Wasu daga cikin masana a fannin aikin noma a Kasar nan sun bayyana cewa, tsare -tsare da kima shirye-shiyen da gwamnatin tarayya ta KirKiro da su, sun taimaka matuKa wajen Kara habaka noma a Nijeriya, inda suka yi nuni da cewa, hakan ya Kara taimaka wa manoman Kasar wajen samun kudaden shiga masu dimbin yawa.
In za a iya tuna wa dai, gwamnatin tarayya, tun hawan ta a kan Karagar shugabancin Kasar ne ta mayar da hankali ta hanyar babban bankin Nijeriya inda ta KirKiro da tsare-tsaren kamar na “Anchor Borrowers” domin ta Kara bai wa manoman Kasar Kwarin gwiwar Kara bunKasa sana’ar ta su ta noman.
Gwamnatin Nijeriya ta fito da tsare-tsare da dama na bunkasar harkar noma ta hannun babban bankin kasar CBN.
Masanan sun yi nuni da cewa, shirye-shiyen da kuma tsare-tsaren da gwamnatin ta samar tun a shalekarar 2015 kamar ta hanyar bar da bashin yin noma da sauransu hakan ya taimaka wajen Kara samar da abinci a Kasar da kuma Kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa.
Tun a farkon fara wanzar da tsare-tsaren da kuma shirye-shiyen manoma da dama manya da kuma Kanana da ke a Kasar nan musamman manoman shinkafa sun samu dimbin kudaden shiga tare da kuma Kara wadata Kasar da abinci.
Sai dai wata matsalar da ake fuskanta ita ce yadda wasu manoman suke kin biyan bashin da aka ba su.
Sai dai, masanan sun yi nuni da cewa, akwai buKatar gwamnatin tarayya da ta Kara sa ido kan yadda ake wanzar da shirye-shiyen da kuma tsare-tsaren ganin cewa, a wasu yankunan da ke a Kasar nan, shirye-shiyen da kuma tsare-tsaren ba sa tafiya yadda ya kamata.