Ci Ka Yi Santi
Abubuwan Da Yakamata Uwargida Ta Tanada:
Kwai, Nama, Kuri, Magi, Gishiri, Tumatir.
Assalamu alaikum. ‘Yan Uwa barkammu da sake saduwa a cikin wannan shiri namu na
Girki Adon Mata) mai albarka shiri ne da yake kawo muku yadda Uwargida zata rika hada abinci kala-kala.
Yadda Ake Hada Ci Ka Yi Santi:
Da farko za ki fara dafa kwanki daidai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, ki sa magi, kuri, gishiri, ki kada ya kadu sosai, ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai.
Yadda ake Awaran kwai
Abubuwan hadawa; Kwai, Attarugu, Albasa, Man, Magi, Leda.
Yanda ake hadawa;
Da farko za ki sami kwanki ki fasashi a kwanonki mai kyau ki kada shi, sai ki zuba kayan hadinki: attaruhu, da albasa wanda dama kin yi giretin nasu da sauran kayan dandano dai-dai misali.
Sai ki dinga zuba kwan naki a cikin leda kina yi masa kamar kullin alalan leda, sannan sai ki dora ruwanki cikin tukunya ki dafa kullallen kwan naki, idan ya dahu sai ki kara fasa wani kwai, kuma ki cire wannan kwan naki na leda kina yanka shi yankan tsakiya za ki ga ya ba da alamu kamar zanen zuciya, watau ‘heart’ sai ki dinga tsoma shi a cikin wannan kwan naki
Sai kuma ki soya shi a manki mai zafi sosai, amma ki yi suyar sama-sama don ya yi kyau. A ci dadi lafiya.
Egg Sauce
Abubuwan da za ki tanada:
Kwai, Albasa, attaruhu, tattasai, kuri, Magi, gishiri, tafarnuwa, kuri powder, mai.
Yadda za ki hada:
Da farko za ki jajjaga kayan miyan duka su jajjagu sosai, sai ki zauna ki yanka albasa dinki isashe ko kuma ki nika. Daga nan zai ki dauko frying pan ki sa a wuta, ki sa masa mai kamar cokali uku, sai idan ya fara zafi sai ki juye dukkanin albasarki, ki soya man da shi, daga nan sai ki juye kayan miyan, ki sa magi, gishiri, kuri kadan.
Ki cigaba da soya shi, kuma a lura da wuta, saboda ana so ya dan dahu kayan miyan musamman idan da yawa ne, za ki iya dan rufe kayan miyan ko da na minti biyu ne saboda ya yi taushi in ba ruwa za ki iya diga ruwa.
Daga nan sai ki dauko kwai din wanda dama kin fasa kin kada sai ki juye, ki jujjuya su hade sosai. Idan kina so ya yi dunkule-dunkule, zaki bar shi ne har sai ya fara soyuwa, sai ki rika juya shi ba tare da kin barbaza ba. In kuma kina so sai ki barbaza shi. Kwai din na gama soyuwa sai ki sauke ya yi.
Wani Hadin:
Shi kuma wannan wasu suna fasa kwai ne a kwano, sai su juye dakakken kayan miya da albasa din su a cikin kwai din, sai su sa mai ya dan yi zafi sosai su juye shi ya soyu. Ana cin egg sauce da Plantain, dankali, doya, da ma sauran su.
Mata da yawa suna bata sauce din su ne ta hanyar zabga tumatir, amma ni ban yarda da tumatir ba a sauce. Idan ma za ki sa tumatir to kada ya wuce guda daya, saboda yana sa shi ya yi ruwa, kuma yana sawa a ji tsami, yana kuma bata dandano idan wacce bata iya ba ta sa.
Egg sauce ana cin sa da abubuwa da yawa, ba wai dole sai dankali, doya ko plantain ba.
Don haka In za ki yi na miya da yawa ne ake yi.