Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta sanar da kisan ‘yan ta’addan da ba a san iyakarsu ba a wani artabu da suka yi da su a lokacin gudanar da aiki a wasu yankuna biyu na jihar.
Jami’an sun gudanar da aikin ne a kauyukan Dadawa, Barkiya da kuma Kurfi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihra, ASP Gambo Isah ya sanar da hakan a ranar Litinin da yamma. Ya ce da misalin karfe 1:30 na daren Litinin aka kwato tumaki 74 da awaki 34 da kuma shanu 92 da ‘yan ta’addar suka sato.
Ya ce rundunar ‘yansandan ta amshi kiran gaggawa daga al’ummar yankin a daidai lokacin da ‘yan ta’adda sama da tamanin (80) kan babura dauke da makamai suka kai farmaki a kauyuka guda biyu na karamar hukumar Kurfi.
ASP Gambo Isah ya ce rundunar za ta kara aje wata tawagar jami’anta na musamman don dakile hare-haren ‘yan ta’adda a yankin.
A cewarsa, tawagar jami’an ta ‘yansandan sun tarwatsa ‘yan ta’addan tare da kwace shanu da tumaki da kuma awaki da dama daga maharan.
Ya ce har ya zuwa yanzu jami’an ‘yansandan na gurin da abun ya faru don kama sauran ‘yan ta’addan tare da tattara gawawwakin wadanda suka mutu. Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar, Idris Dabban na shawartar al’umma da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai don kawo karshen ta’addanci.