A yau, duniya ta koma zamanin intanet inda yara da matasa ke amfani da waya da kwamfuta wajen samun ilimi, wasanni da sada zumunta. Sai dai, hakan yana zuwa da barazana da illa idan ba a taka-tsantsan ba.
Matsalolin Da Yara Ke Fuskanta a Intanet
Yaudarar Yara (Online Grooming): Wasu mutane na amfani da intanet don yaudarar yara da yi musu alkawurra na karya.
- An Bude Sabon Shafin Internet Na Samar Da Hidimomi Na Kasa Da Kasa Na Beijing
- Guinea-Bissau Na Neman Karfafa Hadin Gwiwar Kafofin Yada Labarai Da Sin
Fadawa Cikin Illolin Blue Film: Yara na iya shiga shafukan da basu dace da su ba tare da sun sani ba.
Sata Ko Bayyana Bayanan Sirri: Wasu shafuka da aikace-aikace (apps) na satar bayanan yara.
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari.
Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online.
Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar
Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su.
Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa.
Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna.
Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da yara za su rika amfani da intanet.
Sanin abokansu na online – Iyaye su bincika su san wanda yaran su ke hulda da su a WhatsApp, Facebook, da sauran shafuka.
Guje wa kyauta ko aikawa da kudi online – A hana yara karbar ko aika wa da kudi ga mutane da ba su sani ba.
Kar a saka Hotuna masu fallasa – Iyaye su koyar da yara cewa duk abin da aka saka a intanet yana nan har abada.
Labari Mai karfafa Gwiwa
Akwai wani yaro mai suna Abdul, mai shekaru 12. Ya saba danna duk wani link da ya gani a Facebook. Wata rana, ya bude wani link wanda ya yi downloading na wani application da ba shi da lafiya. Wannan application ya dauke bayanansa kuma ya aika wa wani mutum wanda bai sani ba. Sai dai da yake iyayensa sun koya masa kada ya bayyana bayanansa, bai bayar da lambar katinsa ba, hakan yasa bai fada tarkon zamba ba. Wannan na nuna cewa idan iyaye suka koya wa yaran su yadda za su yi taka tsantsan, hakan na iya ceton su daga hatsarin intanet.
Kammalawa
Iyaye su fahimci cewa intanet yana da amfani, amma yana da hatsarori. Muna bukatar wayar da kan yara da matasa a kan yadda za su kare kansu. Ku kasance masu lura da irin shafukan da yaran ku ke ziyarta don kare su daga barazanar duniya ta yanar gizo.
Ku ci gaba da bibiyar wannan shafi don samun karin bayani kan yadda za a kare kai daga hatsarin intanet!