduwar al’adun kasar Sin da na yammacin duniya da aka taba yi a wurin. Kogo mai lamba 27, kogo ne mai yawan alkukai, wanda kuma ke da salon musamman na tsakiyar kasar Sin, ta haka aka gano cewa, addinin Buddha wanda aka gabatar da shi zuwa tsakiyar kasar Sin, ya habaka kuma ya sauya halinsa, bayan ya hada da al’adun yankin, sannan ya sake komawa Kucina…
Irin wadannan mu’amalar al’adu da musayar cinikayya ne ke sa kaimi ga cudanya tsakanin kabilu daban daban, wanda ya kai ga jihar Xinjiang, inda dukkanin kabilu ke rayuwa tare da samun ci gaba yadda ya kamata a yau.
Don haka, a duk lokacin da ta yi bayani, Nuryan ba ta mantawa da gaya wa masu yawon shakatawa cewa, Xinjiang wani yanki ne na kasar Sin, kuma bai taba rabuwa da kasar ba a tarihi.
A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke rangadin aiki a jihar Xinjiang, ya nuna cewa, an kafa tarihin Xinjiang ta hanyar yin mu’amala, al’ummar kasar Sin al’umma ce mai yawan jama’a da hadin kai, kuma kyawawan al’adun kabilu daban daban sun hade zuwa al’adun kasar Sin.
Nuryan ta amince da haka sosai. A ganinta, amincewa da al’adun kabilu daban daban na da muhimmiyar ma’ana, ta kuma kara fahimtar nauyin da ke kanta a matsayin mai yada al’adu. A idanunta, kayan tarihi masu dadadden tarihi suna da rai, wadancan jerin kogo da ke kan tsaunin duwatsu da zane-zanen bango dake cikin kogon, tamkar wani dattijo ne wanda ya sha fama da jujjuyawar rayuwa, kuma a hankali yana ba da labarin tarihi da zamani.
Aikin ba da kariya, shi ne tushen nazarin kayan tarihi. Bayan fiye da shekaru 1,700, jerin kogon Kezil sun riga sun kasance masu rauni sosai. A lokacin rani, akwai masu yawon bude ido da yawa, iskar carbon dioxide da mutane ke fitarwa na iya haifar da yanayin zafi a kogon, kuma ba za a iya shigar da na’urar sanyaya wuri cikin koguna ba, saboda busa iska mai sanyi kai tsaye zai illata zane-zanen jikin bangwayen.
Baya ga haka kuma, jihar Xinjiang tana da bambancin yanayin zafi tsakanin dare da rana, raguwar yanayin zafi zai kasance tare da hauhawar danshi, wanda kuma ba shi da kyau ga kare zane-zanen bango. Sabili da haka, wajibi ne a yi la’akari da daidaita yanayin zafi da na danshi a cikin kogon, da samar da iska mai dacewa, da kuma rufe kofofi a kan lokaci.
Nuryan tana da hakuri da kwazo wajen yin wadannan ayyuka na karshe a ko wace rana, sau da yawa ta kan hau dutsen bayan mutane sun sauko, ta kan yi sintirin kimamin sa’o’i 2 kafin ta kammala duba dukkanin kogon.
Hasali ma, rayuwar Nuryan tana da yalwa sosai, baya ga aikin nazarin kogo, tana kuma da wani matsayi na daban, wato ita ce ta kaddamar da wata kungiyar sa kai mai suna “Mu Iyali Daya ne”. Mambobin kungiyar sun fito daga kabilu daban daban, kuma suna kasancewa iyali daya mai jituwa.
Da zarar lokacin sanyi ya zo, kungiyoyin jin kai a biranen Beijing da Shenzhen da sauran wuraren kasar Sin, suna aikewa da tufafin hunturu. Nuryan da abokan aikinta su kan ware su tare da kai su ga yara mabukata a yankin, kafin dusar kankara ta rufe tsaunuka.
Nuryan marainiya ce, amma ba ta rasa iyali ba. Iyaye daga kabilar Han sun dauke ta, kuma sun rene ta tun tana karama, kana kuma tana da ’yan uwa daga kabilar Han guda biyu. Mahaifiyarta ta rasu ne sakamakon rashin lafiya yayin da take kan hanyar neman magani, kuma iyayenta na yanzu ne suka taimaka, suka kai mahaifiyarta gida.
Irin tarihinta na musamman, yana sanya ta sha’awar samun soyayya da kuma son ba da soyayya.
A shekarar 2014, Nuryan ta kaddamar da kungiyar sa kai ta “Mu Iyali Daya Ne”. A lokacin, tana aiki ne da rana, kuma tana shirya ayyukan sa kai da daddare, ciki har da jajantawa masu bukata, da ba da gudummawa, da talla da dai sauransu, kuma tana shagaltuwa sosai.
Shekaru goma sun shude a cikin kiftawar ido, har yanzu kungiyar “Mu Iyali Daya Ne” tana nan tana aiki, kuma ta kasance a sahun gaba a ayyukan sa kai, akwai wadanda suka taba tambayar Nuryan, dalilin da ya sa ake kiran kungiyar ta da “Mu Iyali Daya Ne”, inda ta amsa da cewa, “Dukkan kabilun jihar Xinjiang suna hada kai don neman wadata tare. Don haka asalinsu iyali daya ne!”