• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
4 hours ago
Yara

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi kananan yara, duba da yadda wasu iyayen suke yawaita bawa kananan yara kudi ba tare da sanin yadda za su kashe kudin ba. Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce a kan hakan/wane irin kira za a yi ga iyaye musamman wajen bawa yara kanana kudi?, ko akwai wasu illoli/matsaloli da ka iya faruwa game da hakan?. Ko akwai wani mataki da ya kamata sai yaro ya kai za a iya bashi kudi?”.

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano A Jihar Kano:

Masu aikata haka sam bai dace ba gaskiya, shawarata a nan ita ce mu daina bawa kananan yara kudi, sai idan sun zo da uzurin kudin to a siyo musu abin da suke so din ko a je dasu a siyo idan ma an ga abin ya kama a siya musun kenan. Eh gaskiya komai hankalin yaron to, akwai matakin da kai da kanka ka san yaron ba zai yi shirme da kudin da aka bashi ba. Misali kamar yaron yana son wani aikin lada da kudin ko kuma sana’a. Shawarata ita ce su sani wannan sam ba gata bane.

 

LABARAI MASU NASABA

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama:

A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su. Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace.

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace ba, domin yana da kyau idan iyaye za su bawa yara kudi to, su san me za su yi da kudin kafin ma su amince su bada, don haka zai taimaka wajen kula da tarbiyyar yaro. Eh gaskiya akwai, kamata yayi sai shekarun yaro sun kai na sanin abin da ya kamata da wanda bai kamata ba sannan a fara bashi kudi, domin ya kashe. Kuma ko da za a fara bashi ya kamata a san me zai yi da shi, kuma ana bibiyar sa akan abun da ya ce shi yayi. To, shawara ta a nan ita ce ya kamata iyaye suna taka-tsam-tsan wajen bawa yaransu kudi a kodayaushe ba tare da dalili na gaske ba.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Naija:

Wasu ya danganta da yanayin basu kudin da suke wasu suna ganin gata ne, wanda hakan ba gata bane har a guri na, misali ni inada yara mata to, ba na kokarin na ga na basu kudi sai na tabbatar da abin da za su yi me mahimmanci ko kati ko wano kwadayi yaro yana zaune yana sha’awar wani abu. Tunda matsayinka na uwa ba sana’a ka dorawa yaro ba dole za ka nema ka bashi. To, amma a haka kawai ka ce kana bawa yaro kudi dan jin dadi, wannan sangartawa ne, kuma hakan yakan iya janyiwa yaro shiga wani yanayi idan ya rasa kudi a wannan lokacin. Ni dai ina ganinba burgewa bane ko gata.

 

Sunana Sadi Dauda Baturiya, Kramar hukumar Kirikasamma Jihar Jigawa A Nijeriya:

A gaskiya har yanzu wasu iyayen suna gangancin sakarwa ‘ya’yansu, musamman yara kanana mara wajen ba su kudi ba tare da duba yanayi da kuma hankalin yaro ba, wanda kuma hakan yana haifar da matsaloli da dama. Matakan da ya kamata a dauka su ne, za a iya bai wa yaro karami kudi amma wanda bai fa sayi minti ko biskit ko madara da sauran ababen makulashe ya danganta da waje. Ni ganau ne ba jiyau ba na sha ganin yara da matasa da aka sakarwa mara wajen ba su kudi masu yawa da sunan soyayya, a karshe suka zama ‘yan shaye-shaye wasu kuma suka zama masu bin matan banza, wasu matasan ma gidan haya suke kama wa suna dauko matan banza, Allah Ya shirya mana matasannmu, da mu bakidaya amin.

 

Sunana Princess Fatimah Mazadu, Goben Nijeriya:

Wannan abu ne wanda ke gurbata tarbiyyar yara, wadanda ba a isa a saka su ko a hana su ba, dan gani suke kudi sune komai. Iyaye yara amana ce a garesu da su basu tarbiyya, saboda su yi alfahari da su ranar gobe kiyama, ba a hana ka bawa danka ba. Amma akwai hanyoyi da dama wanda za ka bayar wanda ba za a kira lalata tarbiyya ko sangarta yaro ba. Shekarun da hankalin yaro ake fara dubawa kan asakar masa manyan kudade gudun rudin duniya da lalacewa.

 

Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Eh magana ta gaskiya bata yaro ne, ana bashi kudi tun yana da karancin shekaru domin akwai illoli/matsala idan har ya saba da bashi kudi yana yaro. Matakin shi ne yaro ya kai shekarun sannin shi waye ne ma’ana ya san daidai komai kankanta ko ya san babu da rashi. Shawarar a nan ita ce; iyaye su daina bawa yara kudi suna yara ba tare da sun wakilta wani ‘ya’yansu ko antin su ba idan bukatar hakan ta tashi.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:

Wannan ba gata bane lalata yaro ne, kuma daga baya su iyayen abin yake shafa. In ya yaro ya mallaki hankalinkansa ya san ciwon kansa, dan bashi dan abin da zai bukata ba laifi bane. Su yi karatun ta-nutsu tun wuri, su daina tun lkan yansu su fada shaye-shaye, ato karshen kenan.

 

Sunana Muktari Sabo, Jahun Jihar Jigawa:

Hakika akwai iyayen da suke sangarta ‘ya’yansu da kudi don nuna gata hakan kuma yana illa sosai, daga illolin shi ne; idan bai samu ba yana iya daukar na wani, haka kuma kudin suna iya sa yaro ya lalace kamar shaye-shaye wani lokaci har da kula matan da ba sa’anninsa ba. Matakin shi ne ya cika hankali kamar yadda addini ya tanada idan har kudin yana da yawa, amma ba laifi bane a bashi dan kadan. Lalle ya kamata iyaye su kula da yaransu, kuma su san irin abin da ya kamata su bawa ‘ya’yansu don bukatarsu.

 

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Wannan ba wani abu bane face hanyar lalata tarbiyyar su da kuma samar da gurbacewar zamantakewar irin ta malam bahaushe tare da koyarwar addinin musulunci. Eh tabbas akwai, wannan mataki kuwa shi ne lokacin da yaro ya girma ya mallaki hankali sannan ya san ciwon kansa ya kuma san ciwon yadda ake samun kudi da nemansa da kuma ciwon rashinsa, ta yadda ba zai yi almubazaranci ba. Su kasance masu kula da tarbiyyar yaransu a lokacin da suke basu kudi, sannan su tabbatar da cewa kafin ma su basu kudin sun mallaki hankalisu ta yadda ba za su almubazaranci ba. Kuma su kashe kudi ta hanya mai kyau, domin samin dacewar rayuwa mai kyau a nan gaba

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kishi
Taskira

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

October 12, 2025
Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu
Taskira

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

October 4, 2025
Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu
Taskira

Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu

September 27, 2025
Next Post
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

LABARAI MASU NASABA

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

October 19, 2025
Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.