Kamar kowane mako shafin TASKIRA ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamatakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi ilimi, inda shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ta wacce hanya rashin ilimi yake cutar da al’umma bakidaya?, wacce hanya ya kamata a bi wajen kara habaka hanyar samun ilimi?, ko ta wacce hanya kimiya da fasaha ke taka rawa wajen samar da ilimi?, fadi amfanin ilimi”. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Naja’atu Baffa Jihar Kaduna:
Rashin Ilimi na cutar da al’umma ta hanyoyi da dama kamar; hana samun kwakkwaran aiki na dogaro da kai da kuma aikin samun kudi, idan da babu ilimi da mutane na ta gwagwarmaya me wahala. Hanyoyin habaka ilimi su ne; samun kimiyya da fasaha mai kyau, sannan a sako iyaye cikin al’amuran da suka shafi ilimin. Kimiya da fasaha na taka rawa sosai a wajen ilimi kamar yanar gizo-gizo a yanzu na taimakawa dalibai dsn samun saukin karatu ba tare da sun sha wata wahala ba, sannan yana taimakawa malamai wajen tsara aikin su na tsare-tsaren makaranta cikin sauki, yana kuma taimakawa wajen sadarwa tsakanin malamai, dalibai da ma iyaye bakidaya ta hanya mai sauki. Ilimi yana da amfanoni da yawa kamar; ilimi na kara zurfin tunani a gurin dan’adam musamman wajen warware matsaloli, sai kuma hanyar samun kudi ne cikin sauki, ilimi na taimakawa wajen samun ilimi don a matsayinka na mutum mai zurfin tunani zai iya yu wa kasan illolin wadansu abincincika da suke da hatsari ga dan’adam, ilimi ka iya raya al’adar mutane har ma da karbar wadansu al’adun na mabambantan mutane. Shawarar da zan bawa iyayen da ba sa tura ‘ya’yansu makaranta ita ce; ta hanyar tura yara makaranta hakan zai ba su damar cikar burikansu, kiwon lafiyarsu har ma da iyayen, amfani da baiwar da Allah ya basu, sannan yaran da ba a tura su makaranta ba sun fi fadawa tarkon talauci zuwa bin abokan banza na unguwa.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, Daga Jos A Jihar Filato:
Ilimi Gishirin Rayuwa
Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko da wanda ake koya a wajen aiki ne ko wajen sana’a, ba lallai sai a cikin aji ba. Ana koyon ilimi na aiki da hannu, ko da baki ko a rubuce. Sannan yanzu da zamani ya canza, akwai kafofin sadarwa daban-daban da mutum zai iya samun ilimi ba tare da ya shiga aji ba. Akwai manhajoji irin su YouTube, LinkedIn, Facebook da sauransu da mutum zai iya shiga ya koyi abubuwa da dama na ilimi. Lallai yana da kyau iyaye su rika zaunar da yaran su suna koya musu karatu da ilimin rayuwa, tun daga matakin gida, ko a dauki nauyin mai koya musu, ko kuma a saka su a makaranta. Rashin sa yaro a makaranta na sa ya girma babu wayo, kuma zai rika rayuwar jahilci, da rashin sanin inda yake masa ciwo. Sannan gwamnati ta saukaka hanyoyin samun ilimi, a rika koyarwa da harshen uwa a matakin farko, a samar da ilimi kyau, a rika ba da tallafin karatu ga manya.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hanyoyin da rashin ilimi ke cutar da al’umma suna da yawa domin shi ilimi jigo ne na rayuwar dan’adam muddun kuwa aka ce babu shi to dole abubuwa da dama ba za su tafi daidai ba, domin shi ilimi dan jagora ne ga duk kanin dan’adam shi ke haskawa mutum hanyar daya kamata ya bi da wacce ya kamata ya kaucewa don matsalolin da rashin ilimi ke haifarwa sun fi gaban kidayawa ko kirdado. To magana ta gaskiya a wannan fannin gwamnati ya kamata ta tashi tsaye wajen inganta fannin ilimin dama samar da shi kyauta ga duk kanin al’ummar kasa, sai kuma iyaye suma su tashi tsaye wajen kulawa da sa ‘ya’yansu a makaranta da kuma kula da zuwan yaran akan lokaci. To magana ta gaskiya kimiyya da fasaha tana bada gagarumar gudunmawa wajen saukaka samun ilimi a wannan zamani da muke ciki shi ya sa za ka ga dukkanin kasashen da suka cigaba ta fannin ilimin kimiyya da fasaha to sun fi samun cigaba a fannin ilimi. To amfanin ilimi ko muhimmancin ilimi ga rayuwar dan’adam ya fi gaban kidayawa ko kirdado domin sai da ilimi ne rayuwar take yin kyau kuma sai da ilimi ne ake samun cigaba a rayuwa. To hakika ya kamata irin wannan iyaye su sake tunani domin fa ilimi shi ne hasken rayuwa wanda duk ya rasa ilimi to ya rasa komai a rayuwarsa don haka ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ilimin ‘ya’yansu.
Sunana Fatima Nura Kila A Jihar Jigawa:
Rashin ilimi na haifar da matsaloli musamman a cikin al’umma kamar su sata, fyade, rashin girmama manya duk wadannan rashin ilimi na kawo su. Hanyar daya kamata abi shi ne; Gwamnati ta zage damtse wajen tura yara makarantu da kuma saukaka karatu tun daga matakin firamare, har gaba da sakandare. Ilimin kimiyyya nada matukar amfani ga al’umma ta fuskar tabbatar da sauye-sauye tare da samar da cigaban rayuwa, musamman abin da ya shafi bunkasa tunanin dan’adam wannnan ba karamar taka muhimmiyar rawa yake ba. Ilimi jigo ne sannnan mahadin rayuwa ne, ilimi na da amfani musamman wajen zamantakewa da kuma kasuwancinmu na yau da kullum. Shawarar da zan basu shi ne su bar ‘ya’yansu su je makaranta domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa, mutum mai ilimi ma ya fita daban a cikin al’umma.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:

Hanyoyin suna da yawa amma daya daga ciki ita ce; aikata ibada ba daidai ba da sabawa Allah kai tsaye. Samar da ilmi ta internet duk da mafiya yawan wasu mutanen tuni sun yi nisa ta wannan fannin. Wajen kirkirar wasu abubuwan da bamu saba ganinsu ba a yankunanmu. Daya daga cikin amfani Ilmi shi ne; aiki da shi a dukkan al’amuranka. Shawarata a garesu ita ce gaskiya su canja tunani kada iyaye su ga wai yanzu idan ka yi karatu ba a samun aikin yi a’a shi ilmi koda irin ‘yan iskan gari ne za ka ga sun bambanta da wadanda ba su yi ba, a saka yara su yi Ilmi ko wanne iri ne domin a can gaba za a ga amfaninsa. Allah ya sa mudace.
Sunana Aisha T Bello Jihar Kaduna:
Rashin ilimi cuta ce gaskiya, saboda ilimi shi ne kishin zaman duniya, yanzu misali; gida babu miji ya rasu in mata na da ilimi za ta nemi aiki dan ta kula da yaranta. Saboda yanzu duniya da zaran ba maigida ba masu kulawa da marayu Allah ne gatansu. Kimiya da fasaha na taka rawa sosai wajen kawo, cigaba ga al’umma bakidaya. Ga iyayen da basu tura yara makaranta gaskiya babbar cutarwa ce, domin kuwa yanzu duniya ta ci gaba, yanzu idan baka da ilimi kana ji kana gani ka zama dan kallo, don haka iyaye su daure su tura yara makaranta don cigaban al’umma bakidaya. Allah ya amfanar damu baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp