Wani jirgin Max Air da ya taso daga Legas tayarsa ta yi bindiga tare da kamawa da wuta yayin sauka a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano a daren Talata.
Jirgin na ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida lokacin da ya sauka da misalin ƙarfe 10:19 na dare.
- Ademola Lookman Ba Zai Buga Wasan Atalanta Da Barcelona Ba
- Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya
Abin farin ciki, ba a samu wanda ya ji rauni ko asarar rai ba.
Wani fasinja, Aliyu Inuwa Mansir, ya bayyana yadda abin ya faru.
“Da zarar tayar jirgin ta fashe kuma ta kama wuta, hayaƙi ya cika cikin jirgin, dole muka fice ta kofar gaggawa yayin da ma’aikatan kashe gobara suka yi sauri domin kashe wutar.”
Shugaban Max Air reshen Kano, Bello Ramalan, ya tabbatar da cewa duk fasinjoji sun tsira cikin koshin lafiya kuma ya nemi afuwar jama’a kan abin da ya faru.
Hukumar binciken hatsarin jiragen sama ta Nijeriya (AIB) na gudanar da bincike kan musabbabin lamarin, wanda ake zaton ya faru ne sakamakon matsalar taya.
Max Air ya tabbatar da cewa za ta tallafa wa fasinjoji wajen dawo musu da kayansu yayin da bincike ke gudana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp