• English
  • Business News
Monday, October 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Wasu Jihohi Suka Yi Watsi Da Gine-ginensu Da Ke Legas

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Jihohi

Jihar Legas ta yi gargaɗi kan yadda wasu mutane suka mayar da gidajen jihohin ya dace su zama ofisoshi zuwa gidajen karuwai, wanda hakan ke barazana ga tsaro. Masu yi wa gidaje ƙima sun ce kasancewar jihohin suna da wasu gidajen a Abuja hakan bai zama hujja ba, a maimakon haka, ko dai su sayar da na Legas ɗin ko kuma su bayar da su haya.

Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko an gina gidajen ne domin su zama ofisoshin tarayya na wakilai, amma a halin yanzu a Jihar Legas ana amfani da su a matsayin gidajen baƙi da ba na hukuma ba, kuma a wasu daga cikinsu ma sun zama gidajen karuwai, kamar yadda binciken da LEADERSHIP WEEKEND ya nuna.

  • NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas 
  • Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC 

Waɗannan kadarorin mallakar gwamnati da suke a wurare masu daraja a Legas, na ƙara fuskantar samun sauyi daga manufar da aka gina su zuwa haifar da matsalar tsaro.

Bincike ya nuna cewa da yawa daga cikin waɗannan gine-gine, da aka yi su da nufin sauƙaƙa ayyukan gudanarwa da diflomasiyya ga gwamnatocin jihohi daban-daban, a halin yanzu ba a amfani da su dta hanyar da ta dace ko kuma ba a yunƙurin yadda za a hana masu aikata laifuka yin amfani da su.

Masana harkokin tsaro da mazauna yankin da suka damu sun nuna fargaba kan kwararar wasu mutane da ake zarginsu da aikata miyagun ayyuka a cikin waɗannan wuraren, inda suka yi gargaɗin cewa lamarin ba wai kawai na zubar da mutuncin jama’a ba ne, har ma yana yin barazana ta zahiri ga tsaro da gudanar da harkokin birane a babban birnin kasuwancin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako

Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai.

Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas.

Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke makwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matukar hadari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan jihar a Legas.

Wakilanmu da suka ziyarci ofisoshin hulɗa da jama’a ga ‘yan iskan gari, sun tabbatar da cewa mutane suna zuwa wurin ba bisa ƙa’ida ba domin neman mafaka tare da biyan masu kula da gidajen kuɗi.

A wasu ofisoshin da akwa na jihohin Arewa, waɗanda ake kasuwanci da su ba bisa ƙa’ida ba ‘yan kasuwa, masu sana’a, da ma’aikatan gine-gine da ke aiki a wurare daban-daban a faɗin Legas. An ba da rahoton cewa jami’an haɗin gwiwar sun canza ofisoshin gudanarwa zuwa abin da suke kira ƙakunan “Arrangee” ko “wurin barci”, da kuma ofisoshin talla da shagunan caca. Waɗanda suka kama hayar wurin ba bisa ƙa’ida ba, maza da mata, sun kuma mayar da ofisoshin gidajen zama.

An ruwaito cewa wasu mutanen ma sun kwaso iyalansu sun zo sun tare a waɗannan gidaje, yayin da tuni wasu ma har sun hayayyafa suna renon ‘ya’yansu a wurin. Yawancin waɗannan tsoffin gine-ginen da ke Ɓictoria Island, yanzu sun lalace, inda ‘yan kama wuri zauna ba bisa ƙa’ida ke aiwatar da haramtattun ayyuka a fili ba tare da takura ba.

LEADERSHIP WEEKEND ta ci gaba da cewa, wasu daga cikin waɗannan gidaje an yi watsi da su gaba ɗaya kuma jihohin da suka mallake su sun yi watsi da su, wanda hakan ya ba da damar ‘yan damfara su gudanar da ayyukansu cikin walwala. Wasu mutane sun canza sassan ofisoshin zuwa wuraren caca, mashaya na gida, gidajen abinci, da kuma abin da ake kira ɗakunan Arrangee da kuma ɗakunan bacci.

Gidajen Jihohin Kwara, Borno, Bauchi, Adamawa, Zamfara, Nasarawa, Gombe, Benue, Kebbi, Imo, Bayelsa, da Ribas na daga cikin waɗanda abin ya shafa. Ziyarar da aka kai wa waɗannan gine-ginen ya nuna cewa yawancin gine-ginen sun lalace, inda jami’an tsaro da ke gadin ginin ke ba da hayar ɗakunan da ke cikin ofisoshin a matsayin ɗakunan yi “barci ka tafi”.

Adamawa

A Jidan Jihar Adamawa, ya yi matuƙar rauni, saboda a hankali sassan ginin ya lalace yana kuma dab da rugujewa idan gwamnatin jihar ba ta sa baki ba. Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane ‘yan Jihar Adamawa ne suka mamaye wasu sassan ginin, inda suka bar shi ba tare da kulawa ba, ƙazanta, sannan tankuna ruwan gidan duk sun farfashe, magudanan ruwa da rufin gidajen duk sun lalace.

Zamfara

Wasu daga cikin ’yan damfara ne a cikin gidan Jihar Zamfara da ke kan titin Adeola Odeku, Ɓictoria Island, inda suka ce suna zaune ne a ginin ne saboda kusancinsa da wuraren aikinsu. Nau’in mtanen da ke cikin gidan dai direbobi ne da kuma masu aikin shara.

Binuwe

Wani bincike da wakilinmu ya yi ya gano cewa an bayar da hayar gidan Binuwe da ke Legas inda a yanzu otal ne na Presken tun daga shekarar 2020. Presken ya karɓe ofishin inda ya mayar da shi otal, da wurin sayar da barasa.

Kuɗin ɗakunan da ke ofishin Liaison Office na Binuwe, wanda yanzu haka Presken Hotels and Resorts Limited ke gudanarwa, ya fara daga Naira 56,000 zuwa Naira 153,000, gwargwadon girman ɗakunan.

Kwara

A gidan Jihar Kwara, wani jami’an tsaro da wakilinmu ya gana da shi, ya ce a yanzu an hana ba da wurin baccin yi ka tafi, an gama gyara wurin. Da aka ci gaba da bincike, sai aka gani cewa iyalai da dama, galibinsu Fulani Musulmi, a halin yanzu suke zaune a ofisoshin na Jihar Kwara, inda suke fakewa a can.

Ya musanta duk wani shiri da gwamnati ta yi na sayar da kadarorin amma ya yarda cewa ana ƙoƙarin gyara ginin, tare da shirin fara aiki nan ba da daɗewa ba.

Nasarawa

A Ofisoshin Nasarawa, wasu Hausawa ne da fulani ke zaune a ciki, yayin da masu sana’ar hannu, kamfanin lotto, da masu sana’ar Betnaija suka kama suna gudanar da harkokin kasuwanci a harabar.

Jihohin Ribas Da Bayelsa

Ga Ofisoshin Jihar Ribas da Bayelsa, duk da cewa suna yanki guda a fannin gudanarwa kuma ofisoshinsu na aiki ɗaya, jami’an tsaron da ke ƙofar gidan su kan yi sulhu ta hanyar karɓar kuɗi daga hannun mutane tare da ba wa masu kwana ɗaki don samar wa kansu kuɗaɗen shiga. Ɗaya daga cikin jami’an tsaro na ofishin jihohin Bayelsa da Ribas ya ce, “Mu jami’an tsaro ne guda uku da ke bakin aiki, duk wanda ya ke son ya biya ya yi ajiya sai ya sasanta da mu uku kafin mu ba shi ɗakin su kwana.

Filato

Binciken da aka gudanar a ofishin Jihar Filato da ke kan titin Ahmadu Bello a Legas, ya nuna cewa ofishin a yanzu ya zama wani sansanin wucin gadi da ke dauke da wasu ‘yan tsiraru kamar sansanin ‘yan gudun hijira, inda ake saukar ‘yan gudun hijira.

Bauchi da Gombe

Ga ofishin Jihohin Bauchi da Gombe da ke Legas, binciken da wakilinmu ya gudanar, ya zanta da ɗaya daga cikin jami’an tsaro mai suna Isiaka, inda ya bayyana cewa, suna da hannu dumu-dumu a cikin sa-in-sa da ake yi a ɗakin da ake kira ‘arrangee’, inda mutane za su riƙa kawo mata karuwai.

Ya ce kuɗin hayar ya fara ne daga Naira 4,000 zuwa Naira 15,000 a ɗakuna “baccin yi ka tafi”.

Gidan Jihar Bauchi ya zama cikakken sansanin ‘yan gudun hijira a Legas, inda ake tsugunar da mutane iri-iri da suka hada da ‘yan gudun hijira da kuma waɗanda ke fuskantar matsalar masauki. Su kan kafa tanti na wucin gadi, suna shimfiɗa don su rufa wa kansu asiri idan sun yi barci. Isiaka ya shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa, “Muna da ɗakunan Naira 7,000, Naira 8,000, Naira 10,000, da kuma Naira 15,000, amma ba mu da ruwa ko banɗaki ga duk wanda zai kwana a nan, sai dai idan ka je banɗaki da ɗakin wanka da ke kusa da kai.”

Kano Da Sakkwato

Dangane da Ofisoshin Kano da Sakkwato kuwa, suna da ɗimbin jama’a, galibinsu masu yankan farce ne da masu sayar da abinci, da masu sana’ar hannu waɗanda suka mamaye kewaye da gaban ofishin.

Abia

Dangane da ofishin jihar Abia kuwa, jami’in tsaron da ya bayyana sunansa da Hosea Alli ya shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa yana karɓar Naira 20,000 na wani ɗakin kwana da ke cikin ofishin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

nema
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

October 13, 2025
Sojojin somaliya
Manyan Labarai

Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako

October 13, 2025
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
Manyan Labarai

Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba

October 12, 2025
Next Post
Sin Na Gaggauta Gina Tsarin Tattalin Arziki Mai Kiyaye Muhallin Halittu

Sin Na Gaggauta Gina Tsarin Tattalin Arziki Mai Kiyaye Muhallin Halittu

LABARAI MASU NASABA

hisba

Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano

October 13, 2025
Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang

Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang

October 13, 2025
Nijeriya

Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista

October 13, 2025
Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano

Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano

October 13, 2025
nema

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya

October 13, 2025
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya

Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya

October 13, 2025
Sojojin somaliya

Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako

October 13, 2025
Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

October 12, 2025
Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”

October 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.