Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen jihar Kebbi, ta tabbatar da kashe Alhaji Isah Daya, Uban kasar Kanya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar. An yi garkuwa da Basaraken ne tare da mutane takwas a gundumar Kanya ta karamar hukumar Danko/Wasagu a ranar 6 ga watan Oktoba.
Tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yansanda, sojoji, da ‘yan banga, sun yi nasarar ceto takwas daga cikin wadanda aka sace a cikin dajin Sakaba a ranar Talata da karfe 10:00 na safe. An garzaya da sauran wadanda aka ceto zuwa babban Asibitin Sakaba don duba lafiyar su.
- NAHCON Za Ta Biya Alhazai Diyyar Wasu Kuɗaɗe Kan Ƙarancin Kula Da Su Lokacin Hajji
- Gwamnatin Zamfara Ta Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Rundunar CPG Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar
Sai dai abin takaicin shi ne, an gano gawar basaraken gundumar ta Kanya ne a lokacin da ake aikin ceto a cikin dajin Sakaba.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bello Muhammad Sani ya mika ta’aziyya ga gwamnatin jihar da masarautar Zuru da iyalan marigayin, inda ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa.
Rundunar ‘yansandan ta bukaci jama’a da su bayar da bayanan da suka dace don taimakawa wajen kamo wadanda suka aikata laifin. Duk mai bayani zai iya tuntuɓar hukuma don tallafawa binciken don samun nasarar aikin da ake yi.