Na kasance mai son tafiye-tafiye, musammam zuwa wuraren da ban taba zuwa ba. Sai dai, duk da na taba zuwa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin a shekarun baya, samun labarin zan kara zuwa, ya matukar faranta min rai, musamman ma da na ji cewa zan ziyarci wani bangare da ya saba da wanda na je a baya. A wannan karo, na tashi ne daga birnin Beijing zuwa Hotan, wanda ake kira da Sinanci da Hetian, dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang, inda na yi tafiyar kimanin sa’o’i 5 cikin jirgin sama.
Galibinmu mun san Hamada ne a baki da kuma hotuna, ba tare da gane yanayin illolinta ga muhallinmu da ma bil adama ba. A tsawon zamana a kasar Sin, na samu damar ganewa idanuna hamada masu girma biyu dake kasar, wato Hamadar Kubuqi dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin da na ziyarta a shekarar 2018 da wani bangare na Hamadar Taklimakan dake jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta da na ziyarta a watan Augustan 2023.
- Shawarar BRI Ta Kawo Manyan Sauye-sauye A Duniya Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
- Sin Ta Kai Daukin Gaggawa Ga Falasdinawa
Abubuwan da na gani da idanu na a gundumar Tsele ta yankin Hotan (Hetian) su ne suka ankarar da ni game da kiraye-kirayen da ake yi na “a daina sare bishiyoyi”. Na dade ina jin wannan kira, har ma na kan ce, “idan muka daina sare bishiyoyi, shin da me za mu yi girki?” An ce rashin sani ya fi dare duhu. Akwai hanyoyi masu dimbin yawa na yin girki da makamashi masu tsafta wadanda kuma suka fi sauki, yayin da illolin da sare bishiyoyi kan haifar suka zarce sanin mutum.
Misali, a gundumar Tsele ta yankin Hotan da na ziyarta, al’umma sun yi ta kaura daga muhallansu har sau uku, saboda matsalar hamada, amma a yanzu saboda wasu fasahohi, musamman shuka bishiyoyi, al’ummar Tsele sun samu wurin zama, domin sun yi nasarar takaita kwarar hamada.
Babban abun da ya burge ni a wannan wuri shi ne, yadda suka yi amfani da dutse daya wajen harbin tsuntsaye biyu. Irin bishiyoyin da aka shuka a gundumar Tsele, ba bishiyoyi ne kadai domin kare kwarar hamada da kiyaye muhalli ba, suna kuma samar da kudin shiga. Mutanen yankin sun shuka bishiyoyi kamar na magarya da tuffa da gyadar Walnut da Inibi da sauransu. Wadannan bishiyoyi na zama hanyar samun kudin shiga baya ga kare muhalli.
Duk da cewa babu hamada ta ainihi a Nijeriya, wasu yankunan kasa a arewa maso gabashi da kuma yammaci, na fuskantar barazanar Hamada. Ta yaya za mu bayar da gudunmuwarmu wajen ganin matsalar bata haifar mana da illa mai tsanin ba?
Darasin da za mu iya dauka a nan shi ne, da farko, mu daina sare bishiyoyi domin suna da matukar amfani. Haka kuma mu sa kaimi wajen shuka wasu sabbi. Ko da muna ganin ba za mu iya shuka bishiyoyi haka kawai ba, yanzu mun samu wata dabara, za mu iya koyi da mutanen gundumar Tsele, wato shuka bishiyoyi masu kwari da za su iya jure matsalar yanayi, su samar mana da inuwa da abun da za mu ci, har ma da uwa uba kudin shiga. Idan muka duba rayuwar al’ummar gundumar Tsele, za mu ga cewa bayan sun yi ta kaura, yanzu sun samu wurin zama, sun kuma samu sana’a. Duk da matsalar Hamada, yanzu rayuwarsu ta inganta, babu sauran kaura, sai dai su tabbatar da cewa, wannan yunkuri nasu ya dore.
Babban tallafin da wannan gunduma ta samu shi ne, kafuwar cibiyar bincike da nazarin Hamada a Tsele, wadda aka kafa a shekarun 1980. Babban abun da wannan cibiya ta fara yi shi ne, lalubo hanyoyin da za ta bi wajen dakatar da ci gaba da kwararar hamada a wannan wuri. Kuma ta hakan ne aka kai ga bullo da dabarar shuka wadannan bishiyoyi da suka yi matukar taimakawa. Ba ma bishiyoyin dake samar da abinci kadai a kan shuka ba, a kan kuma shuka wasu magunguna.
Wani manomi da na zanta da shi, ya shaida min cewa a baya, suna cikin rayuwa mai wahala saboda yadda kwarar hamada ta hana su sakat, ta hana su rayuwa mai dadi, ta hana su noma, ta kuma hana su samun kudin shiga. Amma yanzu, bisa taimakon da suka samu daga wannan cibiya da gwamnati ta kafa, sun samu wurin zama ba tare da zama cikin fargaba ba, haka kuma suna iya noma domin samun kudin shiga.
Hamadar Taklimakan ita ce hamada ta biyu mafi girma dake tafiya a duniya, inda fadinta ya kai muraba’in kilomita 330,000. Kusan ya zarce daya bisa ukun yankinmu na Nijeriya. Yadda kasar Sin take yaki da wannan hamada, muhimmin batu ne dake jan hankalin duniya. Daya daga cikin matakan da kasar ta dauka kuma, shi ne kafa wannan cibiya. Hakika cibiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da rayuwar mutanen gundumar Tsele, har ma da bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin. Ayyukan wannan cibiya ba su tsaya a Tsele kadai ba, tana kuma hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki na duniya tare da horar da dalibai da kwararru. Ko a watan Yunin bana, gomman malamai da dalibai da masana daga kasashen Afrika da dama, ciki har da Nijeriya, sun kai ziyara wannan cibiya da zummar kwayon fasahohin yaki da hamada.
A gaskiya duk wanda ya ziyarci wurin da jin labarin irin gwagwarmayar da aka sha, zai yaba da irin ayyukan da ake gudanarwa. Kasar Sin na gudanar da wannan aiki ne ba don komai ba, sai domin kyautata rayuwar jama’arta da kyautata muhalli ta yadda za a samu zaman jituwa tsakanin jama’a da muhallin da suke rayuwa.
Abu na biyu da ya dauki hankalina a wannan ziyara shi ne, layin dogo na Heruo, wanda ya hada biranen Hotan da Ruoqiang na kudancin jihar Xinjiang, mai tafiyar kilomita 120 a kowacce sa’a. Wannan layin dogo tare da na kudancin kasar Sin da na Kashgar zuwa Hotan da Golmud zuwa Korla, su ne suka hade suka kai tsawon kilomita 2712, tare da kewaye hamadar Taklimakan. Wanda ya zama layin dogon irinsa na farko a duniya da ya kewaye Hamada. A ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2022, jirgin kasa ya fara tashi daga tashar jiragen kasa ta Hotan, zuwa gundumar Ruoqiang a karon farko, wanda shi ne ya shaida kammaluwar layin dogon da ya kewaye baki dayan hamadar Taklimakan.
Kafin zuwa na Hotan a bana, abokin aiki na da ya ziyarci wannan yanki a shekarar 2021, ya ba ni labarin yadda gwamnatin kasar Sin ta shimfida babban titi irin wanda ake kira da Express, da ya ratsa cikin hamada. Labarin ya matukar burge ni, har na yi burin zuwa domin in ga wannan hanya. Amma bayan isata, sai labarin ya sha bambam, domin abun da ya dauki hankalina, ba wannan titi ba ne, layin dogon da aka shimfida ya kuma kewaye hamadar Taklimakan ne. Tabbas na ga babbar hanyar da abokin aikina ya ba ni labari, kuma ta burge ni sosai. Sai dai layin dogon ya fi jan hankalina.
Na samu damar shiga jirgin kasa daga Hotan zuwa Tsele, wanda ke daya daga cikin tashoshin jirgin kasan Hoton zuwa Ruoqiang. Kuma a tafiyar kimanin sa’o’i, abun da na biya a matsayin kudin tikiti, bai taka kara ya karya. Don haka, na yi mamakin yadda ake samun kudin tafiyar da harkokin jirgin kasan. Bayan tattaunawar da na yi da jami’ai, na fahimci irin kokarin da gwamnati ta yi a wannan wuri, domin an shaida min cewa, ana gudanar da wannan layin dogo ne ba tare da cin riba ba. Gwamnati ce ke daukar dawainiyar komai domin tabbatar da walwalar jama’arta.
Duba da yadda a kan samu iska mai karfi da rairayi, har a kan shafe kwanaki sama da 220 a shekara a wannan yanki na Hotan ana fuskantar iska mai karfi da kuma rairayi, ta yaya ake kare wannan layin dogo daga kwarar hamada?
Da nake zantawa da daya daga cikin jami’an dake kula da layin dogon, ya shaida min cewa, su kan dauki jerin wasu matakai. Matakin farko, su kan dasa shingen gajerun kirare da za su kare kwararar rairayi. Na biyu kuma, shukawa ko dashen bishiyoyi. Na uku, dasa kirare masu tsawo. Ya ce bayan wasu shekaru, shingayen kiraren za su lalace, amma zuwa wannan lokaci, bishiyoyin da ake yi wa ban ruwa sun riga sun girma, don haka, za su iya kare kwarar hamada. Wato idan bishiyoyin na iya tare rairayi, ba sai an sake dasawa ba.
To yaya za a kwatanta rayuwar baya da ta yanzu bayan samun wannan layin dogo?
Da nake zantawa da mataimakin shugaban gundumar Tsele, ya shaida min cewa, a baya kafin samar da layin dogon, idan mazauna za su fita daga yankin domin karatu ko asibita sai dai su hau mota zuwa birnin Hotan, kana daga nan kai tsaye zuwa Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang, sai an shafe sa’o’i 20, yankin ya kasance tamkar a rufe saboda babu ci gaban tsarin zarga-zirga.
Kafin samun layin dogon, mutanen yankin ba su da masaniya game da yanayin da duniya ke ciki, bukatarsu kawai su yi noma su sanya tufa, amma a yanzu, suna iya fita su ga yadda duniya ta ci gaba, suna kara bude idanunsu, inda suke komawa yankin da sabbin ilimi har ma da buri da dabarun raya yankinsu don kara kyautata rayuwarsu.
Hakalika, a yanzu an samu kyautatuwar mu’amala tsakaninsu da sauran sassan Jihar Xinjiang da ma sauran sassan Sin ko domin karatu ko yawon shakatawa.
Bugu da kari, ya ce a baya akwai rashin fahimta mai tsanani game da kudancin yankin Xinjiang, amma saboda kyautatuwar tsarin sufuri a yanzu, ba sai an yi ta karyata masu yada jita-jita ba, gani ya kori ji, mutane na iya ziyartar yankin. Kana mutanen yankin su ma za su iya bayyana halin da suke ciki idan suka fita.
Hakika ci gaban tsarin sufuri tushe ne na bunkasar tattalin arziki. Yanzu haka, gwamnatin kasar Sin ta dukufa wajen ci gaba da kyautata tsarin sufuri a jihar, ciki har da gina filayen jiragen sama da tituna domin bunkasa tattalin arziki da zirga zirga a jihar Xinjiang.