Da misalin karfe biyar na asuba ne a sansanin ‘yan gudun hijira, A’isha ‘yar shekara shida ta farka daga barci a cikin tanti da ke da facin buhunan leda da ya yage da kuma sandunan itace marasa fasali madaidaici. Tana tare da iyayenta da ‘yan’uwanta su shida, babu katifa; sai wata tabarma da aka shimfida a kasa cikin yashi. Akwai zafi, amma sanyin subahi ya kawo dan sauki.
Mahaifiyar A’isha, Fatima; na tara kayayyakin kwanuka don samar da abin kalacin safe, amma babu abin da za a dafa, sai garin masara da bai kai loma daya ba; kuma babu sigan da za a zuba a ciki, wadda wata kungiya mai zaman kanta ta samar a kwanakin baya. Wannan ne iyalin mai kunshe da mutane tara za su raba a tsakaninsu. Wanka da safe a nan abin fata ne.
- Rashin Kayan Aiki Kan Sa Muna Kallon Majinyaci Zai Mutu Mu Kasa Taimakon Sa – Dakta Musubahu
- Zulum Ya Gabatar Da Ƙarin Kasafin Kuɗi Naira Biliyan 61 Ga Majalisar Borno
Bayan sun gama karyawa, A’isha ba ta zuwa makaranta; duk da ikirarin da gwamnati ke yi na samar da ilimi a sansanonin ‘yan gudun hijira. Maganar gaskiya a nan ita ce, yara da dama na sansanonin ba sa zuwa makaranta; sannan kayan aiki ba su da yawa, ajujuwa kuma idan akwai su, akwai cunkoso; babu kuma isassun kayan koyarwa.
Kamar sauran yaran sansanin, A’isha takan wuni tana wasa a cikin turbaya ko kuma taimaka wa mahaifiyarta da debo ruwa a rijiya ko tankin jama’a. Bugu da kari, ruwan ba shi da cikakken aminci; wanda ka iya haifar da barkewar cutar kwalara a-kai-a-kai.
La’asar ce a sansanin ‘yan gudun hijira, ga Fatima na cike da kokarin kula da ‘ya’yanta tare da damuwa game da makomarsu a nan gaba. Wannan sansani da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, ba shi da kayayyakin kiwon lafiya. Fatima na da ciki wata shida, amma ba ta da damar samun kulawar unguwar zoma kafin haihuwa; ga rashin abinci mai gina jiki ya yi kamari a tsakanin mata da yara a wannan sansani, haka zalika; Fatima ta damu da lafiyar jaririn da take dauke da shi. Wannan ne yasa take fata tare da yin kira ga kungiyoyin jin kai da su kawo karin kayan abinci nan ba da jimawa ba, amma agajin nasu na lokaci zuwa lokaci ne; wanda ba za a iya tantance ko yaushe ne za su kawo ba.
Kamar sauran iyaye mata ne ‘yan gudun hijira, Fatima ba ta da wata hanya ta samun kudin shiga; ga shi kuma maigidanta shi ma na fama da zuwa neman aikin kwadago na yau da kullum a yankunan da ke kusa. Gonar iyalin, wacce suka gudu shekaru da dama da suka gabata, ita ce tushen rayuwarsu. Fatima na fatan wata rana ta koma kauyensu, su sake gina gidansu; sannan kuma ta samu damar tura ‘ya’yanta makaranta.
Magariba mai cike da firgitarwa ta sake dawowa a sansanin gudun hijirar, A’isha da ‘yan’uwanta suna shirin kwanciya kamar kowane dare mai cike da ban tsoro; saboda rashin wutar lantarki, rashin tsaro a sansanin ya yi karancin; Fatima kuma ta damu game da lafiyar iyalinta. Abubuwan da ke faruwa na cin zarafi da zalunci, sun zama ruwan dare; musamman ga mata da kuma ‘yan mata. Fatima da A’isha da sauran, suna kwance cikin duhu yayin da suke hira a tsakaninsu duk da damuwa da sauraron duk wani sabon sauti ko kara; yayin da suke jiran barci ya sace su, domin mantawa da matsalolin rayuwa.
‘Yan gudun hijirar na cikin gida (IDPs) Nijeriya, na wakiltar daya daga cikin al’ummomin da suka fi fama da rauni da kuma rashin kulawa. Rikici, tashin hankali, bala’o’i da sauran rikice-rikice; sun raba miliyoyin ‘yan Nijeriya da muhallinsu tare da lalata musu rayuwa da kuma jefa su cikin wahalhalu marasa misaltuwa. Ya zuwa shekarar 2024, akwai sama da mutane miliyan 3.2 da ke sansanin gudun hijira a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) a Nijeriya, wadanda akasari sun fi yawa a yankin Arewa Maso Gabashin wannan Kasa.
Wannan shi ne halin da kuma girman matsalar ‘yan gudun hijira a Nijeriya, matsalar jin kai na neman daukar matakin gaggawa daga gwamnatin Nijeriya, hukumomin bayar da agaji, kungiyoyi na cikin gida da na kasa da kasa, masu kishin kasa a ciki da wajen Nijeriya, ya zama wajibi su samar da yanayin da yadace na bai-daya, su kuma daidaita matakan da suka dace wajen magance matsalar, sannan kuma su samar da mafita ta dogon zango tare da dawo da martaba da dogaro da kai na wadannan ‘yan gudun hijira.
Kafin nan, amma wai su wane ne ‘yan gudun hijira (IDPs)? Mutane ne ko kungiyoyin jama’a wadanda aka tilastawa barin gidajensu da garuruwansu, saboda ta’addanci ko wani bala’i; amma suna cikin iyakokin kasarsu. Ba kamar masu yin kaura ba, (Refugees), wadanda suke ketare iyakokin kasa da kasa, suna karkashin kulawa da kariya daga gwamnatinsu. Abin bakin ciki a Nijeriya, yawancin wannan kariyar ba ta isa ba; ‘yan gudun hijira na da rauni, musamman saboda hijirar ta kan haifar da asarar gidaje, dukiyoyi, gonaki, hanyoyin samun kudi, lafiya, ilimi da sauran makamantansu. A sansanonin ‘yan gudun hijira ko al’ummomin da ke karbar bakuncinsu, na fuskantar cunkoso, rashin isasshiyar tsafta, karancin abinci da rashin isasshen ruwa mai tsafta da kuma kiwon lafiya. Yawancin ‘yan gudun hijirar, na rayuwa ne a cikin matsugunai na wucin gadi, wanda hakan ke jawo mummunar rayuwa mai alamar rashin tabbas, talauci da kuma tsoro.
Burin kowane dan gudun hijira (IDPs) mai sauki ne, kuma dan kadan. Suna fatan komawa gidajensu da garuruwansu tare da burin sake samun damar samun ilimi, kiwon lafiya da rayuwa mai inganci, suna kuma fatan sake gina rayuwarsu cikin mutunci da aminci. Ga mutane da dama, fatan komawa kauyukansu ko garuruwansu; na da dan nisa yayin da rashin tsaro ke ci gaba da yin kamari, suna kuma marmarin kasancewa cikin kwanciyar hankali da abin da suke da shi a da ko a baya.
Duk da wadannan burika masu sauki, ‘yan gudun hijirar na ci gaba da kasancewa cikin tarko, cikin wani yanayi na rashi tare da fuskantar shingen da ke hana su cimma burikansu. Komawa gidajensu, sau da yawa ba zai yiwu ba; sakamakon tashe-tashen hankula da ake ci gaba da samu, sannan kuma damar samun ilimi da kiwon lafiya na iyakance ta; ga kuma rashin isassun kayayyakin more rayuwa a sansanonin. Yawancin ‘yan gudun hijiran, sun dogara ne da taimako da tallafin jin kai na mutane tare da karancin damar dogaro da kai.
A halin yanzu, martanin gwamnatin Nijeriya game da matsalar ‘yan gudun hijira, bai isa ba, kazalika kuma bai daidaita ba. Sau da tari, ana yin watsi da ‘yan gudun hijira a cikin maganganun siyasa, kana kuma ana watsi da bukatunsu; don biyan wasu bukatun na siyasa da tattalin arziki. Yayin da wasu hukumomin gwamnati, kamar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Mutane Masu Kaura (NCFRMI) ta kasance, yunkurin nasu sun raunana domin cin hanci da rashawa, rashin ingantaccen tsari, aiwatarwa da kuma gazawar kasafin kudinsu na kowace shekara.
Haka kuma, ita Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), wajen kula da sansanonin ‘yan gudun hijira. Rahotanni sun nuna cewa, aikin nasu ba koyaushe yake haifar da abin da ake tsammani ba, musamman ta fuskar samar da isassun tallafi da kuma kayan agaji.
Wani abin ban takaici shi ne, rashin cikakken tsarin doka; don kare ‘yan gudun hijira wanda ke kara musu rauni. Ko da yake, Babi na II: Muhimman Manufofin Kasa da Ka’idojin Umarni na Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima; ya tabbatar da ‘yancin rayuwa, mutunci da ’yancin walwala, wanda ba a bai wa ’yan gudun hijirar nan ba. Har ila yau, babin ya umarci gwamnati a dukkan matakai da ta tabbatar da tsaro, jin dadin jama’a da walwalar dukkan ‘yan kasa a sashe na 14 (2) (b), sashe na 16 ya kuma jaddada tabbatar da adalci ga tattalin arziki, inda ya yi kira ga gwamnati da ta kula da albarkatun kasa yadda ya kamata tare da tabbatar da tsaro, cewa kowane dan kasa yana da damar samun daidaitattun damammaki; domin bunkasar tattalin arziki da ci gaba da kuma sashe na 17 wanda ke mayar da hankali kan adalci na zamantakewa, inda dole ne gwannati ta nuna daidaito, gaskiya da kuma hadin kai. Yana ba da tabbacin kariya daga wariya tare da jaddada bukatar gwamnati ta samar da tsaro, samar da ayyukan yi da bukatu na yau da kullun kamar ilimi da kiwon lafiya.
Kungiyoyin bayar da agaji, yayin da suke ba da taimakon da ake bukata; su ma ba su tsira daga zargi ba. Kokarin da suke yi, duk da cewa abin yabawa ne; wani lokaci ya kasa magance tushen matsalar gudun hijirar ko samar da mafita mai dorewa.
Tambaya: Shin menene musabbabin gudun hijira a cikin kasa? Wadannan sun hada da;
-Tashe-tashen hankula da rikice-rikice: Rikicin Boko Haram da ke ci gaba da faruwa tun shekarar 2009, ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallansu a yankin Arewa Maso Gabas. Jihar Borno kadai, na da sama da mutane miliyan 1.5 na wadannan ‘yan gudun hijira; yayin da munanan hare-haren da ‘yan Boko Haram da ISWAP suka kai kauyuka da makarantu da kasuwanni, na ci gaba da addabar yankin. Yankin Neja-Delta da aka fi sani da arzikin man fetur, shi ma ya sha fama da rikicin kabilanci. Haka nan, ayyukan tsageru da rikici tsakanin kamfanonin mai da al’ummomin yankin tare da tsoma bakin sojoji, sun yi kiyasin kimanin mutane 200,000 zuwa 300,000 da suka yi gudun hijira daga muhallansu tsawon shekaru.
-Rikicin Kabilanci Da Adini: Jos da ke Jihar Filato, ta sha fama da rikicin kabilanci da na addini tsakanin ’yan asalin yankin da kuma mazauna yankin, wanda ya jawo tashin hankali tun farkon shekarun 2000. Rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya ya raba sama da mutane 250,000 da muhallansu ya zuwa shekarar 2023. Haka kuma, a Jihar Taraba, shi ma rikicin kabilanci, musamman tsakanin kabilun Tibi da Jukun; ya yi sanadiyar raba mutane sama da 150,000 da matsugunansu, tun daga shekarar 2018.
– Fashi Da Garkuwa Da Mutane: Tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, ‘yan fashi da masu yin garkuwa da mutane, sun raba magidanta 500,000 a Kudancin Kaduna da sauran wasu yankuna da muhallinsu. An kori kauyuka, an lalata gonaki, an tilasta wa daukacin al’umma tserewa zuwa wuraren da suka fi tsaro ko sansanin ‘yan gudun hijira a cikin birnin Kaduna da garuruwan da ke kewaye.
A jihar Zamfara, musamman a yankunan karkara; sama da mutane 700,000 sun rasa matsugunansu tun daga shekarar 2019. Kungiyoyin da ke dauke da makamai, na kai hare-hare ba tare da wani hukunci ba, suna kai hare-hare a kauyuka tare da sace mutane; domin neman kudin fansa da kuma tilasta wa wasu da dama barin gidajensu. Kazalika, a Jihar Katsina; kimanin mutane 200,000 ne suka rasa muhallinsu, sakamakon sace-sacen mutane da hare-hare.
-Masifun Canjin Yanayi: Yin hijira sakamakon ambaliyar ruwa, ya ci gaba da zama dalili mai muhimmanci na yin gudun hijira a Nijeriya, sakamakon rashin kyawun tsarin birane, sare itatuwa da sauyin yanayi. A shekarar 2022, Jihar Kogi ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da ta raba mutane sama da 100,000 tare da nutsar da dubban gidaje, musamman a Lokoja da ke daura da mahadar kogin Neja da Benue. A kwanakin baya ne aka samu ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Maiduguri na Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar rugujewar madatsen ruwa da ya haifar da ambaliya mai yawa, lamarin da ya kara ta’azzara yanayin sansanonin ‘yan gudun hijira, inda aka lalata matsugunan wucin gadi. Wannan ya haifar da gudun hijirar mutane sama da 1,000,000 a sansanoni daban-daban da al’ummomin da suka karbi bakuncinsu.
– Tsarin Gwanati Mara Fasali: Yin hijira don gina hanyar da ke hanyar tekun Legas zuwa Kalaba, aikin da ke da tsawon kilomita 1,200, ya haifar da damuwa game da tasirinsa ga al’ummomin yankin da kuma muhalli. Kididdigar farko ta nuna cewa, kimanin mutane 20,000 zuwa 30,000 za su iya kauracewa muhallinsu sakamakon ginin, musamman yankunan da ke da yawan jama’a; inda hanyar za ta wuce kamar Jihohin Legas, Ribas, Akwa Ibom da kuma Kuros Riba.