Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi, Festus Keyamo (SAN) ya ce idan ana so NIjeriya ta iya dakile hanyoyin yada labaran karya, dole ne a rufe duk wani zauren da ke yada labarin karya a shafukan sada zumunta.
Keyamo ya bayyana cewa domin samun nasarar “dakile labaran karya, yana da mahimmanci a rufe duk wani zaure na bogi.”
- Montana Ta Zama Jihar Amurka Ta Farko Da Ta Haramta TikTok
- Mutum 1 Ya Mutu, Da Dama Sun Bace Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kwara
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron fara ba da horo ga ‘yan jarida mai taken, “Balancing Ethics and Patriotism: Obligations of Journalists to their Country”, wato ‘Ka’idar Jin Ta Bakin Kowane Bangare Da Kishin Kasa: Hakkokin ‘Yan Jarida Ga Kasarsu,’ wanda Kungiyar hadin gwiwa don tabbatar da kyakkyawan shugabanci da tabbatar da tattalin arziki a Afirka ta shirya.
Keyamo, wanda Niyi Fatongun ya wakilta, ya ce duk da cewa kafofin sada zumunta sun tsaya da kafarsu, amma dandalin suna aiki ne ba tare da masu sa ido ba.
“Tsayuwar kafofin yada labarun abu ne mai kyau. Amma dai a yau mutane na iya samun damar bayyana ra’ayoyinsu ga jama’a ba tare da kwaba ba, sai dai hakan na faruwa ne tare da amsu daukar nauyi ko mallakia Kafofin sadarwar zamanin ba su dauki masu sa ido a bakin komai ba.
“Domin dakile yada labarun karya, yana da mahimmanci a rufe duk wani zauren da bai dace ba, domin labarun karya na iya lalata tsarin al’umma,” in ji Keyamo.
Har ila yau, daraktan kungiyar Hadin Gwiwa Don Kyakkyawan Shugabanci da Tabbatar da tattalin arziki a Afirka, John Maiyaki ya ce labarun karya na iya haifar da rikici.
Ya ce suna bai wa ‘yan jaridun Nijeriya kwarin gwiwar yaki da labaran karya, inda ya bayyana cewa hatta rashin fahimtar juna ma na iya jawo rikici.