An kashe mutum daya kuma ba a ga wasu da dama ba, bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, suka kai hari karamar hukumar Isin da ke Jihar Kwara.
An ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun je kan hanyar Ijara/Isin a jiya Talata, inda suka sace matafiya da dama, suka kuma kashe wani mai suna Cif Adeyemi a yankin Pamo Isin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Amurka 4 A Anambra
- Za A Rika Tuna Wa Da Mijina A Matsayin Gwarzon Gina Rayuwar Matasa –Aisha Buhari
A cewar wani sako da aka tura a kungiyar Whatsapp na mazauna yankin, sakon ya gargadi mazauna yankin a kan bin hanyar Ijara/Isanlu Isin domin kuwa, an sace wasu matafiya da ba a san adadin su ba.
Talla
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba a garin Ilorin.
Talla