• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare

byAbubakar Sulaiman
1 year ago
Fadar Kano

A wani gagarumin biki na tsakar dare, maimartaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shiga fadar mulkin Kano mai ɗimbin tarihi da karfe ɗayan daren yau Asabar.

Hakan ya biyo bayan mayar da shi a hukumance da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar Juma’a, bayan rusa masarautu guda biyar da tsohon gwamna yayi tare da maido da masarautar Kano kamar yadda take kafin shekarar 2019. Mataimakin gwamnan jihar da jami’an gwamnatin ne suka raka Sanusi II fadar da misalin ƙarfe 1:30 na safe.

  • Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
  • Sarki Biyu A Gari Ɗaya: Aminu Ado Ya Isa Kano

Wannan matakin na bikin tsakar daren ya biyo bayan wani yunƙurin shirin komowa da ake zargin hamɓararren sarki Aminu Ado Bayero ya ke yi, wanda baya gari a lokacin da aka yanke hukuncin tsige shi a jihar.

Sarkin Kano Sunusi Lamido II
Sarkin Kano Sunusi Lamido II

Sarki Aminu wanda aka naɗa shi a matsayin Sarkin Bichi a shekarar 2019 sannan kuma ya zama Sarkin Kano na 15, tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsige Sunusi Lamido II a shekarar 2020. Matakin da Gwamna mai ci a yanzu Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na mayar da Sanusi II na nufin  ya yi watsi da dokar da gwamnati Ganduje ta yi kenan ta rarraba masarautar Kani 5, inda ya yanzu gwamnan ya mayar da Sanusi II a matsayin Sarki tilo a jihar.

Duk da zaman ɗar ɗar da ake ciki Sarki Aminu ya koma Kano a safiyar yau Asabar inda magoya bayansa suka tarɓe shi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Magoya bayansa sun yi ta rera waƙoƙi da addu’o’i na goyon bayansa.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

Zuwansa Kano ya sa gwamnan jihar bayar da umarnin kama shi don zai haifar da hargitsi a jihar.

Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero

Mataimakin gwamnan Kano Comr. Aminu AbdulSalam ya bayyana cewa akwai hannun mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a cikin yunƙurin dawo da Sarki Aminu Ado kan karaga.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
Da Hannun Nuhu Ribaɗo Wajen Yunƙurin Dawo Da Aminu Ado Sarauta

Da Hannun Nuhu Ribaɗo Wajen Yunƙurin Dawo Da Aminu Ado Sarauta

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version