A ranar Juma’a 27 ga Mayun 2022 ne aka bayyana cewa wani katoton dutse zai wuce ta gaban duniyrmu ta Earth.
An sanya wa dutsen suna ‘Asteroid 7335’ (1989 JA) sannan kuma tsawonsa ya fi mil daya.
Hukumar Binciken Sararin Subhana ta Amurka (NASA) ta ce dutsen na asteroid, shi ne mafi girma da ya zo wucewa ta kurkusa da Earh a wannan shekarar.
Sai dai hakan ba wani abin damuwa ba ne – zai wuce lami lafiya ta gaban duniyar tamu da nisan mil miliyan 2.5.
Tawagar da ke bayar da bayanai kan hakan da ke cibiyar binciken abubuwan da ke zuwa kusa da duniyar Earth ta Nasa – wacce ke bin diddigin duwatsun da ke yawo a sararin samaniya kamar irin su astiroyid da kwamet da kananan duniyoyi, ta ce dutsen astiroyid din, wanda shi ne na farko da aka gano fiye da shekara 30 da suka wuce, zai bi ta gaban duniyar ne ranar Juma’a 27 ga watan Mayu.
Tsawon dutsen ya kai mil 1.1, wato ya nunka ginin da ya fi kowane tsawo a duniya Burj Khalifa, har sau biyu.
Masana kimiyya sun ce yana daga cikin duwatsun astiriyod mafi girma da suke nazarinsu, kuma sun yi kiyasin cewa yana tafiyar kusan mil 30,000 a duk awa daya.
Wannan dutse na astiriyod yana daga cikin abubuwa 29,000 da ke yawo a sararin samaniya da ake kira da (NEOs), wadanda Nasa ke sa ido a kansu duk shekara.
Sai dai kuma da wuya su iya fadowa cikin duniyar Earth.
Kazalika Nasa tana da shirin kawar da duk wani abu da ka iya fadowa duniya a nan gaba.
A bara ne hukumar binciken sararin samaniyar ta kaddamar da kudurin bai wa duniya kariya a karon farko.
Ana kiran shirin da The Double Asteroid Redirection Test (Dart), kuma ana yin gwajin ne da nufin kare duniyar Earth daga duk wata barazana ta duwatsun astiriyod a nan gaba.
Ana sa ran dutsen 7335 (1989 JA) ba zai sake zuwa kusa da Earth ba har sai watan Yunin shekarar 2055, kuma a lokacin da ya wuce ne ta gaban duniyar a nisan da ya fi na wannan wucewar.