Masu iya magana na cewa, daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Sakamakon zaben da aka bayyana wanda dantakar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar lashe wa, zai yi matukar tasiri wajen zaben gwamnoni da ‘yan majalisa wanda za ayi nan gaba kadan.
Sau da yawa, wasu masu zabe a jihohi kan jira, su ga jam’iyyar da ta samu nasara a matakin shugaban kasa, su goya mata baya, domin samun su ga ba a bar su a baya ba.
Sakamakon zaben da aka bayyana na cewa, dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zabe, da kuri’a ma fi yawa tsakaninsa da abokan takararsa, wato Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP, sannan kuma akwai, dan takara jam’iyyar NNPP, wato Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Duk da irin talin matsin lambar da al’umma ke ciki, sun fito sosai wajen jefa kuri’arsu ga dan takarar da suke bukata, wannan ma ta sa kowane dan takara ya kwashi na sa rabon, wanda kuma hakan ta sa aka samu wanda ya fi samun rabo mai yawa, kuma aka bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe wannan zabe.
Wani abin sha’awa shi ne, yadda ba a samu wani rahoto da ke nuna tashin hanlai ba, bayan bayyana sakamakon zaben da aka yi. Yanzu haka dai kallo ya koma sama yayin da ake jiran nan da kwani kadan masu zuwa a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.
Saboda haka, ake fatan dukkan zabukan da za su biyo baya, su zama an yi su, ba tare da wata hatsaniya ba, wadda za iya haifar da matsaloli a cikin al’umma.
Zaben da za a yi na gwamnoni da na ‘yanmajalisa, zabe ne wanda yake kusa da jama’a fiye da zaben shugaban kasa, wanda aka yi. Saboda haka tun ganin yadda sakamakon wannan zaben na shugaban kasa,ya sa wasu gwamnonin cewa, dole su sauya taku.
Sai dai wani abu da aka luara da shi, wanda ya hana tasirin yin madudi a wannan zabe shi, matsalar kudi, wadda ta hana wasu ‘yansiyasa amfani da kudi wajen ganin an zabe su.
Ana ganin irin wannan matsalar ta rashin kudi, za ta yi tasiri sosai wajen ganin, ‘yan siyasa basu yi amfani da kudade ba wajen ganin an zabe su.
Zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi, zabe ne, wanda al’ummar kasar nan yanzu haka suke sauraron zuwansa nan da kwanaki kadan masu zuwa.