• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Wani Tsohon A Kauyen Liujiayuan Ya Bude Sabon Babin Shiga Wasanni Na Zamani

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Yadda Wani Tsohon A Kauyen Liujiayuan Ya Bude Sabon Babin Shiga Wasanni Na Zamani

Gasar wasan kwallon tebur da aka gudanar a kauyen Liujiayuan

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Idan aka shuka wani iri mai siffar wasan motsa jiki, me za a girba? Akwai wani kauyen dake arewa maso yammacin kasar Sin, wanda aka gano yana kokarin raya wasannin motsa jiki, kuma ya bude sabon babin shiga harkokin wasanni na zamani.

Wannan kauye mai suna Liujiayuan, wanda yake da tarihin shekaru kimanin dubu 3, tsohon kauye ne a kasar Sin.
A matsayin tsohon kauye mai alama a tsakiyar lardin Shaanxi dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, kauyen Liujiayuan ya kan girbe hatsi mai yawa a kowanne lokacin zafi. Mazauna kauyen kan yi aikin gona a duk tsawon shekara, amma wani tsoho mazauni kauyen ya canja yanayin kauyen ta hanyar wasan motsa jiki.

  • Sin Ta Ba Da Agajin Kayayyakin Aikin Jinya Ga Syria

Chen Changlin, manomi mai shekaru 62 da haihuwa, ya sanya karamar riga ta motsa jiki, yana rike da allon hannu na buga kwallon tebur, ya kuma shirya tsaf don shiga gasar manoma tare da sauran masu sha’awar wasanni dake wannan yanki. A duk yammaci a kan ga magidanta da dama cikin irin wannan yanayi a kauyen Liujiayuan, dake gundumar Qishan ta arewa maso yammacin kasar Sin.

Mazauna kauyen Liujiayuan, mai tarihin shekaru 3,000 da kafuwa wanda ke karkashin birnin Baoji na lardin Shaanxi, suna atisayen wasan kwallon tebur ko “table tennis” a zauruka rufaffu da filaye.
Duk da cewa ba a Liujiayuan aka haife shi ba, Chen yana aikin noman ganyaye da ’ya’yan itatuwa a wannan kauye a tsawon shekaru, tuni kuma ya samu damar gudanar da rayuwa mai inganci ba tare da fuskantar kangin talauci ba. Chen, wanda ya fara wasan “table tennis” yau shekaru sama da 40 da suka gabata, ya gamu da sauran masu sha’awar wasanni da yawa a wannan kauye.

Liujiayuan
•Chen Changlin, mazaunin kauyen Liujiayuan

A cewarsa, “Buri na shi ne tattaro masu sha’awar wasan kwallon tebur dake gundumar Qishan, yadda za mu zama kungiya guda, mu rika koyo daga juna.”
Burin Chen ya cika bayan shekaru masu yawa, inda ya kai ga buga gasar kwallon tebur ajin da ba na kwararru ba. Hakarsa ta cimma ruwa, lokacin da aka kafa kungiyar kwallon tebur ta manoma Qishan, ko QFTTA a takaice a ranar 9 ga watan Yulin shekarar 2021.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Bikin kaddamar da wannan kungiya, ya samu halartar shugabannin hukumar wasanni ta lardin Shaanxi, da wakilan hukumar kwallon tebur ta kasar Sin, da jami’an karamar hukuma, da ma tsohon zakaran kwallon tebur na duniya Qi Baoxiang.

Chen wanda yake cike da shauki murya na rawa na cewa, “Lokaci ne da ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwa ta. Kungiyar na kunshe da manoma dake kauyuka daban daban, yanzu mun samu kungiyar kwallon tebur ta mu ta manoma.”

Burin Chen bai tsaya a nan ba, domin kuwa bayan shekara guda da kafa kungiyar, an shirya gasar kwallon tebur ta Qishan ajin manoma. Karamar hukumar wurin, da kungiyar QFTTA ne suka shirya gasar, wadda ita ce irin ta ta farko da aka gudanar a lardin Shaanxi. Ta kuma hallara masu fafatawa sama da mutum 100 daga kauyuka 25 na Qishan, da makwaftan gundumomi dake Shaanxi.

Liujiayuan
Wasan ja-in-ja da mazaunen kauyen suke gudanar

Chen ya ce, “Jimillar monoma 1,300 sun yi rajistar shiga wannan gasa, kuma ta tattaro sassan al’ummun sama da kauyuka 40 dake Qishan. Na yi farin cikin ganin yadda mutanen dake kewaye da ni ke kara kwarewa yayin gasannin dake gudana. Baya ga kara yawan mambobin kungiyar mu dake shiga wannan wasa, mun kuma karfafa ginshikin wasan, muna yawan shirya gasanni tsakanin ‘yan wasan kauyukan dake kewayen nan”.
Yayin gasar yini guda da aka gudanar, Chen wanda ya wakilci kungiyar QTTA, ya zamo na 2.

Kyaftin din kungiyar kauyen Liujiayuan Zhou Wenlin, ya ce tun da farko kauyen Liujiayuan ya raba rukunoni 5 na ’yan wasa maza da mata, domin shiga gasar ta kwallon tebur a gasar, kuma 4 daga cikin su sun wuce matakin rukuni na gasar.

Zhou Wenlin, wanda kuma shi ne sakataren JKS reshen Liujiayuan ya kara da cewa, “Akwai masu sha’awar kwallon tebur a Liujiayuan. Gasar ta kayatar domin kuwa an fafata, musamman wasan da muka buga a wajen yankin Qishan. Ina ganin sauyin da muka samu a wannan kauye yana da nasaba da kwazon Chen, domin ya karfafa mana gwiwa, inda manoma da yawa suka rika shiga harkokin motsa jiki na yau da kullum. Mazauna wannan yanki sun yi amannar cewa, Chen na da kwazon jagorantar su wajen fita daga kangin talauci, da kuma samun kyautatuwar rayuwa ta hanyar inganta kiwon lafiya.”

Liujiayuan
Mazaunan kauyen Liujiayuan suna wasan kwallon tebur

Zhou ya kara da cewa, “Wannan kauye ya shirya wasanni daban daban domin biyan bukatun manoma ta fuskar motsa jiki na yau da kullum. Baya ga wasan kwallon tebur, da kwallon kwando, an kuma fara gudanar da rawar motsa jiki ta Yangko, da sauran wasanni a kauyen. Mazauna kauyen na buga wasan kwallon tebur, da kwallon kwando da sauran wasannin motsa jiki tare, wanda hakan ke yaukaka alakar su a matsayin iyali guda kuma makwaftan juna. Kauyen Liujiayuan yana kara zama na zamani, kuma mazaunan sa na samun karin ingancin rayuwa ta hanyar wasanni.”

A baya bayan nan, ma’aikatar noma da raya karkara, da hukumar raya wasanni, da hukumar farfado da yankunan karkara na Sin, sun yi hadin gwiwar fitar da ka’idoji na samar da ci gaba mai inganci a fannin wasannin manoma, da inganta karfin jikin su cikin tsarin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14. Karkashin manufar kasar Sin ta gina jagorancin bunkasa wasanni da inganta kiwon lafiyar al’umma, manoma suna da bukatar samun kayayyakin wasanni masu inganci, da suka hada da wuraren motsa jiki, da jagorancin kwararru, musamman a wannan lokaci da wasannin ke kara samun karbuwa cikin shekarun baya bayan nan.

A cewar Chen, “Yankunan karkara na kara bunkasa, kuma manoma suna son samun irin rayuwa mai inganci irin ta birane. A yanzu muna da karin zabi na samun nishadi cikin rayuwar mu ta yau da kullum.”

A nasa bangare, babban alkalin wasan kwallon tebur, kuma babban sakataren kungiyar kwallon tebur ta Baoji Tian Junqing, cewa ya yi ta karkashin gasar Qishan, ci gaban wasannin manoma ya kyautata karfin jiki da na tunanin mutane, ya kuma karfafa manufar aiki tare tsakanin al’ummun yankin.
A matsayin sa na babban alkalin wasan kwallon tebur Tian, ya ce yana iya ganin karfin hali, da jajircewar manoman dake shiga a dama da su a wasan kwallon tebur.

Ya ce, “Kwazon su, da rashin karaya, da rashin tsoro, da sanayyar su game da gasanni, sun karawa wasanni karsashi a yankin, tare da taimakawa manufar farfado da yankunan karkara.”
Koci Tian ya kara da cewa, “Gudanar da irin wannan gasa ta manoma, baya ga ingiza ci gaban karkara da ake samu, matakin yana kuma alamta ci gaban rayuwar manoma a fannonin kiwon lafiyar jiki da tunani. Fatan mu shi ne ganin an kara fadada harkokin wasanni a yankunan karkara a dukkanin sassan kasar Sin.”

Liujiayuan
Mazaunen kauyen sun gudanar da gasar wasan kwallon kwando

Bayan gama ayyukan gona a kauyen Liujiayuan, sai mazaunan kauyen su fara shiga wasannin motsa jiki, ban da wasan kwallon tebur, akwai sauran wasanni kamar su wasan kwallon kwando, da kwallon badminton, da wasan ja-in-ja, da raye-rayen gargajiya na kauyen wato Yangge, da raye-raye a babban fili da dai sauransu, wadanda suka kawo zaman jin dadi a rayuwar mazaunan kauyen, kuma ta hakan kowane mazauni na iya zabar irin wasannin da yake so, lamarin da ya kawowa kauyen sabon yanayi na jin dadin rayuwa. (Zainab Zhang)

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gudummawar Mata A Harkar Samar Da Tsaro A Nijeriya (Ra’ayinmu)

Next Post

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Kano

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

11 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Kano

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Kano

LABARAI MASU NASABA

Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

May 15, 2025
ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

May 15, 2025
‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.