ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Take Kulawa Da Bukatun Kasashe Masu Tasowa Ya Sa Kasar Sin Ta Zama Aminiyarsu

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

A kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ziyarci wasu kasashe tsibirai dake yankin tekun Pasific, daga bisani ya bayyana cewa, “ Kar a bar kasashe marasa karfi su ci gaba da fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.” Maganarsa ta nuna bukatar kasashe masu tasowa ta neman samun ci gaba da wadata, da kuma dalilan da suka sanya kasar Sin ke samun goyon baya daga kasashe masu tasowa, wato saboda yadda take kulawa da bukatunsu.

Wani bayani da wata kwararriya a fannin tattalin arziki ta kasar Kenya Anzetse Were ta rubuta, wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na mujallar Diplomat ta kasar Amurka a kwanan baya, shi ma ya tabbatar da gaskiyar ra’ayina. Wannan bayani mai taken “Sirrin kasar Sin game da manufarta da ta shafi tattalin arzikin kasashen Afirka” ya nuna dalilin da ya sa kasashen Afirka suke nuna goyon baya ga kasar Sin.

Kasar Sin

ADVERTISEMENT

Da farko dai, a cewar Madam Anzetse, kasar Sin tana nuna daidaito ga kasashen Afirka.

Saboda yadda take bin manufofi na “zama daidai wa daida”, da “rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe”, kasar Sin ba ta taba neman yin shisshigi a nahiyar Afirka ba, ko kuma tilastawa kasashen Afirka bin tsarinta. Yayin da a nasu bangaren, kasashen yamma suna tsammanin cewa, ya kamata kasashen Afirka su bi dukkan shawarwarinsu, ko da yake, sun taba yi wa nahiyar mulkin mallaka.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

Na biyu shi ne, domin kasar Sin tana girmama ‘yancin kasashen Afirka na yin zabi bisa ra’ayin kansu.
Bayan da kasashen Afirka sun yi kira da a ba su karin damammaki na yin ciniki maimakon ba da tallafi kawai, kasar Sin ta amshi kiran a farko. Daga bisani, kasar Sin da kasashen Afirka sun fi mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, da raya bangaren kayayyakin more rayuwa, da sauran batutuwan da suka fi janyo hankalin kasashen Afirka. Yayin da a nasu bangare, kasashen yamma suke kallon kansu a matsayin abin koyi ga kasashen Afirka, ko da yake tsarinsu na raya tattalin arziki na fuskantar dimbin matsaloli, da suka hada da rashin daidaituwa tsakanin al’umma, da yawan samun tashin hankali, da masu fama da talauci, da dai sauransu.

Kasar Sin

Na uku, shi ne kasar Sin ta fahimci yanayin da kasashen Afirka ke ciki.
Saboda kasar Sin ta taba kasancewa a yanayi iri daya da kasashen Afirka, a fannin ci gaban tattalin arziki, don haka ta fahimci bukatun kasashen Afirka sosai. Wannan dalili ya sa hadin gwiwarta da kasahsen Afirka ke samar da dimbin alfanu ga kasashen. Misali, aikin gina kayayyakin more rayuwa a Afirka da kasar Sin ta zuba jari a ciki yana taimakawa rage gibin da ake samu tsakanin yankunan Afirka a fannin tattalin arziki, da rage tsawon lokacin da ake warewa da makamashin da ake konawa wajen yin zirga-zirga, da samar da dimbin guraben aikin yi, da damammaki na ciniki, da mika sabbin fasahohi da ilimi masu alaka da wannan fanni ga bangaren Afirka.

Kasar Sin
Yayin da a nasu bangare, kasashen yamma suke ci gaba da tsammanin cewa, ana yabawa kan yadda suke samun ci gaban tattalin arziki, kana kasashe daban daban na son ganin wata babbar kasa daga yammacin duniya ta zama mai fada a ji a duniya, domin hakan zai tabbatar da makomar duniya mai haske.

Amma a sabanin haka, yadda kasashe masu tasowa suke nuna rashin gamsuwa da tsarin kula da harkokin duniya karkashin jagorancin kasashen yamma, shi ma ya kasance daya daga cikin manyan dalilai da suka sa kasashen Afirka ke nuna karin goyon baya ga kasar Sin, wata babbar kasa da ta sha bamban da kasashen yamma. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

November 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

November 12, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Next Post
Manufar Amurka Ta “Monroe Doctrine” Ba Za Ta Samu Karbuwa Ba

Manufar Amurka Ta "Monroe Doctrine" Ba Za Ta Samu Karbuwa Ba

LABARAI MASU NASABA

Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

November 12, 2025
Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a

Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a

November 12, 2025
Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing

November 12, 2025
Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

November 12, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

November 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

November 12, 2025
Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

November 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.