Sojoji sun bayyana a gidan Talabijin na Kasar Gabon, inda suka bayyana cewa sun kwace mulki.
Sun ce sun soke zaben da aka yi na ranar Asabar da aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin
- Sin Za Ta Gudanar Da Dandalin Koli Na Hadin Kai Bisa Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Karo Na 3 A Watan Octoba A Birnin Beijing
Hukumar zabe ta bayyana Mista Bongo a matsayin wanda ya lashe zabe da kashi biyu cikin uku na kuri’un da aka kada amma ‘yan adawa sun ce an tafka magudi.
Wannan matakin ya kawo karshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a kasar Gabon.
Sojoji 12 sun bayyana a Talabijin inda suka sanar da soke zaben tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”.
Daya daga cikin sojojin ya sanar a gidan Talabijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo karshen wannan gwamnatin.”
Mista Bongo ya hau kan mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2009.
Wane ne Ali Bongo?
Wasu na kallonsa a matsayin sangartaccen da, wanda ke kallon mulkin kasar Gabon a matsayin hakkinsa na gado.
Ya taba zama mawaki, inda daga baya ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaban kasar, ya dora a kan shekara 50 da iyalansa suka kwashe suna mulkin kasar.
Wasu kuwa na yi masa kallon mai kawo sauyi, kuma sun ce talakawa ne suka zabe shi bisa tsari na demokuradiyya.
Sai dai rashin lafiyar da ya yi fama da ita a shekarun baya sun haifar da tantama a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan biyu.
A ranar 7 ga Janairun 2019 wasu gungun sojoji sun yi yunkurin yi masa juyin Mulki, lamarin da bai yi nasara ba.
Sojojin sun ce dalilin yunkurin nasu shi ne domin su mayar da mulkin demokuradiyya a kasar bayan zaben shekara ta 2016, inda Mista Bongo ya yi nasara da kyar duk da zarge-zargen cewa an tafka magudi.
Gabon na daya daga cikin manyan kasashen Afirka da ke samar da man fetur, inda kusan kashi 90 cikin 100 na kasar dazuka ne.
Idan juyin-mulkin ya tabbata, to za ta kasance kasar Afirka ta takwas, reinon Faransa da aka yi wa juyin-mulki a cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai, sauran kasashen da suka fuskanci wannan yanayi a yankin Arewa su ke na Sahel inda mayakan jihadi suka ba da kafar korafi ko amfani da su wajen kifar da gwamnatin dimokuradiyya.