A yanzu da bukatar dashen koda da hanta suke kara karuwa a musamman a kasashe masu tasowa, ana nuna damuwa a kan yadda safarar sassan jikin dan adam ke karuwa a Nijeriya musamama kuma ga wadanda suka dandana dadin safarar sassan jikin mutanen.
Ana samun karuwar wannan muguwar sana’a a kasashe masu tasowa, musamman a tsakanin mutanen da suke samun kazamin kudi ta hanyar abin a Nijeriya kamar yadda sashin bincike musamman na LEADERSHIP ya gano.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Xi Ya Taya Tebboune Murnar Sake Zama Shugaban Algeria
Masana sun ce harkar cire wani sashi a jiki mutum abu ne da ba shi da kyau kuma yana zama wani nau’i na cin zarafin bil adam, inda ake yaudarar mutane da ke da matsalolin rayuwa a cuce su. Ana bukatar wasu mutane marasa imani wajen aiwatar da wannan muguwar sana’a da ke cire wa mutum sassan jikinsa.
Wasu ‘yan Nijeriyan da lamarin yake damu su sun bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya su hada karfi da karfe domin samun nasarar fattatakar safarar sassan jikin da adam a kasar nan.
Biciken LEADERSHIP ya kuma nuna cewa, a kwai alaka a kan yadda ake samun karuwar garkuwa da mutane da karuwar haramtattciyar sana’ar ta safarar sassan jikin mutane a Nijeriya.
Misali a shekarar 2023, wani dalibin Jami’ar Fatakwal ya kashe budurwarsa inda ya cire mata wani sashen jikinta da niyyar yin tsafi da shi. An kuma gano cewa, sashen jikin da aka fi safararsa a Nijeriya shi ne koda.
Bayanai daga cibiyar tattara bayanai da karbar gudunmawa da dashen koda ta ‘Global Database on Donation and Transplantation’ sun nuna cewa a tsakanin shekarar 2015 da 2020, an yi dashen koda fiye da 651 ba bisa ka’ida ba a Nijeriya.
An kiyasta cewa, safarar sassan mutum ba bisa ka’ida ba a duniya na samar da tsakanin Dala miliya 840 da dala biliyan 1.7 a duk shekara a fadin duniya. Ana kuma sayen koda a kan ‘yan daloli a kasashe masu tasowa, daga bisani a sayar tsakanin dala 20,000 zuwa 30,000 a kasashen da suka ci gaba. An kuma kiyasta yin dashen koda fiye da 129,681 a shekarar 2020 kawai, inda aka samu koda 36,125 daga wadada suka mutu. Wannan ke nuna ana yin dashen koda akalla 15 a kusan duk awa 1 a duniya.
Saboda tsanannin rayuwa, a yanzu wasu ‘yan Nijeriya da dama suna sayar da wasu sassan jikinsu masu muhimmaci wanda hakan yana sanya rayuwarsu a cikin hadari. Wasu matan Nijeriya na shan wasu kwayoyi domin ya haifar musu da wani yanayi da kwan jikinsu zai bunkasa daga nan sai su sayar da su ga cibiyoyin bincike. Wasu dalibai mata na jami’a suna kuma sayar da kwan haihuwarsu ga masu bukata, masu amfani da shi wajen samar da jarirai ta fasahar ‘IBF’.
Ba kamar yadda abin yake a manyan kasashe ba, mata ke bayar da kwansu a karkashin kulawa da sa idon dokoki, amma a Nijeriya kananan ‘yan mata na sayar da kwansu kusan akalla a kan Naira 50,000.
An kuma samu wasu rahottanin da ke nuna yadda ake tilasta wa ‘yan mata sayar da kwansu a kan dan kudin da bai kai ya kawo ba. Akwai rahottanin kafafen yada labaru da ke nuna cewa, wasu matan masu shekara 16 na sayar da kwansu ba tare da samun jagoranci daga wani wakili ba.
A kwanaki ne, wani magidanci mai suna Olaniyi Iyiol, dan shekara 41 mazaunin Jihar Ondo ya bayyana cewa, talauci ya sa shi yanke shawarar sayar da daya daga cikin kodarsa duk da kuma yana sane da kasadar da ke tattare da dokokin yin haka da kuma yadda abin zai iya shafar lafiyarsa, amma saboda ba shi da wata hanya ta ciyar da iyalansa ya sa ya yanke wannan shawarar.
Wani abin takaii game da wannan lamarin kuma shi ne yadda wasu ‘yan Nijeriya masara imani ke daukar wasu matasa maza da mata daga kauyuka da alkawarin za a samar musu da aikin yi a birane amma cikakken dalin dauko su shi ne a cire musu wasu sassa a jikinsu domin a sayar.
A shekarar da ta gabata, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice da wani likita mai suna Dr Obinna Obeta, sun shiga hannu, aka kuma daure su a kasar Birtaniya saboda yaudarar wani matashi mai suna Dabid Nwamini, suka kai shi Birtaniya da niyyar cire masa koda domin a ba ‘yar Ekweremadu Sonia Ekweremadu, wadda ke fama da ciwon koda.
An daure Ekweremadu da abokan burninsa ne na tsawon shekaru a gidan yari bisa laifin safarar mutum zuwa kasar Birtaniya.
Wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa a kan yadda ake shigar da likitoci a wanan dambarwar.
A Abuja babbar birnin tarayyar kasar nan, an gano masu safarar sassan jikin mutane ba bisa ka’ida ba, bayan da aka gano wasu gungun masu aikata laifi da suka yaudari wani matashi dan shekara 16 mai suna Yahaya Musa, zuwa asibiti a Abuja tare da cire masa koda.
A wani rahoton da aka yada ta tashar talabijin ta intanet ta LEADERSHIP TB a makon da ya wuce, wani mutum mai suna Malam Musa ya bayyana cewa, an yi masa alkawarin naira miliyan 1 in ya yarda ya bayar da kodarasa. Ya yi bayani ne a mastayin mai bayar da shaida a babbar kotun babbar birnin tarayya Abuja da ke Zuba yayin da ake shari’ar ma’akata 4 na asibitin ‘Alliance Hospital and Serbices Ltd’, wadanda ake zargi da cire sassan jikin mutane ba da cikakken izini ba.
Hukumar yaki da safarar mutane ta (NAPTIP) ta gurfanar da Dr. Christopher Otabor, Emmanuel Olorunlaye, Chikaodili Ugochukwu, and Dr. Aremu Abayomi inda take tuhumar su da laifuka 11 da suka hada da cire sassan jikin dan adam ba tare da izinini ba. Babban lauya, Hassan Dahiru, ya bayyana yadda wadannan jami’an asibitin ke kan gaba wajen cire wa mutane sassan jiki.
Wannan wani misali ne na yadda rashin sanin doka da kuma hadarin da ke tattare da harkar cire sassan jiki ke azalzala lamarin safarar sassan jiki, haka kuma halin talauci da natsin rayuwa yana jefa wasu matasan fadawa tarkon masu safarar sassan jiki.
A martaninsa kan yadda lamarin yake kara kamari, shugaban kungiyar likitocin yankin Abuja, Dr Charles Ugwuanyi, ya nemi a samar da dokar da za ta taka wa masu safarar sassan dan adam birki, ya ce lamarin akwai tashin hankali ta yadda ake amfani da halin matsin rayuwua da talauci da al’umma ke ciki wajen jefa su halin da zai iya kai ga rasa rayukansu
Haka kuma wani abbban likita mai suna Oluwole Adeleke, ya ce a halin yanzu ya kamata masu ruwa da tsaki su shigo domin kawo karshen wannan lamarin gaba daya ba tare da bata lokaci ba.