A shekara ta 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar kofin duniya bayan ta samu kuri’u 22 na shugabannin FIFA kuma ta yi nasara ne a kan Amurka, da Koriya ta Kudu, da Japan, da kuma Australia, wadanda su ma suka nemi karbar bakuncin gasar kuma ita de kasar Larabawa ta farko da ta dauki bakuncin gasar.
An zargi Katar da laifin bai wa jami’an FIFA cin hancin kuci Dala miliyan 3 domin samun goyon bayansu, sai dai an wanke ta bayan wani bincike da aka gudanar na shekara biyu sannan shugaban FIFA na wandan lokaci Sepp Blatter ya nuna goyon bayansa ga Katar a wandan lokacin.
- Shugabannin Sin Da Congo (Kinshasa) Sun Aike Wa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 50 Da Dora Huldar Kasashen Biyu Kan Hanyar Da Ta Dace
- Sai Mun Kawo Kuri’un Kano Ko Da Lalama Ko Da Tsiya – Shugaban APC
Gasar cin kofin duniya dai ana gudanar da ita ne duk bayan shekara hudu, sai dai ana bayyana kasar da za ta karbi bakuncin gasar shekara 12 kafin buga gasar domin ba wa kasar dammar shiryawa yadda yakamata. Katar, wadda ke da yawan mutum miliyan 2.9, na daga cikin kasashe mafiya arziki a duniya, sannan cinbin arzikin kasar shi ne man fetur da gas wanda da shi kasar ta dogara wajen samun kudade.
Kasar ta gina sababbin filayen wasa guda bakwai domin wannan gasa sannan an gina sababbin otal-otal 100 da sabuwar hanyar dogo da kuma hanyoyi, sannan a matsayin ta ta kasa mai bin tsari na Adcinin Musulunci, an hana shan giya.
Nawa katar ta kashe wajen shirya gasar?
Kamar yadda Ministan Wasannin kasar ya bayyana, Katar ta kashe Dala miliyan 500 duk sati wajen gina muhimman abubuwan da ake bukata na gasar cin kofin duniya da take karbar bakunci a yanzu haka.
Ministan Kuci na Kasar, Ali al-Emaci ya de suna ci gaba da kashe wannan kucin duk mako, har tsawon shekara 3 zuwa 4, wajen gina sabbin filayen wasa, da tituna da layin-dogo da asibitoci da sauransu.
Kasar mai arzikin iskar gas ta kashe sama da Dala biliyan 2200 a aikin gaba daya sai dai Ministan ya musanta maganar cewa gasar cin kofin duniyar ta shekarar 2022 tafi kowadde a tarihi cin kuci.
Gasar cin kofin duniya ta 2014 da aka yi a Brazil kamar yadda aka de ta lashe Dala biliyan 11, yayin da Rasha kuma ta kara yawan kudaden da za ta kashe domin shirya wa gasar kofin duniya na 2018 daga Dala miliyan 321 zuwa biliyan 10.7.
Ministan kucin na Katar, ya shaida wa manema labarai a birnin Doha cewa tun da farko, sai da suka biya kashi 90 cikin 100 na kwangilar ayyukan, kuma an kammala kashi biyu bisa uku, na aikin cikin watanni 24. Katar ta tilasata wa kamfanonin da suke aiki akan su dauko ma’aikata ‘yan kasashen waje, galibi daga kasashen kudancin Asia, wadanda kungiyoyin kare hakkin dan’Adam suka de ana ci da guminsu, tare da sa su aiki a yanayi mai hadarin gaske.
Gwamnatin Katar cin dai ta sha musanta wannan zargi, kuma a watan Cisamba na shekarar da ta gabata ta yi wasu sauy-sauye na kyautata ‘yancin ma’aikata ‘yan kasashen waje wadanda suka yi aiki a wuraren gine-gine.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Gianni Infantino, ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su tsagaita bude wuta na wata guda saboda gasar cin kofin duniya da zai gudana a Katar. Infantino ya shaida wa shugabannin a taron kolin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a Indonesia cewa gasar cin kofin duniya na samar da wani “tsari na musamman” kan zaman lafiya da hacin kai domin mutum kimanin biliyan biyar ne za su kalli gasar ta talabijin.
Dagewar katar akan dokokinta
Da yawa daga cikin kasashe da kungiyoyi ba su san da dokokin da kasar Katar take da su ba musamman wadanda suka shafi dokokin kasar da sauran dokokin da ake ta ka de-na de da su tun a shekarar da ta gabata. Tawagar kasashen Argentina da ta Uruguay da suka tafi gasar kofin duniya sun yi dakon tarin nama mai yawa zuwa Katar domin su rika tuna wa da dandanon abincin kasashensu a lokacin gasar.
Sai dai tun farko ‘yan kasar Katar sun so hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta sauya shawarar da ta yanke ta barin a sayar da barasa a dukkanin filayen wasannin da za a yi gasar kofin duniya. Sai dai bayan da ya rage saura kwana biyu a fara gasar hukumar kwallon kafa ta duniya ta tabbatar da cewa ba za’a sayar da giya ba a filayen wasa takwas da za a gudanar da gasar, a cewar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Da farko dai an aminde a sayar da giyar ga ‘yan kallo a wasu lokuta na filayen wasannin, duk da cewa an haramta sayar da ita a fili a kasar da ke bin tsarin adcinin Musulunci wanda hakan yake nufin mutanen da ke cikin ofisoshi ko wuraren kasuwanci ne kadai za su iya samun damar sayen barasar.
Ban da shan giya, hukumomin kasar ta Katar sun hana made da made kama dakin Otel guda daya, sun hana na miji da namiji kama daki guda daya, sannan kuma sun hana made da na miji kama daki guda daya wanda hakan yake nufin dole ne sai dai kowa ya kama daki guda daya.
Sannan FIFA ta yi watsi da bukatar kasar Denmark na neman izini ga ‘yan wasan ta su sanya rigar da suke atisaye da ita da rubutun ‘yancin dan’Adam a gasar kuma FIFA ta haramta wa kasashe sanya duk wani sako mai tattare da manufar siyasa tare da neman ‘yan kwallon su mayar da hankali kan kwallon kafa.
Katar tasha suka kan matsayarta game da auren jinsi da ‘yancin dan’Adam da kuma yadda take tafiyar da lamuran ‘yan cirani kuma da farko Denmark ta de za ta sanya rigar da ba ta da wata kwalliya domin nuna kin aminde wa da mai masaukin baki Katar.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA de ke kula da duk wasu abubuwa da kasashe ke amfani da su ciki har da kayan sawa, wanda suke cewa kada su zama masu manufar siyasa a cikinsu ko adcini ko wani kirari.
Matsayar Qatar kan hakkin ‘yan Luwadi?
Luwaci da macigo haramun ne a Katar kasancewar abubuwa ne da shari’ar Musulunci ba ta aminde da su ba kuma ana yanke wa wadanda aka kama da wadannan laifuka hukuncin dauri na shekara bakwai ko kuma na kisa.
Masu shirya gasar cin kofin duniya da Katar take karbar bakunci sun de ‘ana maraba da kowa’ domin kallon wasannin da za a buga, kuma ba za a ci zarafin kowa ba sai dai, shugaban shirya karbar bakuncin na Katar, Nasser al Khater ya de gwamnatin kasar ba za ta sauya dokokinta da suka shafi auren jinsi guda ba kuma ya bukaci wadanda za su je kasarsu martaba al’adun al’ummar kasar.
Ya kara da cewa ayyukan badala a bainar jama’a, tsakanin mutane masu jinsi guda ko ma wadanda ba jinsi guda ba lamari ne da ba za a lamunta ba saboda haka dole ne kowa sai ya bi dokar kasar idan ya shiga.
Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Human Rights Watdh ta fitar da wani rahoto inda ta de jami’an tsaron Katar na kama ‘yan luwaci, da macigo, da masu sauya jinsinsu a kasar, inda a wasu lokuta ake tursasa masu daukan darussan sauya hali sai dai Katar ta de akwai zarge-zarge na karya a cikin rahoton.
Katar ta fuskanci adawa mai zafi
Tawagar kwallon kafa ta katar ta wallafa wani biciyo tana neman Katar ta yi watsi da dokokinta na alakar soyayya ta masu jinsi guda kuma a cikin biciyon, ‘yan kwallon sun soki masu daukar ma’aikata na Katar kan zargin takura wa baki ma’aikata kimanin dubu 30,000 wadanda suke aikin gina filayen da za’a buga wasannin na gasar kofin duniya. Ana zargin cewa ma’aikata da dama ne suka rasa rayukansu sanaciyyar rashin daukar matakan kare lafiyar ma’aikata a wuraren gina filayen wasanni matakin da Katar cin tasha musantawa a gwamnatan de.
Kyaftin cin kungiyar kwallon kafa ta Ingila Harry Kane da na wasu kasashe tara na nahiyar Turai, da farko sun yi alkawarin sanya kyallen ‘One Lobe’ a damtsensu domin nuna adawa da dokokin auren jinsi guda na Katar.
Sannan birnin Paris na kasar Faransa da wasu biranen kasar Faransa ba za su haska wasannin gasar a allunan nuna wasa ba, duk da cewa Faransa de ta lashe gasar da ta gabata a shekara ta 2018 a Rasha.
A shekara ta 2010 ne Katar ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar kofin duniya bayan ta samu kuri’u 22 na shugabannin FIFA kuma ta yi nasara ne a kan Amurka, da Koriya ta Kudu, da Japan, da kuma Australia, wadanda su ma suka nemi karbar bakuncin gasar kuma ita de kasar Larabawa ta farko da ta dauki bakuncin gasar.
An zargi Katar da laifin bai wa jami’an FIFA cin hancin kuci Dala miliyan 3 domin samun goyon bayansu, sai dai an wanke ta bayan wani bincike da aka gudanar na shekara biyu sannan shugaban FIFA na wandan lokaci Sepp Blatter ya nuna goyon bayansa ga Katar a wandan lokacin, amma yanzu ya de da alama FIFA cin ta tafka kuskure a wata hira da ya yi da manema labarai a Switzerland.
Shin Katar ta ciri tuta?
Za’a iya cewa Katar ta ciri tuta wajen da gewa akan dokokin da take da su a matsayin ta na kasa mai cikakken iko da kuma nuna wa duniya cewa dokokin kasar ta ababen mutunta wa ne da girmama wa.
Yadda ta tsara gasar da irin bikin da akayi a ranar da aka bude shine ya tabbatar da cewa shugabannin kasar sunyi abinda yakamata wajen nuna wa duniya cewa suna mutunta kasarsu da dokokinta fiye da komai kuma ba za su sauka daga tsarin yadda dokar su take ba a kan wani dalili wanda bai wude kwanaki 30 ba.
Katar ta ciri tuta wajen nuna wa duniya cewa yadda take ganin girman dokokin wata kasar haka itama dole a girmama nata idan aka shigo saboda kowadde kasa tana da nata tsarin wanda take girmama wa musamman abubuwan da suka shafi adcini da al’ada da kuma tsarin shugabanci kama daga siyasa da sarautar gargajiya da sauransu.