• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za A Kula Da Tafin Kafa Lokacin Hunturu

by Bilkisu Tijjani
3 years ago
Kafa

Masu karatu da ke jimirin bibiyarmu a wannan shafi mai farin jinni na Ado Da Kwalliya ina muku gaisuwa ta ban girma assalamu alaikum. Ina fata kowa yana nan cikin koshin lafiya amin.

Kamar yadda aka sani, a duk lokacin da hunturu ya shigo, ana samun tamukewar fata ta yadda wani lokaci abin kan kai da fashewa a samu faso.

  • Yadda Qatar Ta Zo Da Sabon Salo Na Ba-zata A Gasar Cin Kofin Duniya
  • Tsoma Baki Da Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Da Amurka Ke Yi Bai Samu Karbuwa Ba

Saboda mihimmancin kula da tsaftar kafa a wannan lokaci ya sa muka dauko wannan batu mai muhimmanci a wannan makon.

Dole ne mu kula da tafukan kafafunmu. Mata da dama na mantawa wajen kula da kafa a duk lokacin da suke kwalliya. Lallai idan aka yi hakan kamar an yi tuya an manta da albasa ce.

Abin kunya ne a ce mace idan ta taka mutum sai ya ji kamar kaya saboda tsabagen kaushi da faso da ke tafin kafarta. Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kula da tafukan kafarmu kamar haka:

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

Kamar yadda bayanai daga Manhajar Kwalliya Da Gyaran Jikin Mata suka nuna, abu na farko da za a yi shi ne, a samu man glycerin da gishirin Epsom (ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man tee tree da kuma man peppermint a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon minti 15 zuwa 20 sannan a dauko dutsen goge kafa a diddirza, za a ga canji.

Na biyu kuma, za a iya amfani da baking soda (ana samunsa a inda ake sayar da kayan hada kek) da man tea tree da man lafinta sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su sai a tsoma kafa na minti 20 sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kaushi da faso a tafin kafa.

Hanya ta uku ita ce, a samo Man lafinta da sea salt da ruwan aloe bera da man Rosemary a hada su a ruwa sannan a tsoma kafa na tsawon minti 20 sannan a dirza kafa har sai ta fita tsaf.

Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da tawul. Sannan a shafa man glycerin da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa. Sannan sai a yanka farce a gyara su.

Wadda ke fama da matsalar kaushi lallai ne ta dage wajen yin amfani da safar kafa idan da dama a shafa man basilin a tafin kafar kafin a kwanta a kullum. Sannan a sanya fatar kafar yin laushi da kuma rage shi daga tsagewa.

Dutsen goge kafa na taka rawar gani wajen tabbatar da samun tafin kafa mai sulbi da kuma cire kaushin kafa. Ya kasance kafa ta jiku kafin a yi amfani da dutsen goge kafa domin samun sakamako mai matukar amfani.

Muna fata za a kara kula sosai da tsaftar kafa domin a wannan lokaci galibin inda ya fi samun matsala ke nan a wannan lokaci na hunturu a jikin Dan’adam.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Next Post
Sin Ta Kara Baiwa Zimbabwe Allurar Rigakafin COVID-19

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.