Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku, a cikin wannan filin, ina fata kuna cikin koshin lafiya.
A wannan makon na kawu muku guzurin bayani kan yadda za ku yi amfani da madara wajen magance maikon fuskarku.
Ku sani yawan shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, tana sanya ta taushi da kuma santsi. Hakan ya sanya na kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance maikon da ke fuskarku.
Abubuwan daya kamata uwargida ta bukata:
Madara, Gishiri, Ruwa, Auduga, Zuma
Amfanin madara wajen magance maikon fuska:
Madara na goge daudar fuska- A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska zuwa wuya kamar na tsawon minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
Madara na sanya fata santsi, don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Sai a jira ta bushe kafin a wanke. Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi, musamman lokacin sanyi da gashi ya kan kakkarye. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta kai cikin tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska a lokacin sanyi ki rika goga bawon kankana da bawon ayaba a fuskanki yana cire dattin da suke makalewa a fuska.
Ki samu ayaba ki kwaba kina shafama fuska na tsawon minti 10-15 sannan ki wanke.
Ki kwaba lalle ki diga miski kadan da man Hulba sai ki shafa a gabanki bayan minti 30 sai ki wanke da kanki za ki ji sauyi, yana kare shigar cututtuka.