Sakamakon ambaliyar ruwar da ta auku a daminar bana, ana ci gaba da samun rahotannin yadda saran macizai a fadin kasar nan ke addabar jama’a sakamakon yawaitar fitowar dabbobi masu rarrafe daga ramukansu inda lamarin ya fi addabar jihohin Filato da Gombe.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, saran macizai na kara jefa al’ummomi da dama cikin fargaba da hatsari gami da tashin hankali.
- Xi Ya Jaddada Bukatar Inganta Farfado Da Yankunan Karkara
- Barazanar Kai Hari Abuja: Buhari Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Kwantar Da Hankalinsu
Lokuta daban-daban mutane na rasa yadda za su je cibiyar jinya domin neman makarin macizai a lokacin da suka gamu da saransu.
Sannan, maciji na iya tsitta yawu ga mutum wanda yawun nasa mai hatsari ne sosai ga mutane.
A bias yawaitar fitowa daga daji da macizai ke yi sakamakon yawan ruwan da ke addabarsu, jama’a kuma na shiga cikin hatsari sakamakon yaduwa da macizan da kuma yawaitar saransu da suke yi.
A ziyarar da wakilan kamfanin dillacin labarai suka kai zuwa cibiyoyin kula da saran macizai da kuma jinyar wadanda suka gamu da saran, sun gano cewa an samu karuwar ke sa ke san saran macizai sosai, yayin da aka samu karuwar mutuwar mutane a bias wannan saran a cibiyoyin jinya daban-daban.
Daga cikin wadanda saran macizai ya kashe har da matar sarkin Magama da ke kudancin karamar hukumar Langtang ta jihar Filato.
“Tabbas zan tabbatar maka cewa an samu karuwar saran macizai, daga cikin wadanda tsautsayin saran macizai ya shafa har da matar sarkin Magama.
“Lamari ne mai ban tsoro da firgici matuka. Macizai da dabbobi masu rarrafe su na guduwa ga ambaliyar ruwa kuma suna samun artabu a hanya sa’ilin da suke neman wurin fakewa,” a cewar Dakta Nandul Durfa.
Durfa, babban manajan gudanarwa na kamfanin Echitap, masu sarrafa da maganin kashe (makari) dafin saran Macizai, ya nuna takaicinsa kan yadda ake samun asarar rayuka sakamakon saran Macizai.
Tsohon Shugaban asibiti (CMD) na jami’ar koyarwa ta Abuja ya nuna damuwa da takaicin yadda ake samun karancin maganin kashe dafin saran Macizai a cibiyoyin jinya.
Sannan da yake magana, Dakta Abubakar Saidu Balla, jami’in Nazari da bincike na asibitin kula da makarin saran Macizai da ke Kaltungo a jihar Gombe, ya yi karin haske sosai kan lamarin tare da neman a dauki matakan shawo kan matsalar.
“Sabili da ambaliyar ruwa, gonakai da filaye sun jike sharkaf, sannan macizai na garzayawa zuwa manyan tudu domin neman mafaka inda suke haduwa da mutane.
“Wannan matsalar ta yi kamari sosai musamman yankunan kogunan da suke Borno, Adamawa, Kogi, Gombe da jihar Bauchi.
“Ambaliyar tana tilasta wa macizai kaura daga inda suke zuwa neman wani waje da har hakan kan kai su zuwa dazuka, gidajen mutane ko wuraren daruwa ke taruwa.
“Karin babbar matsala ma a nan shi ne, da dama daga cikin wadanda saran macizai ke shafa ba su iya zuwa asibitocin da ake kula da irin jinyar sakamakon lalacewar hanyoyin ko marashin kyan hanya da gadojin da za su fito da su daga yankunan da suke ko saran macijin ya same su. Kuma, ana samun hakan ne ko ta sanadiyyar ruwa ya yi awun gaba da gadoji da lalata hanyoyin.
“Kamar a yankunan karkara, an saba ceto irin wadannan mutanen ta amfani da mashina, amma mashinan ba su iya taimaka ma wasu sakamakon cewa tukin ma ba yiyuwa yake yi a cikin ruwa. A takaice, da dama daga cikin wadanda suke gamu da irin wannan lamarin nasarar maciji kafin a kai su cibiyar jinya sun mutu.”
Balla ya kara da cewa, yanzu zuwa gonakai na zama wa manoma da farga ma musamman a yankin Gombe.
LEADERSHIP Hausa ta nakalto cewa, Langtang wata karamar hukuma ce da ake yawan samun saran macizai.
Mazauna yankin a duk shekara sukan cire rai kawai saboda yawaitar saran macizai, kuma har zuwa yanzu suna zaman jiran tallafin gwamnati kan wannan lamarin.
Wata mazauniyar yankin, Naomi Bako, wacce ta misalta cewa kauyuka da dama a karamar hukumar suna fuskantar wannan matsalar ta saran macizai, “Muna da cibiyar kula da majinyatar saran macizai a Zamko. Babu wata shekara da za ta wuce da ba ka samu adadin kesa-kesan saran macizai sama da 1,500 ba. A wannan shekarar malamarin bai canza ba.
“Ko a satin da ta gabata, na ga mutum biyu da aka kai asibitin da suke fama da saran macizai.”
Kazalika, Shugaban kungiyar Mafarauta na karamar hukumar Josta Gabas, Atsen Daniel, ya ce jama’a ayankin na fama da matsalar yawaitar saran macizai, kuma hakan na zama abun fargaba ga al’umma.
Daniel ya ce, “Abun da zan iya cewa shi ne akwai kesa-kesan saran macizai a yankunanmu. Ban san adadin mutanen da lamarin ya shafa ba zuwa yanzu, amma a matsayina na shugaban mafarauta na san akwai rahoton wadanda saran ya shafa da yawa.”
Ya kara da cewa, sau tari a duk shekara a lokacin damina ana samun yawaitar saran macizai, kuma hakan bai rasa nasaba da ruwan da ke yawan yi da ke fitar da macizan daga dazuka zuwa neman mafaka.
Ya ce, “Macizai na yawan neman mafaka a damina, kuma da wuya garesu su samu wurin da bai jike ba su zauna domin gudanar da rayuwansu, sannan, a lokacin rani kuma sun fi son zama wurin da ke da sanyi. Mu ba tsoron macizai muke ba. Mun san cewa macizai na zama abu mai hatsari idan ya sari mutum.”
Sannan, wani Farfesa a fannin yanayi kasa, Farfesa Olaniran Olajire, da tsohon shugaban NIB, Sunday Wusu, sun nuna bukatar da ke akwai da cewa gwamnatoci a dukkanin matakai da su karfafi yawaitar dashen itatuwa domin dakile ambaliyar ruwa a nan gaba.
Suka ce, matsalar ambaliyar ruwa a sassan kasar nan na faruwa ne sakamakon canjin yanayi don haka suka nuna bukatar karfafa matan da suka dace na kariya daga wannan matsalar.
Ambaliyar ruwa wadda akalla ya jefa ‘yan Nijeriya miliyan 2.5 ciki har da yara miliyan 1.5 cikin hatsari a cewar rahoton asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF),wanda ya janyo mutuwar mutum sama da 600 da tilasta wa sama da miliyan 1.4 kaura daga muhallansu.
Da ya ke magana kan wannan lamarin, Olajire, ya shaida cewar dumamar yanayi na bukatar daukan matakan gaggawa, don haka ne ya nemi gwamnati da ta tashi tsaye wajen yin abubuwan da suka dace kan lamarin.
Wani rahoton da hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ta taba fitarwa ya nuni da cewa, kimanin mutum miliyan 5.4 ne dai maciji kan sara a duk shekaraa duniya, adadin wadanda kan rasa rayukansu kuma ya kama daga 81,000zuwa 130,000.
Akwai kuma mutane da dama da ke rasa gabbansu da kuma nakasa sanadiyyar saran macijizai. Nijeriya dai na daya daga cikin kasashen da macizai ke barna sosai.
Al’ummomi da dama a kasar dai na rayuwa ne kullum cikin fargaba saboda da matsalar saran majici, musamman yanzu lokaci damina zuwa kaka.
Manoma da kuma kananan yara ne matsalar ta fi shafa. Da dama daga cikinsu a kan kai su asibitin jinyar sarar maciji ne da ke garin Kaltungo, daya daga cikin cibiyoyi kalilan na musamman domin jinyar sarar maciji da ake da su a kasar nan.
Wata babbar matsalar dai ita ce yadda wadanda macijin kan sara ba sa samun magani yadda ya kamata.
Wasu lokuta dai magani kan kare karkaf a cibiyar ta Kaltungo, amma akullum marasa lafiya sai kwarara suke yi domin neman maganin.
Kuma masana na cewa samar da magani a kan kari da kuma kai duk wanda maciji ya sara asibiti da wuri za su taimaka matuka wajen rage yawan mace-macen.