Makonni biyu bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya raka ɗalibai masu tafiya karatu ƙasashen waje har zuwa cikin jirgi, gwamnan, ya sake komawa filin Jirgin Malam Aminu Kano domin rakiya ga tagwayen da aka haifa manne da juna zuwa kasar Saudiyya domin tiyatar raba su.
Tuni dai, tagwayen suka isa Saudiyya, inda al’umma da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan bajintar da gwamnan ya nuna na ganin an raba tagwayen da ke manne da juna a kasar ta Saudiyya.
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
- Bikin Al’adu Na Inganta Mu’amalar Al’adun Sin Da Najeriya
Kwana ɗaya kafin rakiyar tagwayen a filin jirgin saman, Gwamna Abba ya raba wa wasu majinyata kuɗaɗen da likitoci suka nema kafin a kula da lafiyarsu.
Gwamna Abba ya yaba wa gwamnatin Saudiyya kan ɗaukar nauyin yin tiyatar raba tagwayen da aka haifa manne da juna a jihar.
A yayin rakiyar, gwaman ya gode wa Sarki Salman na Saudiyya kan wannan ƙoƙarin, tare da addu’ar Allah Ya saka masa da alkairi.
Gwamnan ya tuno da yadda ba a daɗe ba, wasu likitocin ƙasar Saudiyyar suka yi wa masu fama da ciwon zuciya da idanu tiyata kyauta a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke jihar.
A nasa jawabin, babban jami’in Ƙaramin Ofishin Jakadancin Saudiyya a Kano, Shiekh Khalil Al’adamawi, ya bayyana cewa, irin wannan shiri yana nuna ƙoƙarin da Saudiyya ke yi wajen kyautata jinkan al’umma da kuma sadaukarwa ga mabuƙata.
Da yake godiya, mahaifin tagwayen, Isa Hassan, ya gode wa Sarki Salman bin Abdul’aziz na Saudiyya ya kuma jinjina wa Gwamna Yusuf kan jajircewarsa har aka samu nasarar tafiya zuwa kasar Saudiyya domin yin tiyatar.