Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan motocin da ke dauke da maniyyata a jihar Sakkwato a ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne a ranar litinin a lokacin da mahajjatan ke kan hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama domin zuwa kasar Saudiyya ranar Talata don gudanar da aikin hajji.
Majiyoyi sun bayyana cewa an jikkata wasu daga cikin ‘yan bindigar a yayin fafatawarsu da jami’an tsaron dake rakiyar maniyyatan.
Jaridar 21stcenturychronicle ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun yi wa maniyyatan kwanton bauna ne a dajin Gundumi amma jami’an ‘yan sanda da ke cikin ayarin motocin sun dakile harin.
Majiyar ta ce an kubutar da dukkan maniyyatan, daga bisani kuma aka kaisu fadar hakimin Isa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp