Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai muku bayani akan yadda za ku hada Boga.
Abubuwan da za ku tanada:
Burodin Boga, Salad, Tumatur, Ciz Na Boga, Albasa, Kokumba, Nama na Boga, Mustad:
Yadda za ku hada:
Da farko idan kika samu burodin boga sai ki yanka tsakiyarsa ki ajiye shi a gefe, sannan ki gyara tumatur dinki ki yanka shi a kwance wata ‘Circle’ a turance shima ki ajiye shi a gefe, sannan kokumba itama ki wanke ta da dan gishiri ki yanka ta a kwance ‘Circle’, sai albasa ita ma ki yanka ta a kwance ‘Circle.’
Sannan boga ciz din shima ki yanka shi kwana hudu wato ‘Skuare’ a turance, sannan salad din ki wanke shi sai ki dan cire masa wannan dan farin na idan za’a yanka shi amma kar ki yanka haka za ki barshi ki ajiye a gefe.
Sannan ki soya naman na boga ki dauko Mustad din sai ki shafa a jikin Burodin sannan Salad din ki shimfida a kansa, sannan tumatur shima ki jera akai, sai Kwakwamba, ita kuma ki jera sai albasa itama ki jera, sannan ki shifida ciz din shima a sama, sannan ki dauko daya yankan Buredin ki shafa masa mustad din sai ki rufa a kai sai ki dan sanya shi a oben ya dan gasu haka ko kuma a ‘fry pan’ abin suya. Za ki iya yin sa a karin kumullo a ci da shayi, a ci dadi lafiya.