Ina kara yi wa masu karatun wannan shafi barka da Jumma’a babbar rana, tare da yin kira ga uwargida da ta ci gaba da bayar da himma wajen ganin an ci gaba da jajircewa kan ayyukan gida da kula da yara.
A wannan makon ma mun leka tsohuwar ajiya a Taskar Aunty Jummai, inda muka zakulo muku sirrin kwai da ridi a jikin mace.
A kullum burin wannan shafi shi ne ya kawo wa mata tsaraba ta gyara da kula da jiki, tun daga kan kwalliya har zuwa inganta surar jikin mace.
Ina ganin babbar ribar da uwargida za ta samu ita ce kula da kai da na iyali baki daya da yara har da shi ma maigidan. Amma idan kika saki jikinki, ki ka murde ko kika cure a waje daya babu wani muhimmin aikin da za ki iya yi wa kanki ma, balle ki sauke wadancan nauyayan hakkokin da ke kanki.
Za mu yi magana a kan wasu abubuwa ne guda biyu wadanda a kullum muna amfani da su, amma galibi ba mu cika sanin amfaninsu a jikinmu ba.
Misali kwai, da dama ana ganin cewa babu abin da kwai ke kara wa mutum a jikinsa illa don jin dadi ne kawai, alhali kuwa ba haka abin yake ba. Kwai na taka muhimmiyar rawa wajen rage gurbataccen jini, kitse da rage duk wani nau’i na abin da mace ba ta bukata a jikinta, sannan ya rage kiba. Haka ma kuma Ridi. Shi ma yana da na sa amfanin a jikin mace.
Bari mu fara da na Ridin. Yawanci ba kowa ba ne ya san alfanunsa ba. Yawanci Hausawa ba su cika damuwa da shi ba, sai wasu kabilu dake makwabtaka da su.
Ridi daga darajarsa ya kamata mu fahimci lallai yana kunshe da amfani mai yawa ko ga zakkarsa idan muka duba. Ridi yana da amfani mai yawa a jikin mace da namiji.
Ga Mace yana mata matukar amfani ga mahaifarta, don yana wanke dattin mahaifa, da rikirkicewar al’ada.Yana kuma saka mace saurin daukar ciki, da samun lafiyar mahaifa da rigakafin kamuwa da ciwon dajin mahaifa da sauran wasu cututtukan da suka shafi mata. Yana saka jikin mace ya daina bushewa da taushin fata.
Idan za kiyi amfani da ridi wajen neman lafiya,to akalla ki yi kwana biyu kina aikinsa, kafin ki kai ga samun garinsa yadda ya kamata.
Da farko za ki gyara Ridinki ta hanyar wanke shi sai ki bar shi ya bushe, sannan a nika shi zuwa gari.
Za kiga ya dunkule saboda yana da mai, sai ki baza shi ya kara bushewa, sai ki zuba a turmi, harki samu ya warware. Sai ki rika diba kina sha a nono, ko ki ci shi haka nan. Amma ana so ki dan ba shi tsoro da wuta.