‘Yan Boko Haram da ‘yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna tare da kai wa mazauna gari hari a jihohin Borno da Filato da Katsina a tsakanin daren Lahadi zuwa ranar Litinin, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu da dama. Rahoton Daily trust
Sun kuma kai hari a wani kauye da ke babban birnin tarayya Abuja inda suka kashe wani yaro dan shekara bakwai tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin.
kwanton bauna a Borno
A jihar Borno, da sanyin safiyar Litinin ne mayakan haramtacciyar kungiyar Boko Haram suka yi wa ayarin motocin hadin gwiwar sojoji da na farar hula (CJTF) kwanton bauna a karamar hukumar Gubio.
Duk da cewa babu wani adadi da aka samu a hukumance, amma dai an kashe shugaban CJTF, Alhaji Bukar Mandama da mambobinsa hudu a harin kwanton baunar.
Sojoji sun dakile harin a Neja
A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindigan sun kai wa wani sansanin soji a Sarkin-Pawa, dake hedikwatar karamar hukumar Munya a jihar Neja hari, inda Sojojin suka yi nasarar dakile harin.
Daily trust ta rahoto cewa ‘yan ta’addan sun yada zango ne kusa da sansanin sojojin da misalin karfe 2:23 na dare.
Harin ‘yan bindiga a Katsina
A jihar Katsina, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara da suka hada da matan gida hudu da yara biyar a Shema kwatas da ke karamar hukumar Dutsin-Ma.
An kashe mutum 2, Daya ya jikkata a Filato
Wasu ‘yan bindiga a daren Lahadi sun yi wa sojoji kwanton bauna a kauyen Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato. Wani mazaunin garin Salisu Dahiru ya ce wasu fararen hula biyu sun rasu sannan daya ya samu raunuka sakamakon harbin da aka yi musu.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar harin, ya ce: “ Harin kwanton bauna ne.”