Direban babbar motan da ya tsallake rijiya da baya bayan da ’yan banga a garin Uromi na jihar Edo suka kashe matafiya 16 na jihar Kano, ya musanta ikirarin cewa, lamarin na da alaka da kabilanci.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a a lokacin da matafiyan da ake kyautata zaton mafarauta ne, ke kan hanyarsu daga Fatakwal ta Jihar Ribas zuwa Kano domin gudanar da bukukuwan Sallah.
- Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Hadin Gwiwar Inganta Amfani Da AI Don Amfanar Da Kowa
- Shugaban Ohanaeze Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Ƴan Arewa 16 A Edo
Direban babbar motar, wanda ba a bayyana sunansa ba a wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, ya bayyana cewa, yana jigilar kayayyakin kamfanin rukunin Dangote ne zuwa Obajana da ke jihar Kogi a lokacin da ya ci karo da mafarautan a Elele, inda suka nemi ya dauke su zuwa yankin Arewacin kasar nan.
“Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban.
A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar.
Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince da su ba ya bukaci su sauko. Da jama’a suka ga irin makamansu da karnuka, sai suka far mana,” in ji direban. “Shugaban ya shaida wa wadanda ke wurin cewa, mu masu garkuwa da mutane ne kuma ‘yan Boko Haram ne, sai suka fara dukanmu.”
Direban tare da wasu mutum biyu, an ce shugaban ‘yan bangar ne ya daure su a hannu tare da kai su ofishin ‘yansanda da ke kusa, inda ya shaida cewa, masu garkuwa da mutane ne ya kamo, lamarin da ya sa aka tsare su cikin gaggawa.
Direban ya bayyana cewa, “A lokacin da aka sake mu na koma wurin, an riga an kashe mutane 16.”
Sai dai ya yi watsi da zargin cewa, lamarin rikicin kabilanci ne. “Wannan ba rikicin kabilanci ba ne, ‘yan banga ne kawai ke da alhakin wannan harin, su ne suka sa aka kashe mutanenmu cikin ruwan sanyi,” in ji shi.
Wannan mummunan lamari dai ya janyo tofin Allah tsine a fadin kasar, tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike domin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp