Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako ga Abdelmadjid Tebboune, inda ya taya shi murnar sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Algeria.
Xi Jinping ya bayyana cewa, yana jinjinawa ci gaban da aka samu a dangantakar Sin da Algeria, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Tebboune, wajen amfani da cikar dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Algeria shekaru 10, a matsayin wata dama ta kara bunkasa aminci da fadadawa da zurfafa hadin gwiwarsu a aikace da hada hannu wajen kara damarmakin hadin gwiwar abota tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)
Talla